← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 78

Sashe 58

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi sauri na girgiza Kai nace

" A'a fa, kawia har yanzun Anna Bata ce komai ba"

Yayi murmushi yace

" Zata ce, I promise you kede ki fara Shirin Zama amarya ta, Ina kike son na kaiki?"

Na danyi shiru Ina murmushi a hanakli nace

" Las Vegas da Italy"

Yayi murmushi yace

" Done Baby, zamu Kara wasu ma Inshaaa Allah, ko me kike so ki fada min idan Ina da Rai Zan miki ko da great Wall kike son gani"

Mun Yi Hira ranar sosae, se Bayan mun Gama wayar Naga Ashe Abba ya Kira ni call waiting, nayi sauri nayi dialing number din shi, ya dauka na gaishe shi shima ya amsa nace

" Abba I was on phone ban ga Kiran ba"

Ya girgiza Kai fuskar shi da annuri yace

" Ai na Kira shi shima naji waiting, yaushe Zaki zo gida?"

Nace

" Anna tace Wai na zauna Kar na dawo se ta Kira ni, Kuma har yanzun Bata kirani ba"

Yayi murmushi yace

" Ki Kira ta kice Mata nace tunda kina da off gobe kizo Ina San ganin ki"

Wani irin Dadi naji a zuciyata, haba Mana na kusa wata banje gida ba, na saki murmushi Ina Masa godiya sannan mukai sallama. Bayan mintina biyar na Kira Anna, Bata Jima tana ringing ba ta dauka, muka gaisa ta tambayeni aiki da mutane gida nace duk absu dawo ba.

" Anna Abba yace Wai nazo gida gobe"

Tace

" Allah ya kaimu, ya fada Miki kenan?"

Nace

"Eh ya fada min"

Tace

" To ai shikenan, se ki dage da addua kada ki manta azkhar sannan kuma se ko fada min abubuwan da Zan Kara akan wancan kayan, auren sati goma kawai aka saka"

To fa! Na gane ban gane ba! Wannan maganganun kamar suna nufin aurena aka saka Kuma ni da King Dina, kamar zanyi ihu nace

" Anna Wai Kun yarda na aure shi? Anna auren zamuyi dashi?"

Muryata wani irin farin ciki ne fal cikin ta, tace

" Ubanki! Dama Bai fada Miki ba, to shikenan nayi Miki albishir auren ki nan da sati goma"

Daga Haka ta kashe wayar, kunsan Allah tun bayan rabuwata da Al'amin ban Kara Jin farin ciki makamancin Wanda naji a wañnan lokacin ba, I was super excited, super elated kai I was euphoric. Na saki wayar na dakko daga gadon nayi sujadda, Amma nace allahumma laka sajadtu...se na kasa kawai cewa nake

" Allah nagode! Allah thank you!! Allah nagode maka!!"

Na dauki wayata na Kira shi Amma number busy, gashi Zuhra tata a kashe gaba daya, nayi tsalle nayi hamdala nayi ihu duk ni daya, I was like irin awnnn Nima dai a karshe zanyi aure, Nima zaa kirani matar aure, mutane zasu daina tambaya ta ke se yaushe Zaki aure? Zanji me ake ji a wañnan auren, Zan kalla gida inace gidan aurena ne. Nayi farin ciki har kamar Zan shide Dan dadi, naji irin burinnan da kake jira shekara da shekaru Allah ya amsa shi, se na kwanta kawai Dan bana yanayin da zanyi Sallah. Ashe bansani ba kwanakin auren na matsowa shi Kuma kwanakin barin shi duniya na gabatowa.

Ban samu Zuhra ba se dare, ita ta Kira ni lokaci daya muka furta

" Albishirin ki!"

Se mukai dariya, nace

" Fara fadar naki naji, tunda ni nawa me tsada me"

Tayi dariya tace

" Ai nawa se kin saya ma Zan fada Miki karewa"

Nayi dariya nace

" Daga baya kenan, anyways ya Zan saya?"

Tayi sauri tace

" Next week Zaki yaye Noorham!"

Na kusa zagin Zuhra nace

" To da akwai uwar da zata yaye Noorham idan bani ba, kefa kinci Kai, fada min Ina jinki"

Tace

" An saka ranar auren ki da Abiey 10 weeks"

Bazan iya ce Mata na sani ba, Dan Haka nace

" Allah ! Yaushe?"

Amma duk yadda naso mamakin da Kuma excitement din yayi sounding real se na kasa saboda na rigada nayi iyakar farin cikin da zanyi. Ta jinjina Kai tace

" Banza kin sani ashe!"

Nayi dariya na fada Mata yadda mukai da Anna, tayi ta dariya tace

" Se mu fara shiri Kinga bamu da time"

Nace

" Shirin me? Badai wani event ba? Nidai Dan Allah Zuhra karki wani tarko wani event Kuma"

Tace

" Dallah ja can, Haka zaayi bikin lami, to bazawara ce ke? So kike Yan comments section su cinye ni da Raina ko, to ba Dani ba Hajiya, biki zaayi Wanda ba zai gani ba ya bar kasar"

Nasan dasu Aseey take nace

" Zuhra Kinga Aseey dangin ki ne, kada ku Bata a kaina"

Tace

" Naji, kin yadda zaayi bikin?"

Nace

" Zan mishi magana yadda yace"

Se ta fara min dariyar shakiyanci Wai

" Inyeeee zanyi mishi magana idan ya yarda, kaga amarya a gidan ubana, amaryar Abiey, amaryar honorable"

Nayi murmushi nace

" Zaki maimaita a gaban shi yarinyar, see he's calling se anjima"

Ta min sallama sannan muka kashe na dauka Kiran shi

" Abiey na!"

Yace

" Unaisa ta, what's the news Naga se murmushi kike"

Nace

" Baka fada min ba Ashe har anyi fixing date ma"

Yayi dariya yace

" I thought kin sani fa, ankai kudi Mana"

Nace

" Se anjima ni nayi fushi da Kai"

Ban ma jira abinda Zan ce ba kuwan na kashe wayata, na kwanta Ina rungume pillow ko kadan murmushi Bai bar fuskata ba.

Washegari na tafi kano, direct gidan Badi'a na tafi, Dan Anna da Dada Basu nan sunje kasuwa, na same ta Bata je makaranta ba, na zauna muka gaisa Bayan tayi sauri ta soya min kwai ta hado min da bread da tea, tace

" Adda Ashe Abu yazo Kuma?"

Nayi murmushi nace

" Haka Nima naji"

Tayi dariya tace

" Allah ya Sanya alkhairi, Dadyn Adeel ke fada min irin kurar da akai, nasan kema kin shiga damuwa"

Nace

" Ai yadda bazai fadu ba Badi'a, Kinga yadda naji bayan nasan maganar"

Tace

" Haka Allah ya tsara Allah ya Kade fitina"

Ta amsa da Amin sannan muka cigaba da Hira, Babu dadewa naji sallamar Yaya Man, na tashi na zauna Ina maida mayafin jikina, ya shigo Yana fadin

" A'a our own Nurse kece a gidan"

Na gyada kai Ina murmushi, se ganin Muhammad nayi Ashe tare suke har da Bilkisu. Ya zauna Yana fadin

" Anty Unaisa Ina kwana?"

Kunya naji ta lullubeni nace

" Ayya! Yaya Muhammad Ina kwana, ya Afreen?"

Yace

" Lafiya Lau alhamdulillah, Allah ya Sanya alkhairi, Allah ya bada zaman lafiya!"

Nayi shiru na kasa amsa shi nayi kasa da kai, budar bakin Bilkisu se cewa tayi

" Ya kikai shiru ai se ki amsa shima, macuyiya, butulu, ke idan banda kwadayi da zarmewar zuciya Ina ke Ina Abiey, ko Dan ai Haka talaka take..."

" Shut up Bilkisu, ba ruwan ki, idan abin kirki bazai hada ku ba to ba ruwanki da ita"

Ko dagowa banyi ba balle na kalleta, Badi'a ma kasa magana tayi saboda ita tana ganin mutuncin bilkisu, tunda kuwa suna shiri sosae. Mikewa yayi yace ta tashi su tafi ya bani hakuri Suka tafi, Yaya Man ya zauna yace min

" Se kinyi hakuri, se kin dai na ji saboda bani wanda zai Miki uzuri, Amma kinsan watarana zakiga ya wuce kinji?"

Na gyada kaina, shima Bai Jima ba ya fita daga gidan ya barmu mu kadai, tayi ta bani Baki nace

" Ba komai, ai bazan taba wanke kaina ba, gwara ita abinda tace kenan!"

Bayan wajen awa daya naji knocking a kofar, Ina can ciki Ina shirya Mata Kaya cikin wardrobe ita Kuma tana zaune tana min Hira nace

" Badi'a ana knocking!"

Ta mike tace Bari ta dawo , shiru har wajen mintina uku Bata dawo ba se na fara Jin hayaniya na mike Ina aje shawl din hannuna na mike na nufi kofa se naji a kulle, Kuma Ina jin tashin muryoyi, saboda yanayin fanka yasa bana fahimtar muryar waye ba, na dauki wayata Amma na rasa wa Zan Kira, kawai na Kira Yaya Man Dan naji Yana ce Mata ba nisa zaiyi ba, se bayan wajen mintina goma naji shiru, se gashi ya bude min kofar, nace Mata cikeda damuwa

" Me ya faru?"

Yaya Man yace

" Unaisa kin fadawa Abiey abinda Aseey ke Yi Miki?"

Na girgiza Kai nace no ban fada ba, se sannan Badi'a ke fada min wai Bilkisu ce da Aseey Suka zo suna ta zage zage ta fito dani se sun min dukan tsiya, nayi shiru ban dauka abin zai Kai har Haka ba Ina ganin nayi kuskure kenan.

" Ki Kira Abiey ki fada Masa abinda ke faruwa kinji ko?"

Na girgiza Kai nace

" A'a Yaya Man, bazan hada shi da yayan shi ba, ni ba wannan ne gabana ba, Zan barsu su cigaba duniya zata fada musu daidai"

Yace

" Zan fadawa Abba kuwa, Dan wallahi duk Wanda yayi gigin tabaki se ya sani ai ba hauka akeyi ba!'

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan and send evidence of payment to 09063467258.
[6/22, 9:01 AM] Hauwa Galadima: *Y_Y*

Idan ka Suma yawanci ka Kan tashi a hankali ne, Amma ni farkawar da nayi a gigice na tashi daga gadon, Ina juyawa, Zuhra na tsaye Haka Yaya Khalifa, Haka Baba Asabe, se Kuma Al'amin dake tsaye shima Yana canja min fluid zuwa wani. Na saki kuka tunawa da nayi ba mafarki nake ba, Ina Raye ne, Zuhra ta zauna gefena tana fadin

" Ya Isa sister Haka nan, Dan Allah ki bar kuka Haka Dan girman Allah"

Nace

" Sister a ciki ya rasu in front of my eyes, he died just in there, I missed him Zuhra, na kasa mantawa kewaar shi nakeyi"

Duka sukai shiru suka barni, nayi ta kuka har seda in charge din gurin yazo ya zauna kujerar dake facing gadon da nake, dake Bayan na Fadi se suka maida hankalin su kaina, aka dauke ni zuwa nurses room dinsu da bani taimakon gaggawa.

" Me yake damun ki yanzun? Akwai inda ke Miki ciwo?"

Na girgiza Kai nace

" A'a"

" To me yasa kike kuka? Tuna shi kikai?"
Chapter 58 · 0% Book details