← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 78

Sashe 44

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na danyi kasa da kaina Ina ayyana ya Kare min kallo kenan, ya tafi na koma ciki se da nazo se Naga harda irin turaren da nake amfani dashi da abubuwa dai se na Masa godiya. Nayi mamakin turaren, ya akai yasan da shi nake amfani? Banda amsa. A cikin wannan satin suka tura, aka sanar ma baffani na Dake Masaya tuni kowa ya fara murna Unaisa lokaci yayi zatai aure, wannan abin da yayi se na saki jikina sosae dashi har bansan mun fara soyayya sosae ba, sede bana Jin shi kamar yadda nake jin Al'amin, bana daukin shi kawai dai Ina son nayi aure Kuma shi din opportunity ne da nayi grabbing kawai, a Haka Anna ke siyayya wadda bama ta saka ni a ciki, kayan kitchen da zataje sari Dubai ta siyo su tsaf bayan na fada Mata yadda nake so. Kowa na shiri Nima se na saki jiki na fara shiri, duk abinda na gani na siya, zuhra da Aseey kullum ana cikin plan din yadda zaa yarda Noorham da Aabid a cashe a bukina, abinda ke rage musu ma karsashi yadda ni din ba wani bada hadin Kai nake ba.

An saka Rana watanni takwas zuwa lokacin munyi council mun gama min huta, dukda Abba yace wata takwas yayi yawa Amma se ya nuna hakan yake so, tohm seda watanni uku  ya rage se ya samu Abba akan a Kara wata uku making six,Wai saboda azumi babbar sallah and stuffs, Abba ya tuntube ni nace ba matsala ni meye nawa a ciki, aka Kara successfully muka Gama karatu muka huta na wata biyu sannan muka koma aiki. To anan abin ya fara

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[6/13, 2:13 PM] Hauwa Galadima: *L_L*

Daga auren nayi tunanin ba zai same ni ba Amma se Naga kamar ya Raina Mana hanklai ne, bayan maganar ta fito ya Kira ni na dauka bayan min gaisa nace

" Dan Allah me yasa kake daga bikinnan, like seriously na tsani ana daga biki idan baka shirya ba tuntuni se ka Bari se ka shirya"

Ya danyi shiru na mayi tunanin ba zai amsa ni bane har na fara kokarin kashe waya ta se yace min

" Dama nasan zakiyi complain shi yasa na Kira na Baki hakuri, kinsan yau yadda take abubuwan sun Dan cushe min, I promise you ba zaa Kara daga bikin ba"

Na tabe baki nace Masa

" Allah yasa! Gobe Zan koma hadejia Zan Yi reporting aiki"

Yace

" Haka ne fa Kinga na shaafa, to Wai ya zamuyi Dake ma kina aiki a jigawa gidan auren ki na Kano"

Nace

" Naga Kun Gama magana da Abba, ko bakuyi ba?"

Yayi karamar dariya yace

" Was kidding you, muyi magana anjima goben zanzo na kaiki hadejia"

Nace

" Tohm la fada Masa"

" Wai komai kice se an fadawa Abba, me Zan Miki a cikin motar ne?"

" Me nace zakai min? Me yasa kake tsarguwa?"

" Se anjima"

Kafin ya kashe wayar na kashe tawa tare da sakin siririn tsaki, na cigaba da hada kayana Ina taunar gum a hankali, sallamar Anna yasa na aje takalman hannuna na amsa sallamar ta, ta shigo ta zauna Nima na zauna Ina Mata murmushi, tace

" Gobe se tafiya"

Na Dan Bata Rai kadan nace

" Wallahi Wai har Zan koma"

Tayi murmushi tace

" Ai duk abinda aka saka Masa Rana zai zo, Allah ya bada saa kince dakin haihuwa Zaki koma"

Nace

" Eh can suka maida ni Kinga ai nayi karatun yanzun"

Ta gyada Kai sannan tace

" Zancen Hafiz, kin Masa maganar dalilin wannan Jan auren da yake?"

Na tabe baki na fada Mata yadda mukai dashi tace

" To wannan ma abin dubawa ne, bana dai son abin ya dameki"

Nace

" Babu komai Inshaaa Allah!"

Ta zauna muna Hira Ina hada Kaya har na Gama. Da yamma na Gama gyara gida se Ahmad ya Kira ni akan zai zo. Nace Masa Ina gida, Babu jimawa se gashi yazo muka zauna mukai ta Hira nace Masa

" Wai Yaya Ahmad Wai ba zaka kaini gurin budurwar taka ba?"

Ya shafa Kai yace

" Ba kin hanani Nuzla ba"

Nayi dariya nace

" Ikon Allah! Yau Kuma sharrin kaina ya dawo"

Se ya girgiza Kai kawai yace

" Wai kinsan me ya kawo ni, wallahi medical team zaa hada Wanda zasu je aikin hajji so I thought of you, should I give you my vacancy?"

Nace cikin murna

" Kai baza kaje ba?"

Ya girgiza Kai yace

" Gaskiya kin yadda ni da yawa Dan kawai zakiyi aure, ba komai"

Na rufe bakina nace

" Ba Haka bane ba Allah"

Yace cikin marairaice fuska

" Kin manta zanje Vancouver wani aiki da aka tura ni? Date din sunyi tallying, naje Makkah uncountable is better na Baki kawai"

Se lokacin na tuna, na Masa godiya shi Kuma Yana harara ta, sannan muka rabu ya tafi, na fadawa Anna ta Kira Dada ta fada Mata kowa yayi min murna, washegari Hafiz yazo da wurwuri Dan tafiya dani, ban fada Masa ba saboda jiyan ba muyi waya ba se a Hanya nake fada Masa, kallon da ya fara min was envious look, se Kuma ya kirkiro murmushi yace

" Kice Zan Zama mijin Hajiya! Allah ya Sanya alkhairi Tawan"

Nace

" Amin"

Yace

" Kinga gwara da aka daga auren ai, Amma da kinata fada idan nasan ban shirya ba..."

Nayi dariya wadda ta katse maganar shi nace

" To ai ya wuce"

Ya gyada Kai se muka fara Hira a hankali cikin Jin Dadi, Muna tafiya Se na Kai hannuna Zan dauki ruwa Dake kusa da gear, shima ya Kai hannu ko canja gear zaiyi oho Masa, karaf se hannun shi Akan nawa, nayi saurin janyewa Amma na kasa saboda yadda ya rike hannun, na kalleshi ya falshing min wani murmushi da yasa nayi saurin dauke kaina, yasa hannun shi da baya Kan steeree ya fara bin lallaen Yana zanawa, gaba daya tsikar jikina ta tashi, I was feeling wani iri, na Kara kokarin janye hannuna na kasa dukda ban wani saka effort sosae ba, ya matso daf da kunne na cikin wata irin murya da tasa naji kamar bashi bane yace

" Hannun ki laushi, I love it!"

Na Kara lumshe idanuna gabana se faduwa yake Amma Kuma se nake jin abinda yake min da Dadi, idan na hanashi ran shi zau baci, se na kasa janyewa. Ya Allah ka yafe min! Ya Allah na tuba!! Se can kaina ya fara fada min abinda yake Yi is not right, saboda hannun shi har ya fara sama cikin rigata, nayi saurin ture hannun, Ina sakin ajiyar zuciya motar tayi wani irin shiru dukkan mu Babu me cewa wani abun se can yace

" I'm sorry! Bansan me yasa nayi Haka ba, I'm sorry"

Bance Masa komai ba saboda wani irin abu nake ji, ni Unaisa ni na Bari namiji ya taba ni yasa min hannu cikin rigata, naji kamar na kwala ihu zuciyata se tafasa take, I'm stained na ayyana. Seda muka zo kofar gidan Baffa sannan yace min

" Unaisa kiyi min magana, I dunno abinda ya shiga kaina har na taba ki. Kiyi hakuri"

Na dago na kalle shi kallon was intense cikin idanu, so nawa kawai da kaunata da Kuma nadama na gani cikin idanun Dan Haka se na amince wannan din kuskure ne, mukai sallama dukda naki sakin jiki ya tafi na shiga ciki, a tsorace na shiga saboda gani nake kowa Yana ganina zai San namiji ya taba ni, harda kuka na ranar, nayi ta istigfar tare da alkawarin motar shi ma bazan Kara Hawa ba, yazo yayi staining littafin rayuwa ta.

Babu Wanda baiyi murnar dawowa ta gidannan ba kada ma Tasnim taji labari, harda kukan ta da ta dawo daha school ta ganni. Na Shiga daki na gyara na shirya komai yadda yake, Amma a zuciyata tsantsanin kaina nake, haushin kaina nake ji, bakin ciki da tukuki nakeji. Da yamma muka shirya muka tafi gidan A'isha, ni da Maryam da Tasnim, duk a kokarin ganin na manta da abinda ya faru Amma ko sau daya ban manta ba

In takaice muku labari bansan me ya faru ba, bansan me ya hau kaina ba, bansan wanne irin abu yayi amfani dashi a kaina ba, bana son inyi blaming kaddara saboda abinda na yadda dashi Dan kaddara Bata magana ba zaa ce kullum akai Abu se ace kaddara ba, a'a akwai son zuciya saboda baiyi forcing Dina ba, kawai dai nasan ko ma menene ya cice ni ya Gama Dani, ya Bata ni ya lalata rayuwa ta, yasa min tabo da tsatsa cikin zuciya ta Kuma nayi adduar Allah ya tarwatsa tashi rayuwar.

A hankali Kuma se ya fara brainwashing Dina, sokon ci da Kuma tsoron Kar ya barni na dinga bin shi yadda yake so, na farko ya nuna min ai dama mu Yan Adam ne we sinned shiyasa Allah ya bamu damar muyi istigfar zai yafe Mana, ya nuna min cikar soyayyar kenan, bawai kawai zance kullum ba at least dai a samu touches dinnan, Kuma yace min ai ya kamata nasan Ina ne weak point Dina tunda dai nace ban sani ba. Kullum se nayi adduar Allah ya yaye min, ya shirya ni yasa na daina abinda nake, duk yadda yaso mu hadu se naki yarda a Haka dai kwatsam nayi wajen wata daya Bayan Ramadan Bayan sallah ma Dan ko da sallah kin yadda nayi mu hadu. Ranar afternoon nake so Bai zo da wuri ba se yamma yazo asibiti ya jira ni, seda na fito daga unit kawai se ganin shi nayi, ba karamin mamaki nayi ba, na nufe shi da murmushi nace

" Oyoyo! What a surprise!"

Yayi dariya yace

" Na gaji shiyasa nazo na ganki"

Na xagaya na shiga na manta duk alkawarin da nayi, a lokacin na manta ma abinda nake aikatawa Babu kyau, Ina Zama ya tada motar Muka nufi titi dukka munyi shiru se saurin Waka dake tashi a speaker din motar.
Chapter 44 · 0% Book details