← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 78

Sashe 71

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi tsaki Ina Murmushin jin kunya bance Mata komai ba, se daya bayan nayi sallah sannan na fara Shirin tafiya, Zuhra tuni ta tafi mijin ta yazo Suka tafi, na dauki wayata na Kira dji, bugu daya ya dauka Yana fadin

" Babes mu hadu wajen parking"

Bance komai ba Amma wannan Babes din seda taikar jiki na ta tashi, wani irin sassanyan yanayi naji, na dauki jakata na fito, Yana tsaye gaban mota ta, na bude ya Shiga mota sannan na shiga nima, na tada motar Ina tambayar shi mummy da Amra, yace duk suna lafiya suna gaishe ni, na gyada Kai yace

" So..."

Na kalle shi sannan na kalli titi Ina jiran abinda zai fada, se ya ce

" Are you ready yanzun? Kin shirya aure na?"

Na Dan Kara kallon shi, he look serious Kuma dama nasan he's always serious akan magana ta, nayi shiru Ina hango yarana, Ina hango idan nayi aure Zan rabu dasu Dole tunda Abba har dasu Ahmad bazasu bar kannen su suyi agolanci wani gurin ba, nace

" Can you give me time?"

Ya kalleni yace

" Kamar zuwa yaushe? I thought I've given you enough Babes, shekara uku da wasu abun ya kamata kiyi sorting feelings dinki, nasan da da yanzun ba daya bane, Amma kinsan ke kadai nake so wannan lokacin nake ta jira na cika Mana burin mu, don't worry about the boys I can be there for them, I'll take care of them"

" Cànîm!"

Na Kira sunan shi a hankali daidai lokacin nayi parking a gefen titi, ban masan Ina Zan kaishi ba, ya dubeni da sauri fuskar shi dauke da murmushi yace

" I longed to hear you say Cànîm again"

Nayi murmushi kamar yadda nayi ta jiran Jin yace min Babes.

" Ina son yarannan, ni kadai suke da, idan na fara maganar auren ka se na rabu dasu..."

" Zan iya rike Miki su Unaisa, please marry me, Dan Allah Unnie!"

Na kalleshi he pleads with komai na jikin shi hatta idanun shi roko na suke, Nima Ina son shi Amma Kuma da da yanzun ba daya bane, a wancan lokacin bani da komai shi kadai nake dashi, I wanted badly na aure shi, har Ina tareda Hafiz Ina ganin idan ya dawo Zan iya barin Hafiz na koma Masa, to yanzun abin ya canja, yanzun inada yara, na Kuma girma.

" Ina Zan kaika"

Yayi Murmushin da yake Yi kullum yace

" Can I see the boys?"

Nayi murmushi nace

" They will be glad of course!"

Aikuwa dai mukaje, tunda nayi parking nayi knocking na fara jiyo muryar Alby Yana

" Ommaah oyoyo!"

I felt warm, wani irin Dadi nakeji, shima Yana ta kallona Yana murmushi, he's happy I'm happy! Ana budewa Suka fito, daya ya rungume kafa ta ta baya, daya Kuma ta gaba, na daddago su Ina tambayar yadda suke. Kawai kallona suke with so much love a idanun su, ya karaso ya Mika musu hannu, dukka Suka kalleni suna jiran na gyada kaina suje, nace

" Call him Papa"

I can see the smile on his lips, ya karbe su, mun Jima anan ya karba key Dina ya fita dasu ni Kuma na shiga ciki nayi wanka na canja Kaya, nayi girki se laasar suka dawo ya tafi shi Kuma. Kamar Wasa Al'amin ya dawo da karfin shi, ni Kuma har lokacin ban Gama sorting kaina ba, Haka Kuma bansan duk abinda ya faru ba, ana Haka Zuhra ta haihu, Dan ta namiji me sunan Baffa muka Sha suna. Wasa Wasa akai watanni Yana ta Bina but still na kasa samun courage din yin magana da wani ma, dukda kasan zuciyata son shi nake Kuma Ina son auren shi Amma yarana Kuma fa, I've to give up Zama dasu kenan! Baba Asabe ta fahimci hakan ta same ni a daki Ina gyara musu kayan su, dukkan su suna kwance saman gado suna Wasa sun baza letter toys dinsu da nake koya musu, se Wasa suke happily. Ta zauna nasan magana zatayi, Dan Haka na Bata hankalina tace

" Yaronnan Aminu Yana son ki Ommaah"

Na danyi murmushi nace

" Na sani Baba Asabe"

Tayi murmushi tace

" Kinyi kankanta kice ba zakiyi aure ba, kowa tausayin ki yake shiaysa baa Miki maganar auren Amma da sunsan sashi.."

Na katse ta nace

" Baba Asabe yarannan, Ina Zan kaisu"

Ta dube su tace

" Gashi nan gurin Yan uwan su Mana, da kin bar Ahmad ai da tuni ya dauek su, ya kamata kiyi wani abun, mutuncin ki auren ki"

Ta fita nayi shiru, Abiey left me so early, he left me stranded, gaba daya Ian Jin rayuwata ta koma baya from square zero.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

[6/30, 10:40 PM] Hauwa Galadima: *H³*

Nayi shiru na rasa wanne tunani zanyi Kuma, wannan shi ne gaba Kira Bata sayaki, Ina son shi Ina kaunar Zama dashi Amma Kuma bana son rabuwa da yarana, na kalle su yadda suke ta Jin Dadi suna wasanni abinsu, ni dince dai solace din su, to Amma Kuma idan na hanga na hango se Naga ya kamata ace nayi aure, gaskiya Baba Asabe da tace iyayena Basu San da zaman Al'amin ba da tuni sun bashi damar ya turo din da nake ki. Da kyar tunani ya barni na Gama saka musu kayan su, na dube su nace

"Oya boys will you go out?"

Jr yafi kowa son yawo ya saki letter "Q" din hannun shi ya taho ya rungume hannuna Yana squealing murnar maganar da nayi, na fara shirya shi sannan na janyo Alby nace

" Baka ji Ommaah na magana ba?"

Ya Dan turo Baki yadda nakeyi yace

" Mu zauna a gida"

Na shafa Kan shi nace

" We're going out to buy sweet"

Se ya danyi murmushi, shi din bai son yawo ko kadan kullum so yake muyi ta Zama a gida. Na shirya shi kayan su iri daya komai da komai sannan Nima na shirya cikin wata atamfa gold embellish, dinkin gown yayi min kyau nayi Yar caras Dani, slay Mamaa, na saka wedge sandal sannan na daura dankwali Muka shirya da kyau na dauki wallet da wayata da makullin mota mukai gaba, bansan ma Ina Zan kaisu ba kawai gidanne ya ishe ni se kawai na Kai su wani bee's Ice cream parlor na siya musu Suka Sha a wajen sannan muka fito, na duba agogon dake makale a hannuna Naga biyar tayi lokacin zuwa bikin da aka gayyace mu yayi da banyi niyyar zuwa ba Amma Dan na Dan kashe lokaci se kawai muka tafi, se a sannan Anty A'isha ta Kira ni, gaba daya na manta tare zamuje da ita.

Kafin mu dawo har sunyi bacci so Ina parking, na daddauke su na Kai su ciki, na rage musu kayan jikin su sannan Nima nayi Shirin kwanciya, na kwanta a gefen su inata kallon su, Haka ne dalilin da yasa Anna taki tayi aure kenan saboda mu, Amma Kuma ni Ina son Al'amin, kamar yasan Ina tunanin shi Sega kiran shi ya shigo, na Dan saki murmushi nace

" Cànîm!'

Yace

" Babes ya kike? How are my boys?'

Na dube su sannan nace

" They have slept already, munje unguwa ne"

" Wow! Ni an wareni a gefe ai, Unnie kin daina so na ne? It's taking longer than expected fa, kullum se kice na Kara Miki lokaci Babes I'm not getting any younger fa"

Na Dan saki ajiyar zuciya nace

" I'm sorry, I'm really sorry! Da gaske Ina sonka..."

" Ki yarda muyi aure to, shi ne kadai abinda zai tabbatar min kina Sona"

Na danyi shiru nace

" Cànîm the boys! Bansan ya zanyi dasu ba"

Yace

" How many times nace Miki Zan rike su, kina ganin Zan ki abinda yake naki"

Nace

" Cànîm Yan uwan su bazasu yarda ba wallahi, I really want to be with them and you!"

Yayi shiru ya fahimci maganata se kawai ya dauke maganar muka koma wani, na daga idanuna na kalla agogo it's past eleven, nace

" Cànîm ka.tafi gida Mana!"

Yace

" Ina gida ai tun Bayan sallar Isha"

Nace

" Ayya Kuma muke waya? This is unfair"

Se lokacin ya tuna Bai fada min baiyi aure ba Kuma yasan Babu inda Zan San baiyi auren ba, yayi murmushi yace

"Tohm, sleep well!"

Kafin ma ya karasa naji wani takaici ya lullubeni so da gaske Yana da aure kenan, OMG!

Washegari ban fita aiki ba saboda Babu aikin, Ina zaune a gida Ina saka, Dan sosae na Kara bude wuta akan sakar Kuma Babu laifi I'm hitting the button, Dan kuwa na samu alkhairi sosae a ciki. Se Sha daya na aje na fito na shiga kitchen Dan daura abinci, nayi mashing Irish da kwai na saka musu a cikin Dan bowl na Barbada seasoning da Mai na kiar su na Basu, ni Kuma na zuba sauran na fito, ban Gama ba Sega Nuzla da Ahmad, har lokacin shekara biyu da wani Abu ko Bari Bata Yi ba, tun Bata damuwa har abin ya fara damun ta, muka gaisa dasu sannan muka fara hira Ina ce musu su dinga bani notice idan zasu zo. Yaran duka sun makale su Dan sun Saba dasu sosae barin ma Ahmad, da idan Bai aiki zai zo ya dauke su suyi ta yawo, se azahar na Gama abincin Rana na zuzzuba musu na fito se Naga Alby na rike kirji, Yana Jan numfashi da kyar, nayi murmushi Ina girgiza Kai, Jr ya tafi da gudu inda nake aje inhaler ya dakko Masa, ya bashi Bai cire murfin ba yasa a Baki Yana Dan tari, na Kara dariya na karasa shigowa Ahmad yace

" Wai kwaikwayon ki suke?"

Ina dariya Ina zaunar dasu saman may din Dana shimfida nace

" Ai kullum se anyi wasan Ommaah, sunyi tunanin hakan Dadi ne dashi"

Nuzla tace

" Suna da wayo da Suka gane condition din maman su"

Nace
Chapter 71 · 0% Book details