← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 78

Sashe 19

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da yamma na Gama dakko ma Zuhra Kaya, tana zaune gefen gado tana shafa powder, ta dauki atamfar ta saka, tayi kyau sosae mashaaa Allah, na dauki wayata na kashe Mata pictures sannan na juye chilled zobon Dana hada Masa cikin jug, se na jera finger food din da mukai order na rufe da cling film. Husna Dana Kira tazo ta dauka muka fita zuwa inda yake kafin ita gimbiyar ta fito. Yana zaune cikin cafeteria school, ya bada baya da waya Kare a kunnen shi, muka cigaba da tafiya har muka Isa seat din, na saki fuska Ina gaishe shi ni da Husna, Yana dagowa idanun shi cikin nawa yace

" Unaisa?"

Nace

" Sorry! Ba gurinka muka zo ba"

Nasa hannuna Zan dauke basket din, kunma San Wai wa na gani? Wannan mutumin da mukai gware a asibiti me azabar kallo dinnan, Husna ta zungure ni tace

" Shi ne fa dallah!"

Na harareta shi Kuma se kallon mu yake barin ma ni na e

" Wannan din? He doesn't deserve her"

Na juya da niyyar tafiya Se ga Zuhra tana taku daya daya, ni kaina seda na shagala Ina kallonta balle shi Kuma, ta karaso bakinta ya kasa rufuwa, na kalleta na Kuma kalle shi Naga kallon da yake Mata na kauna se naji contemplating da nake akan son da yake Mata ya tafi, na aje basket din ta karaso tace

" Sannu da zuwa"

Ta zauna mu Kuma muka tsaya kamar zakaru,

" Wannan ce Unaisa Taki? I've finally meet her"

Tayi murmushi, muka gaisa sannan na juya na tafi, Husna tace min

" Wai me yasa Kika Masa abinda kikai dazun?"

Kawai nayi shiru bance komai ba, se yamma ta kirani zai tafi , Nima na fito Amma ban saki jiki ba se tayi tunanin rashin sabo ne tunda dama Haka nake, na karba kayan muka tafi hostel,

" Unaisa Yaya? Yayi?"

Nayi murmushi nace

" Yayi mana! Karshe ma"

Tayi tsalle hade da fadin

" Na iya zabi"

Na Harare ta nace

" Se ya ganki kina tsalle ai"

The next day bayan karfe goma an Gama rounds na fito zuwa Doctor's common room, Ina Isa na iske Dr ishaq a tsaye da wani guy suna ta dariya, na gaishe shi sannan nace

" Dan Allah Dr Khalifa nake nema"

Yace

" Yana ciki, ayi mishi magana?"

Na gyada kaina, baa Jima ba se gashi ya fito hannun shi da mug din coffee, Muna hada idanu yace

" A'a sister mu ce? Sannu da zuwa?"

Na amsa Masa se mukai shiru se shi yace

"I hope I'm safe?"

To me zance masa? Nace Masa me yasa yake kallona ko Kuma nayi questioning son da yake ma Zuhra, se na ga wauta ta Amma Kuma Zuhra ce, Ina son tayi farin ciki. Kamar yasan abinda ke Raina se Naga ya Ciro wayar shi ya danyi scrolling kadan sannan ya Miko min tare da fadin

" Nasan kina tunanin me yasa nake kallon ki duk lokacin da muka hadu ko? You look exactly like my sister! Kalla hotin ta"

Na saka hannuna na karba, subhannallah! Shi ne abinda na furta she sure looks like me sosae kuwa, banbanci mu shekaru ne kawai, yace

" Da ace wani zai ganki zaice ita ce, kullum na ganki se Naga kamar ita ce shiyasa nake Miki wannan kallon Amma da gaske Ina son Zuhra Kuma auren ta zanyi"

Na sake ajiyar zuciya na relief na bashi hakuri, yayi dariya yace

" Haka kike son Yar uwarki, naji Dadi. Ya aikin?"

Nayi murmushi nace

" Alhamdulillah"

Daga Haka Kuma se na Masa sallama na tafi, Bayan na tafi hoton yarinyar da bansan sunan ta bane kawai a idanuna, how on Earth zamuyi Kama irin wannan? Ta Yaya? Se Kuma wata zuciyar ta kwabe ni da fada min ba Allah ne ke hallitta ba? Then everything is possible. Banyi magana da Zuhra akan hakan ba se da daddare nake fada Mata tayi dariya kawai Bata ce komai ba. Wannan weekend din kuwa Muna tashi daga asibiti muka daura abaya akan farin uniform dinmu, idan ka ganmu baka ce daga asibiti muke ba bamu jira kowa yazo daukar mu ba, muka ma Kano tsinke. Tun a Hanya munata Hira, danmu dai hirar mu Bata taba karewa,

" Idan mukaje zanyi ma Anna zancen Doctor, ko ya Kika gani?"

Na gyada kaina nace

" Hakan yayi kuwa, Kinga gwara ace ansan kina tare dashi"

Muka danyi planning yadda zamu samu Anna da maganar Bayan mun Gama nace

" Nikam Zuhra wani abu ya tsaya min a raina"

Ta Dan kalleni kamar me son karanta Rai din nawa tace

" Warris that?"

Nace

" Sister Doctor, have you seen her picture?"

Se ta dakko wayar ta ta Miko min, ya ilahi se yanzun na Kara ganin kamar tamu, na dube ta nace

" Baki jin kamar akwai wani Abu, like irin ko we're related hakan?'

Se tayi shiru kafin Kuma tace

" God! Haka ne fa, Allah na manta, Kuma yace min da kakar su ta gurin Baba take Kama, likely..."

Na gyada kaina, se muka Bari akan zamu Masa magana a hankali, muka fara Jin kanmu kamar wasu legend a cikin family, tunda mu mukai uniting family din wannan kenan.

  Gidan Anna muka sauka Dan anan muka samu Dada, seda muka ci abinci sannan mukaji labarin Ashe sallama zamuyi da Anna zata tafi Dubai, zata fara saro Kaya, nayi ma Allah godiya Babu adadi, tabbas arziki da Kuma daukaka ta Allah ce!

Unaisa is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First Bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[5/20, 12:21 AM] Hauwa Galadima: *Q*

Ranar lahadi da sassafe jirgin su Anna ya tashi, ba karamin kewar ta mukai ba, Dan dukka seda mukai kuka, daga nan Dada ta wuce damu gidan ta, Dan dama ta rigada ta tafi da kayan su, ganin ana wannan Shirin tafiyar yasa bama mu musu maganar Dr Khalifa ba. Da yamma muka koma hadejia, a Tasha yazo ya dauke mu

" Sweet nikam Baffa Bai taba ce muku Yana da Yan uwa da ya rasa ba?"

Ya Dan kalleta sannan ya maida Kan shi Kan driving din da yake yace

" He always says that, ko yau da safe seda yayi maganar, yace idan Yana kallon A'isha gani yake kamar mahaifiyar shi ce"

Se Zuhra ta juyo ta kalleni se na gyada Mata Kai alamar ta sako Masa maganar se tace

" Ni da Unaisa iyayen mu Mata uwar su daya uban su daya, kasan me Basu ma San juna ba kasancewar Dada Bata ma San an Haifa Anna ba, kamannin Unaisa yasa Dada ta gane cewar Anna Yar uwar ta ce"

Parking yayi saboda lokacin mun riga da mun karaso cikin makarantar, muka fito dukkan mu, ya dubeni sannan ya maida hankalin sa Kan abinda Zuhra ke cewa yace

"Baffa mentioned Zainabu da Zulai, Dan a gidan mu Muna da kanne hakan"

Na Dan ware idanuna na ayyana wannan bazai Zama coincidence ba, Zuhra tace

" Sunan Dada kenan Zainabu, se Kuma inna Zulai da ta rasu, na tabbatar Baffa shi ne Yayan su Anna da Dada ke fada"

Yayi saurin bude motar shi ya shiga, na dube shi Ina iya hango excitement yace

" Then ni Zan fara fada Masa wannan labarin"

Bai ma jira amsar mu ba yayi gaba, kayan da muka zo dashi na motar Haka muka wuce hostel muna Jin kamar mun fi kowa amfani da hada Kan dangi, Ina ma Anna na nan taji wannan labarin. Se dare mukai shawarar fadawa Abba, Zuhra ta fada Masa yadda ya fahimta yayi Mata alkawarin washegari Yana hanya.

Washegari ya kasance 12th May ranar Babu makaranta, Babu lecture Babu Kuma clinical posting saboda wannan ranar ce Nightingale day, mu Nurses muna celebrating ranar na birthday Florence Nightingale as the founder of modern Nursing science. Dan Haka Bayan munyi breakfast mukai wanka, na shirya cikin maroon din skirt da riga na lace, itakuma Zuhra ta saka wani fuschia pink din silk material, ta Kira Doctor, bayan sun gaisa tace

" Sweet ya kukai da Baffa am?"

Yace

" Se dare sosae ya dawo, Kuma lokacin na same shi se yace min Dan Allah na bar ko meye zuwa safe"

Ta gyada kanta tace

" Kada ka barshi ya fita, su Abba sun wuce Yan leman!"

Daga Haka sukai sallama ta dubeni nace

" I just hope hakanne Kar mu saka musu Rai"

Tace Amin. Babu jimawa muka same su a bakin gate, Abba a gaba se Yaya Man a driver's seat se Dada da Yaya khulthum a baya, muka shiga muka gaishe su, Dada ta dubeni tace

" Wai meye kuka saka muka zo garinnan Naga jiya kuka tafi?"

Nan nasan Bata masan abinda yake faruwa ba, Abba yayi saurin fadin

" Naga dai nace Miki kiyi hakuri, zakiga koma menene"

Se tace

" To Abba nayi shiru"

Muna Isa muka samu Doctor a kofar gida yana jiran mu, mukai parking dukka muka fito, se wani kallon kallo suke shi da Zuhra Wanda a lokacin gani nake duk iskanci ne se daga baya na fahimci they should do more than hakan. Har kasa ya durkusa ya gaida Abba da Dada, sukai musabaha da Yaya Man sannan ya gaida Yaya khulthum. Muma muka gaishe shi yayi Mana iso ciki, katon gida ne me kyan gaske, wani katon parlor muka shiga, muka samu dattijo a zaune ya girmi Abba sanye da farar jallabiyya hannun shi rike da mug din tea, se wata Mata da Bata wuce saar Anna ba zaune gaban shi tana zuba Masa chips da omelette, sallamar mu ta katse Masa fadin

" Wai Ina Khalifa ne? Shi ne yasa ban fita ba har yanzun..."

Ya karaso ciki Yana fadin

" Baffa am gani, kayi Baki"

Ya dago Kan shi Yana kallon su daya bayan daya, ni ban shigo ba na tsaya amsa call din Yaya Ahmad, seda yazo Kan Dada wadda tayi mutuwar tsaye sannan ya dakata tare Kuma da mikewa tsaye yace

" Zainabou!"

Jikin shi har kakkarwa yake, itama jikinta na rawa tace

" Maharazu! Kana nan dama"
Chapter 19 · 0% Book details