← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 78

Sashe 26

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansani ba ko ya fahimci excitement din dake cikin muryata, Amma dai har wani sanyi naji a cikin zuciyata da yayi min tayin zuwa ya ganni, sau biyu kawai na ganshi Amma idanuna kullum so suke su Kara ganin shi, ko hoton shi banida saboda I don't feel ok asking him, ance ya kamata mace ta dinga Jan aji ko? Ance namiji shi yake soyayyar ko? Na mace kawai tayi tagging along? Wannan shi ne abinda nayi tunanin shi ne soyayyar Amma daga baya se Naga bana cikin jerin matan da suke suppressing zuciyar su, idan Ina son Abu, Ina so tsakanin da Allah, da zuciyata, kaina, jinina, jikina da komai nawa, I love sincerely Kuma ni na dauka soyayya Abu me matukar muhimmanci a rayuwa, dukda Nasha wahala ba say daya ba ba sau biyu ba, se ace Wai na daina nayi so baya baya, to ni ba Haka nake ba, bazan iya ba banma yarda da hakan ba. Ko Dan zaku ga komai ai

" Tohm you'll always be welcome!"

" yaushe?"

Na danyi shiru se nace

" Ok! Idan baka komai!"

Se yayi murmushi yace

" Unnie komai da kike gani a rayuwa ta Banda Mummy will wait for you, I can bend anything for you Banda Mummy. So just tell me yaushe zanzo"

Wasu zasu ga kamar dadin Baki ne, ban damu ba ko dadin Bakinne ko da menene, ni dai ya Shiga zuciyata, ya sanyaya min Raina, na lumshe idanuna Ina jin I'm worthy sannan Ina jin nafi kowacce mace dacen shi, baice Yana Sona ba fa!

Na koma daki na samu Zuhra Bata nan, na cire uniform din jikina na saka wata karamar riga iya cinya, na kware sosae wajen saka Kaya kanana, indai aka ganni da Kaya complete to definitely wani gurin zanje wannan a rubuce yake. Na kwanta Kan gado na kunna kallo a wayata, wata zuciyar na fada min nayi karatun hospital final Amma nace kashe kaina zanyi? Taba kidi taba karatu! The gold empire sunan shi, it's a crime movie, na tsunduma sosae na fara kallo Ina Kara Jin kalaman Al'amin a tsakiyar kaina, lokaci zuwa lokaci Ina sakin murmushi.  Zuhra ta shigo da sauri da wayar ta a hannu, ta dubeni yace

" Kin dawo? Abiey ne yazo Yana office din provost zanje"

Na gyada Kai na Ina pausing movie din nace

" Se kin dawo, baban su Aseey ki?"

Ta gyada min Kai tace

" Ba Zaki zo muje ba?"

Na Dan yatsina fuska nace

" Kije kawai, Kinga idan zanje se min Bata wani uniform din fa"

Dake she's lazy se ta yadda, Wanda na cire ta saka ta fice cikin sauri, ba tare da Jin komai ba na cigaba da kallona a wayata. Yana zaune office din provost Zuhra ta karasa admin, aka Mata iso ciki, ta saki murmushi ganin shi tace

" Abiey Ina wuni?"

Yace

" Zuhra ta! Yau dai na ganki a uniform, you look smart and beautiful"

Tayi murmushi ya tambaya provost performance dinta yace ba matsala sannan ya mike Suka fito, yace

" Ina cousin dinki, Engineer yace min tare kuke anan?"

Tace Masa

" Eh tana wanka ne!"

Seda ya shiga mota sannan daya daga cikin securities dinsa aka sakko Mata da kayan da ya taho dasu, paper ya Bata yace ta rubuta Masa account details dinta, se ta rubuta nawa tace Masa nata ya Dan samu matsala. Ta amsa godiya, kafin ta karaso nikam har naji alert din uban kudi, Kuna Wasa da Yan siyasa ko? To ku daina. Seda ta dawo da uban Kaya sannan nace Mata naga alert from Aminu Bashir Jahun. Tace

" Abiey ne fa! Wai pocket money ne fa"

Na gyada Kai Ina mamakin babbar kyauta Haka. Cikin satin mukai finalizing yadda zamu fitar da anko, seda muka Gama hada abinda zasuyi sannan muka fitar da ankon. Da wannan kudin gurin Abiey muka siyo sample Dan nunawa, sannan muka bada wata daya a hada kudin se a siyo Bai daya. Ranar Saturday duk Wanda yazo wucewa ta kofar kitchen dinmu yasan zamuyi bako Dan kuwa Zuhra sosae ta zage dantse ita da Husna har Aisha da suka gayyato zuwa girki. Ina daki Ina goge goge da kalkale kalkale ku kwace idan yazo bude Masa jikin nawa zanyi ya kalla. Amma dai fuskata kadai ka kalla kasan ni Yar gayu ce ta kin karawa. Karfe goma daidai Kiran shi ya shigo wayata, lokacin duk sun Gama komai Dan dama yace goma zai zo. Na dauka Kuma se naji kunyar shi nake

" Naam"

" Nazo!"

" Tohm!"

Na sauke wayar a kunne na na dubi Zuhra dake gyara zaman saviette nace

" Yazo!"

Ta saki guda, ni na kasa Gane Kan Zuhra tun jiya nake Mata kashedin bafa Sona yake ba Amma Taki ji, har Aseey ta Kira da Nuzla Wai saurayina zaizo, Nuzla tace

" Amma Adda Zuhra se ki fada min tuntuni na tsiri zuwa gidan Baffa hutu"

Zuhra tayi dariya tace

" Karki damu Yar gidana Zan Miki video kauna"

Itama Aseey cikin saa ta tafi Abuja shiyasa da ita dai se ta zo wannan a rubuce yake. Straight skirt ne Wanda aka rufe kasan da net, se thigh length riga me dogon sleeve da aka rufe hannun da saman da net, atamafar tayi kyau ta Kuma yimin kyua. Kaina a tsefe yake nayi parking Kan da ya fara laushi saboda nacin gyara dukda ma naga Yana kara cika da tsayi se na maida gyaran wata wata. Nayi kyua Sosae idan ka kalleni I swear seka Kara kallona. Na Gama yafa veil din sannnan na fito ni da Aysha muka tafi inda yake. Tundaga kofar nake jin hirar su da Zuhra se dariya yake, da dai zaka rantse kace dama can sun Saba, to inaga ko ni no kaina bamu taba irin wannan dariyar dashi ba. Tun da ya hango ni ya dauke wuta, idanun shi da ban taba tunanin suna da kaifi ba naji Yana Bina dasu, na turo bakina Ina sunkuyar da Kia kunsan bana son kallo ko kadan ko Yaya ne takura min yake, Ina karasawa nace

" Zan Fadi fa, se kallona kake"

Yayi dariya a hankali cikin nishadi yace

" Kinyi kyau Unnie, you're an epitome of beauty!"

Zuhra tace

" A'a Muna nan fa, ka Bari ku gaisa dasu Husna ai"

Ya kalla Zuhra yace

" Kiyi sauri, bama lalle na gane su ba"

Aysha tace

"Naga dai Kama muke da Unaisa ai"

Se lokacin ya furta ya danyi mamaki sannan Suka tafi. Na saki ajiyar zuciya nace

" Ina Mummy? Ya Hanya?"

Yace

" Duk suna lafiya!"

Muka Dan taba Hira kadan sannan na zuba Masa abinci Yana ta complain maimakon mu maida hankali muyi karatu shi ne zamu wani Yi girki, sannan yaci shima seda na Bata Rai. Bayan anyi clearing gurin ya gyara zaman shi yace

" Unnie ni menene dinki?"

Nace

" My friend of course"

Na fada hankalina Yana Kan stones din jikin veil dina, yace

" Unnie dago ki kalleni"

Na dago na kalleshi, but idanun shi sunyi min nauyin na tsayar dasu akan shi, kunya nake ji da Kuma nauyin shi, Ina kokarin janye idanuna yace

" Ina sonki Unaisa!"

I was expecting, I wasn't expecting so still seda na Dan zaro idanuna se Kuma na Yi kasa da kaina Ina murmushi, yace

" Come on ki kalleni Mana, wannan kunyar duk ki daina. Seriously I love you, Naga kamar samari basa gabanki shiyasa nayi ta contemplating fada Miki, a karshe gashi nazo da gaske nake I'll make you mine in har kin amince Dani"

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and then send evidence of payment to 3091721807
[5/24, 10:44 PM] Hauwa Galadima: *W*

Ina Shiga gidan ban ma shiga da motar ciki ba, nayi parking a waje tareda kwantar da kaina jikin steeree Ina Kara sakin kuka, se yaushe ne? Se yaushe? Shi ne tambayar kawai da nake yiwa kaina, Amma deep down zuciyata Ina jin na kusa naji Dadi, in dai Allah ki bayarwa nasan zai bani Koda ba a duniya ba. Akwai lokutan da nayi tunanin ko dai na sabawa Allah ne shiyasa hakan yake faruwa Amma se Anna tace kada na kuskura ta Kara Jin na furta hakan. Bayan na Gama kuka na se naji Kiran sallar azahar da sauri na fito a motar na kulle sannan na saka key na bude gidan na shiga, Ina Shiga parlon kamshi ya doki hancina, dama Yunwa nakeji, se na juya tsakar gida na daura alwala sannan na dawo, seda nayi sallah sannan na leka kitchen din, tana tsaye da leaking spoon da waya a kumnenta tana sakin murmushi, nayi sallama Wanda yasa ta juyo ta Dan dauke wayar daga kunnen ta tace

" Kin dawo?"

Na karaso nace

" Na dawo, kin sha bacci"

Tace

" Wallahi! Karasa kiyi wanka kafinnan na Gama abincin"

Nace Mata to sannan na juya Dan fita ta Dan daga murya tace

" Adda"

Na dawo ta aje wayar ta tace

" Kuka kikai ko? Kiyi hakuri Dan Allah bana Jin dadin ganin ki a Haka"

Na gyada Mata kaina kawai bance komai ba na wuce daki. Nima baa son Raina nake hakan ba kawai kukan sh ne kadai abinda nakeyi nake samun sauki Dan Haka indai kuwan zanji sauki a zuciyata to tabbas Zan Yi ta kuka Banga ranar da Zan daina ba. Nayi wanka na shirya cikin brown din material me fuschia pink a jiki, skirt da riga, na tsaya Ina kallon kayana da suke a jere neatly, na tuna yadda na dinga cin alwashin kwalliyya da cakarewa Amma gani nan takaba nake. Na lumshe idanuna Jin karar doorbell, na sako hijab na sakko se naji muryar Zuhra hakan ya tabbatar min biyo no tayi.

" Ki dinga Jin tsoron Allah! Maimakon ki tafi gida shi ne Kika taho nan ko?"

Ta kalleni Amma se tayi murmushi tace

" Na zata Zan same ki kina ta kuka, shiyasa hankalina yaki kwanciya, alhamdulillah"

Nayi murmushi nace

" Banyi tunanin ganin shi ba, Dana ganshi kawai se naji rauni a zuciyata, bansan dalilin ba"

Ta Dan dafa ni tace
Chapter 26 · 0% Book details