← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 78

Sashe 32

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi dariya na zauna sannan ya zauna shima, mukai ta Hira har wajen awa sannan yace na fada ma Anna zai shigo ya gaishe ta, ta fito tsakar gida Suka gaisa sannan ya tafi kofar gida, Anna ta bani turare da Dan kunne na bata bayna munyi exchanging number. Muka tsaya ni dashi ita Kuma Amra kafin ta Shiga tayi Mana hoto tace Wai ba karamin dacewa mukai da juna ba, ba kuga bakin mutuniyar ku ba se murmushi nake ni irin an yabe ni dinnan, tana murmushi ta shiga cikin mota, ya dubeni yace

"Yaushe Zaki fara classes din?"

" Monday!"

Yace

" Allah ya bada saa, se yaushe kenan?"

Nace

" Se idan kazo"

Yayi min murmushi ya shiga mota Wai idan ya biye ni ya dinga kallo na kenan, na kalla Amra nace

" Se Monday ko? Ki gaida Mummy"

Ta amsa sannan suka tafi na Dan tsaya Ina kallon anguwan, rayuwa gudu take kamar Wasa Alhaji Yahai ya saki Anna, kamar Wasa Anty Nana tasa ta saya gida se gashi gida yayi amfani, Allah ya rufa Mana asiri yayinda shi yaso tona Mana. Ina Shiga na samu kyakyawan labari gurin Anna akan Zuhra zasu je aikin hajji. Na zauna cikeda Jin Dadi nace

" Mashaaa Allah! Ita da Yaya khalifa?"

Anna tace

" Dukkan su, baban Asiya ya biya musu Wai shi ne gift dinsa na auren su"

Nace muku ku daina Wasa da Yan siyasa Kun ki ko, kunga irin wannan kyautar, nace

"Wai wa da wa?"

Tace

" Su takwas din, har da A'isha ya hada da mijin ta"

Nayi ta Masa addua sannan na Kira su na musu murna. Washegari naje kasuwa na siyo wool da yawa different colors da knitting pins. Dake Cànîm ya bani shawarar nayi classes, na saka akai flyers se gashi na samu wasu zasu shigo, bayan Amra. Duk kayan da ake bukata na siyo.

Al'amin

Dawowar shi kenan daga kazaure, a matukar gajiye yake yayi parking motar shi Amma Bai fito ba ya tsaya ya janyo wayar shi ya fara kirana, Ina kusa da wayar na dauka sede cikina ciwo yake, Dan a kwance nake

" Me ya faru? Baki da lafiya ko?"

Nace

" Uhmm!"

Yace

" Me yake damun ki? Tell me"

Bansan lokacin da nace

" Dysmenorrhea nake Yi!"

Yace

" Subhannallah! Kinsha magani, nasan kinsha ki cewa Nuzla ta siyo Miki coke Kisha, it will go. Nima na dawo anjima Zan Kira ki"

Se yayi min sallama ya shiga gida, Bai ma tsaya ya shiga ciki ba yayi baya inda dakin shi yake, ko Ina Kal Kal tamkar na mace, dama ko motar shi ka kalla kasan Yana da tsafta, yadda motar kullum daukar idanu take balle ka kalle shi Haka yake so ba abin mamaki bane Dan ya kasance me tsafta. Wanka yayi sannan ya fita yayi laasar Yana dawowa ya wuce parlor. Tun daga muryar yaji yasan Mummy tayi bakuwa, Amma tunda ya riga da yayi sallama se kawai ya shiga ciki. Hajiya Attine ce zaune suna ta Hira ita da Mummy. Ya zauna can gefe ya gaishe ta, tace

" Hajiya Nafisa Haka dama Al'amin ya Zama magidan ci, to ai Zan iya ganin shi ban gane shi ba"

Mummy tayi dariyar Jin Dadi tace

" Aikuwa dai, gashi nan"

Se ta kalleshi tace

" Abinci fa? Ko se anjima"

Cikeda kosawa yanzun da yayi aure he's sure an kawo Masa abinci, dukda Mummy na kokarin kula da shi Amma he needs a family, kullum bukatar Unaisa yake ya akamata yayi speeding process din. Ya mike yace

" To Mummy, idan kina free Zan shigo"

Ya fice, Hajiya Attine tace

" Yana ta aikin shi abin shi"

Mummy tace

" Wallahi fa! Sede godiyar Allah"

Ta Dan gyara Zama tace

" Ai ya kamata yayi aure kinsan yaran nan fa"

Mummy tace

" Kinsan shi da high taste din shi nan, kowa nace ya nema se yace a'a shiyasa na zuba masa idanu, Kuma Baba yace na kyaleshi aure lokaci ne"

Tace

" Gaskiya kam, Amma ai da kin mishi maganar Nura kiga ko zai amince"

Mummy tayi dariya tace

" Kema Hajiya da wani Abu, inace Zunnura da kanta tace Bata son Al'amin din"

Hajiya Attine tace

" Kai shirirta ne fa, da zaayi abunnan I'll be very happy zai Kara strengthening kawancen mu"

Mata se a barmu, shekarun baya aka so ayi wannan hadin Amma Zunnura wadda ake Kira da Nura da kanta ta fadawa Mummy ita gaskiya Bata son shi, ita me kudi take son ta aura to Kuma yanzun ga wata ta bullo. Mummy tace

" To ai shikenan Zan Masa magana anjima."

Se dare ya samu ya same ta a daki, Bayan sun Kara gaisawa ya tambaye ta aiki sannan yace

" Mummy aure zanyi"

Da sauri ta aje abinda ke hannunta, ta Kara fadada fara'ar ta tace

" Mashaaa Allah! Wacece? A Ina ka hadu da ita"

Tiryan tiryan ya zauna ya Bata labari kaf, seda ya gama tace

" To Ina mahaifin ta?"

Yace

" Sun rabu da Maman nata"

" Se Bata Kara aure ba, take zaman kanta? Wani irin abu ne wannan"

Ya Dan dubeta da mamaki yace

" Mummy Dan Allah! Wallahi you'll love her, Bata da matsala Amma idan kina tantama kafin Daddy ya shiga maganar kiyi bincike"

Tace

" Se ka bani lokaci, sannan ko zaka iya zuwa kaga Zunnura Yar Attine?"

Da mamaki ya kalleta tare da Bata fuska yace

" Wai wannan Nuran? Haba Mummy Mana, Dan Allah ki bar maganar kawai"

Tace

" Me yasa"

Yace

" Na fada Miki Unaisa nake so, ya kike zancen wata Nura Kuma? Dan Allah Mummy"

Tayi ta kallon shi tace

" Al'amin idan na baje maganar Unaisa fa? Nace sede ka aura Nura fa?"

A take yaji hankalin shi yayi balain tashi, ya Mike se Kuma ya zauna ya riko hannunta yace

" Mummy Kar kiyi Haka, Dan girman Allah!"

Ta gyada Kai tare da bashi umarnin yaje ya huta.

A bangarena nasha coke din, it did a miracle Dan ciwon daukewa yayi gaba daya, nayi bacci se bayan maghrib na tashi, nayi wanka sannan na dauki wayata Amma ga mamakina se Naga kawai Babu notification ko daya, either message or call. Abin ya bani mamaki se nayi laakari da banida lafiya kilan baya son takura min. Naci abinci na Kara Shan coke sannan mukai kallo wajen 9pm na tafi Dan na kwanta Amma still Babu Kira Babu message, na kunna data wadda banida ita Amma seda nayi shima Babu komai last seen dinsa tun lokacin da mukai waya da Rana. Na Yi saurin dialing number din shi Dan nasan Babu lafiya kenan, tabbas Babu lafiya tun daga ranar da muka fara ganin juna Bai taba tsallake Rana Bai kirani ba, Bai taba tsallake Kirana yayi min seda safe ba balle yasan banida lafiya. Wayar a kashe se na fara ayyanawa, kila ya saka charge ko Kuma ta mutu Bai sani ba, na zame na kwanta Amma kunsan me ? Na kasa nutsuwa kwatakwata hankalina yaki kwanciya, an tasa abinda yake min Dadi a duniya, wani irin bakin yanayi nake ji.  A Haka bacci can ya lalalbo ya sace ni, believe me walahi duk baccin cike suke da mafarkan sa.

UNAISA is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[5/29, 8:19 AM] Hauwa Galadima: *B_B*

Se da nayi sallar asuba kafin nayi bacci me dadi, wajen takwas da na tashi na samu message dinsa na ban hakuri akan jiya, ko bakina ban kuskure ba na Kira shi, bugu daya ya dauka nace

" Me ya same ka?"

Yayi murmushi yace

" Na tayar Mata da hankali Babu komai, charge ne ya dauke, ya Kika tashi?"

" Ni ban yarda ba gaskiya!"

" Karya nake kenan?"

Nace

" A'a kawai dai Haka nake ji Kamar akwai abinda ya faru baka son na sani"

Yayi dariya yace

" Dama na taba boye Miki Abu ne? Nothing happened I'm sorry"

Se na yadda da hakan muka Dan taba Hira sannan mukai sallama, ban taba kawowa abin zai zo a Haka ba, ni fa a wauta ta ban taba kawowa cewar Zan ma rabu dashi ba, like all in the novels first love se anyi aure hakan Nima nayi tunanin a wañnan son da yake min Dole zamuyi aure it can't go in vain! I was mistaken nayi kuskure, na saka hopes dina very high shi yasa da abin yazo ya buge ni more than yadda kowa zaiyi tunani. Ranar Monday na fara classes, Dake bana beginners bane duk yawanci sun iya kawai zasu kara koya ne. Amra is very nice person, ita take fara zuwa ta tayani arranging gurin, tayi ta bani labarin Al'amin da yadda yake da yadda suke good relationship da Mummy. Abinda na fahimta kamar sunfi shiri da Maman su Akan Baban su hardly ko shi Cànîm kaji Yana zancen Baba, Amma magana dayan biyu zaka ji ance Mummy, matar is so powerful.

Ranar Thursday na Gama classes, duk sun shirya zasu tafi na fada musu Monday bana gari Kar su zo zanje hadejia, na fito raka su kamar yadda muka Saba, Ina fitowa mukai kicibis da Dada, na dafe ta Ina fadin

" Dada oyoyo!"

Tace

" Sakeni karki karya ni, Hassana Bata fita ba ko"

Na gyada kai nace

" Bata je ko Ina ba"

Ta amasa gaisuwar students Dina sannan ta shige ciki, ban wani Jima bana dawo ciki na tarar da Dada tana cewa Anna

" Isa ya Kira Baffa ya fada Masa shi Kuma yace ya nemeki Bai sameki ba nazo na fada Miki"

Bangane Kan zancen ba nayi kokarin shigewa ciki Anna tace min

" Baban ku bashi da lafiya, Yana asibiti Kuma Babu kowa a wajen shi"

Da tace Baban ku se naji I'm confused waye Baban mu? Nace

" Wai Abba?"

Na fada gabana na faduwa, Dada ta girgiza Kai tace

"Alhaji Yahai! Baban ku"

Nace

" Ayya Allah ya bashi lafiya"
Chapter 32 · 0% Book details