← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 78

Sashe 54

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Haka sukai sallama ta tafi, tana zuwa ta tarar Abba Yana jiran ta, ko Kaya Bata cire ba tace

" Daga gidan Hassana nake, Wai Kuma honorable ke Neman auren Unaisa kuam?"

Abba yace

" Seda nace ma Unaisa kada ta fada Mata, ta jira na Mata magana"

Se kawai Dada tace

" Shi yaje da Kan shi, Abba me kayi deciding? Me kake gani zaayi?"

Yace

" Bansani ba Zainab, wallahi Allah I'm confused, Kuma from all indication suna son junan su"

Dada tace

" Muyi addua kaji, inshallah komai zai zo da sauki"

Ko da na tashi se naji sauki sosae cikin Raina, nayi ta karanta addu'oi Dan na samu sauki cikin zuciyata, Haka nan kuwa na dinga Jin sauki na koma daki na kashe wayata.

Bangaren Abiey se wajen Tara na dare ya koma gida, ya samu dukka suna gida, ya shigo fuskar shi Babu yabo Babu fallasa saboda yayi ta kirana wayata ba ta shiga alamar na kashe kenan. Ya zauna suka gaisa da Muhammad ya duba time yace

" Idan Babu wani important Abu da kake Yi ya kamata ka tafi ko?"

Ya mike Yana murmushi yace

" Dama Abiey jiran ka nake mu gaisa na wuce"

Ya gyada Kai yace

" Allah yayi muku albarka"

Daga Haka sukai sallama ya wuce sama Yana cewa Mamaa ta same shi a daki, he needs to discuss something with her, ita kuma ta tsaya korawa Muhammad bayani, kafin ta karasa dakin Abiey ta samu har ya shiga wanka, ya bar wayar shi da ya Gama kirana akan gado Kuma Bata shiga lock ba, ta Kai hannun ta ta dauka " Beautiful" ne rado rado last call din shi, ta fara scrolling kasa Amma

" Beautiful!"

Kawai take gani, idanun ta sukai wani irin dishi dishi ta samu guri ta zauna tana gyara zaman glasses idanun ta, ta fita zuwa messages nan tayi searching Beautiful take kuwa thread Dina ya fita, tabbas messages din da ta karanta da tana da hawan jini zai tashi, ko Kuma da zaa gwada jinin ta a lokacin to tabbas ya hau. Ta share wani gumi da ya keto Mata tare da daga idanu ta dubi air-conditioning Dan ta tabbatar ko tana aiki, 16°c take reading Dole ta mike ta kunna standing Dake gefe a wata kusurwa, wani iri takeji, wannan ba gaske bane, bazai taba Zama gaske ba, ba mijin ta ba sede wani, ta Yaya? Ta shiga gallery Dan duba WhatsApp images, Amma kafin ma ta bar camera ta hangi hotona, bansan yaushe yayi ba bansan yaushe ya dauka ba balle har nasan Yana aje cikin wayar shi ba. Tayi zooming hoton gaban ta ya dinga faduwa ita tasan fuskata Amma so take ta tuna Ina ta sanni ma, kamar a bikin Aseey ko? Kafin kwakwalwar kanta ta Gama booting se gashi ya fito, Bai lura wayar shi hannun ta ba seda yace

" Sorry I kept you waiting"

" Wacece Beautiful?"

Ya dubeta sannan ya kalli hannun ta yaga wayar shi a hannun ta, yace

" This is trespassing! Kin sani ko?"

Ta mike tsaye tace

" Ka fada min wacece Beautiful? Who the hell is she?"

Ya kalleta kawai se ya girgiza Kai yayi murmushi ya nufi wardrobe Dan daukan soft pyjamas din shi, ta karaso inda yake tabbas mace Bata girma da kishiya, tace

" Magana nake maka, who the hell is she? Me kake da hoton karamar yarinyar a wayar ka?"

Yace

" Son ta nake auren ta zanyi, are you ok?"

Ta rike hannun shi tace

" Wallahi baka isa ba, wallahi kayi kadan baka Isa ba"

Yace

" Talatu ki zauna muyi magana ta fahimta"

Ta kwace hannun ta tace

" Maganar fahimta? Wallahi baka isa ba, aure zaka Kara?"

Ya Kara rike hannun ta Dan ta saurare shi Amma ta tauburr wayar shi dake hannun ta ta hada ta da jikin bango ta sakko kasa ta baje, ta tashi aiki, Yana kallon ta baice uffan ba tace

" Na rantse da Allah Babu wata mace da ta Isa ta shigo wannan gidan, har ka Isa ma"

" Talatu ki saurare no"

" Bazan tsaya ba, me zaka ce min. Saar Aseey? Ita zaka aure, honorable shekarar mu nawa? Se yanzun zaka min kishiya. Ka cuceni"

Baice komai ba ya Barta ta Karaci abinda zatayi ta gama, ta fita sannan ya lumshe idanu, ya dauki karamar waya ya Kira chief security din shi yace ya samo Masa sabuwar waya a wañnan daren!

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 First Bank of Nigeria A'isha kwalam Hassan and send evidence of payment to 09063467258.
[6/19, 3:01 PM] Hauwa Galadima: *U_U*

Tana shiga daki kamar mahaukaciya ta dauki wayar ta ta fara Kiran Aseey,a cewar ta ciwon 'Ya mace na 'ya mace ne, Aseey kawai zata fahimci hakan, Bata duba karfe nawa ba kawai ta kirata, se aka samu tayi bacci wayar Kuma a silent take. Ta mike tana tunano fuskata Amma ta kasa tuna inda ta sanni kamar an tsikare ta ta janyo wani katon album na bikin Aseey, ta dinga budewa Babu jimawa taga hotona a zaune gefen beach, na saki murmushi exactly irin Wanda nayi a wayar shi, ta Ciro hoton ta Kura min idanu, a take memories dinta Suka dawo Unaisa sunan ta, yarinyar kanwar Zainab da Suka taba zuwa itada Zuhra, Kuma ta taka rawa muhimmiyar gaske a bikin Aseey, me honorable yake son aikata mata kenan? Yar cikin shi? Kawar Yar shi zai kawo matsayin kishiya, wallahi ko sama da kasa zata hade ba zaayi auren nan ba, wannan alwashi ta dauka, da baayi Mata kishiya Haka yanzun ma Babu uban Wanda ya Isa. Ta mike ta fito zuwa dakin shi, bacci har ya fara daukar shi yaji an banko kofa, cikin sauri ya farka, ta kunna chandeliers da tasa idanun shi saurin rufewa saboda light din d yayi yawa, ya kalleta, she looks pitiful se tausayin ta ya Kara Kama shi, Bai so suyi Haka ba, shiyasa yayi niyyar yu Mata bayani a yau dinnan da kanshi kafin maganar ma ta fita. Ta wulla Masa picture din yayi landing a fuskar shi tace

" Unaisa zaka aura? Kasan wacece ita? Kasan kawar Asiya ce? Wannan wanne irin abin kunya ne?"

Ya dauki hoton yasa karkashin pillow dinshi yace

" Ki zauna magana zanyi miki"

" Ba Zan zauna ba macuci azzalumi"

Ya riko hannun ta ya zaunar da ita tare da rungume ta a jikin shi, tayi kuka sosae ta hakura yace

" Nasan Zaki Haka shiyasa naso muyi magana a tsanake, I'm sorry Amma dama ban taba cewa bazan Yi aure ba, wannan yarinyar is innocent Bata San komai ba, abinda ta sani Ina sonta Zan aure ta Kuma tana Sona. Ki sani no dake abinnan ya shafa, duk abinda Zaki ya tsaya kaina kawai Dada drag her please
na iske waya da Baffa na  mmmmm  a a  Haka Allah ya tsara Masa, kiyi addua kinji"

Na gyada Kai na nace

" A

Ba tCe min komai ba se kawai na mike na Mata sallama, na dauki wayata Ina jin kewar muryar shi, nasan ya Kira yafi a kirga, nasan hankalin shi duk inda yake ya tashi, I need to sort things out tukunnna. Nuzla ta dubeni tace min

" Adda indai kina son shi wallahi karki rabu dashi, se yaushe ke Zaki farin cikin kanki, kullum sadaukar wa zakiyi, ni Zan ma Annan magana"

Na girgiza Kai abuna kawai Ina murmushi bance komai ba. Se Dana dauki Kaya na sannan na Mata sallama na tafi. A mota na kasa jurewa na kunna wayar Amma Kuma Babu message din shi, na damke wayar a hannuna, I missed him. Na Dan lumshe idanuna Ina jin idan mahiafina ne zai auri kawata ya zanyi, se na kasa ayyana komai tunda ni bansan dadin uba ba, Amma nasan Babu dadi Abu ne da Babu dadi kwatakwata, se naji ko na bar musu baban su kawai, se Kuma na tuna masoyi na, sarki na me mulkin zuciyata, ire iren farin cikin da ya sakani a ciki ba zasu taba misaltuwa ba, shin Zan iya rabuwa da hakan?karar wayata yasa nayi saurin bude idanuna, duk tuannai na ma shi ne se Naga Zuhra ce, itama Bata Kira nu ba, se na dauka muka gaisa tace

" Naji kamar kina Hanya?"

Nace

" Mhmm zan koma hadejia"

Tace

" Muyi waya idan kinje Dan Allah, Allah kiyaye Noor na gaishe ki"

Mukai sallama na cigaba da tunani na, ni daya a raina a rayuwa ta duk na dagula rauukan mutane. Isata hadejia Babu kowa gida se kawai na wuce gidan Aisha Dan nasan Zama ni daya ba zaiyi ba, tunda muka gaisa na kwanta Kan kujera na lumshe idanuna kamar Mai bacci se ta kyaleni, banfi awa daya ba se gashi Anty Yusra ta kirani na dawo gida sun dawo suma. Na mike kenan waya ta ta fara ringing, nayi saurin juyata, a take wannan kibuyin suka soke ni a zuciyata, na saki wani murmushi, naji wani irin farin ciki ya ziyarce ni.

" I missed you!"

Shi ne abinda na fara fada Masa, yayi murmushi yace

" I can see an kashe min waya ai jiya, ko tausayina Baki ji"

Nace

" Kai Abiey ba Haka bane bafa"

Ya bude idanu yace

" Did you call me Abiey, Dan Allah karki Kara se kace wata Aseey?"

Nayi dariya mukai Hira sosae, to Wai ta Ina Zan iya rabuwa dashi ne ma, wannan ai ragon zance ne. A ranar se naji zuciyata tayi sanyi ko da Zuhra ta Kira ni se tace washegari zata zo hadejia, ita dai tafiya Bata Mata wuya sede idan bani bace a cikin matsala. Washegari da wurwuri Zuhra tazo Muka kule cikin daki, Bayan mun gaisa na zaunar da Noor Kan cinyata Ina Bata caprisonne

" Me kike planning?"

Na dubeta nasan tanbayar Akan Abiey ne nace

" Bansani ba, har yanzun ban yanke hukunci ba, Amma Ina jin rabuwa dashi tayimin nauyi"

Ta gyada kanta tace

" Carry on! Karki rabu dashi"

Na kalleta da mamaki nace

" Zuhra Ahmad fa? Kunyar su nakeji"

Tace
Chapter 54 · 0% Book details