← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 78

Sashe 52

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na daiyi shiru saboda bana son maganar, Abba ya fahimci hakan se yace

" To me muka samu Unaisa? Nasan wannan ganin nawa akwai magana"

Na fara murmushi rasa yadda Zan fara fada Masa se yace

" Ni ne Abban fa, fada min menene?"

Nace

" Abba dama wani ne yace Yana Sona"

Ya kalleni yace

" Mashaaa Allah that's great! Who's that guy"

Na fara Wasa da hannuna Ina ayyana ta inda Zan fara se wayar shi tayi ringing, ya dauki wayar yace

" Lemme answer"

Fuskar shi da murmushi yace

" Ran honorable ya dade! Anjima nake son shigowa mu karasa maganar nan"

Se yayi dariya yace

" Wai da gaske? Ina gidan ai, Bari na shigo da Kai"

Yayi dariya yace

" A'a wannan maganar babba ce, to ka karaso"

Ya kashe wayar Yana dubana yace

" Unaisa nayi bako, ko Dan ai baban ki ne ma, baban su Ahmad ne, ki jirani parlon Dadar ku idan na Gama Zan same ki can"

Na mike Ina son Naga mutuminnan da baya son hayaniya ta bakin matar shi, nace

" To Abba!"

Ina gyara zaman veil Dina se naji wannan muryar tashi yayi sallama kofar parlon, a razane na juya se fuskata akan tashi, shima se Naga Yana min kallon mamaki, irin what are you doing here? Na kalleshi hannuna har rawa yake, Abba Bai ma lura Dani ba yace

" Honorable honorable sannu da zuwa!"

Ya Dan daga Masa hannu yace

" Unaisa what are you doing here?"

Shi Abba Bai kawo komai ba Dan tuannin shi ai munsan juna, yadda nake da yayan shi. Gaba daya naji wani irin abu ya tsaya min, tamkar duniya ta tsaya, shi ne mahaifin Aseey da Ahmad? Shi ne Uncle din Zuhra? Brother din Abba? What's this? Meke faruwa ne?

" She came to introduce me to someone ne, ka zauna Mana"

Abiey har lokacin Yana tsaye yace

"Ita ce yarinyar da nace maka Zan aura..."

Nayi saurin daga kafafuna Dan fita Abba da ya tsaya shima in shock yace min

" Unaisa dawo"

Na dubi Abba idanuna har sun ciko da kwalla nace

" Allah Abba bansan baban su Ahmad bane, I never know. Abba bansani ba"

Yadda na rikice gaba daya yasa Abiey Zama yace

" Ismail me yake faruwa, how do you know Unaisa, ya kuke maganar su Ahmad"

Nayo saurin fita ba tareda na jira me zasu ce ba, kafata kawai nake cillawa Amma ba game inda nake takawa nakeyi ba. Ina zuwa parlon Dada na zauna na takure Kan kujera, Ina ayyana how could this be? Ya ma zaayi ace Baban Ahmad ne saurayi na,gaba daya kaina ya kulle na rasa tunanin da zanyi . Na Ciro wayata na Kira Zuhra ta dauka dama jiran Kiran take, tana dauka na saki kuka nace

" Zuhra I'm in a mess! Zuhra ban sani ba wallahi, Allah Zuhra ban sani ba"

Cikin rashin fahimta tace

" Unaisa keep calm, me ya faru kimin bayani. Meye Baki sani ba? Kimin bayani"

Nace

" Zuhra Wai saurayina, wannan da nake fada Miki, wannan da nake so... Na Shiga uku, na shiga uku Life is so unfair to me"

Gashi kuka nake Kuma naki Mata bayani, se ta fara roko na na fada Mata abinda yake faruwa

" Zuhra Wai shi din da Wai Baban su Aseey da Ahmad ne!"

Dif naji tayi shiru na tabbatar kokarin assessing abinda na fada takeyi, se wajen bayan 30 seconds sannan tace

" You're kidding right, kina nufin Abiey ne Wanda kike magana akai? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!'

UNAISA is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[6/17, 10:32 PM] Hauwa Galadima: *S_S*

" Unaisa matsayin 'Ya take a gurina, mahaifiyar ta ita ce kanwar Zainab, ai nasan baka manta fuskar mahaifiyar zainab ba? Nasan shaafa kayi shiyasa baka tantance fuskar ba. Unaisa kawar Zuhra ce, kawar Asiya ce sannan aminiyar Ahmad, kadan kafin ka tafi saudiyya ban Kira ka nace maka nayiwa Ahmad Mata ba, I wanted to hook them saboda yarinyar Tasha wahala she was betrayed, Amma se Taki yarda. Shiyasa kaga ta rikice Bata Sanka ba, Bata Yi tunanin Kai din mahaifin aminan ta bane"

Abba ya Gama wannan dogon sharhin, Abiey kawai kallon shi yake har ya gama, shi hankalin shi ma ya kasu biyu Yana Jin sharhin Abba sannan Kuma Yana tunanin halin da nake ciki, a Dan lokacin da ya sannu ya fahimci I'm fragile sosae, ya fahimci Abu kadan ke daga min hankali.

" She talks about you da farko nayi tunanin Kai ka haife ta,se daga baya tace min Kai uncle dinta ne. Duk wannan doguwar maganar Ismail me kake so kace, na hakura? Na janye na fasa auren ta?"

Ya girgiza shi Kan shi he's confused, Yana tuna danganta ka ta dasu Ahmad, zai Kuma so ace Dan uwan shi ya samu abinda yake so, musamman yadda yake zance on and off,idanun shi kadai shows the desperation da yake ciki, Amma Kuma idan aka hanga ya kamata a hango,ya kamata a duba aga Unaisa Kuma fa? Yarinyar ce ni with a golden and soft heart banida nufin cutar da kowa, I'm just craving for love. Mamaaa fa ? Zata iya komai Dan ganin ta Hana aurennan he will never want me to be broken again.

" Ka hakura, Dan Allah honorable ka hakura kawai"

Yace cikin dakewa

" Bazan iya ba, na Mata alkawarin Zan aureta Zan faranta Mata rai, na Mata alkawari I can't break her heart, a labarin data bani she's suffered enough"

Abba yasan halin Abiey, Yana da kafiya da naci akan Abu, shiyasa he prosper yadda hankali Bai tunani. Cikin lallashi yace

" Asiya ba zata ji Dadi ba ka auri kawarta, Haka Ahmad ma. Kasan vacancy Ahmad Unaisa taje hajji? Ahmad ya Bata kujerar shi"

Yayi murmushi yace

" Kace min Aminu ni Ismail bazan baka auren yata ba that's all! Ki Ahmad Bai bada kujera ba it's written se min hadu, se Kuma munyi aure I'm determined"

Abba ya runtse idanu yace

" Ba Haka bane, wallahi I'll love ka aureta, ni kaina hankalina zai kwanta na Mika ta hannun Dan uwana, Ahmad nake tunani"

Abiey ya mike yace

" Wallahi! Wallahil azim!! Ko Ahmad ke son ta ya rabu da ita, Zan aure ta saboda Ina son ta, nasan tana Sona so ya rage naka kayi deciding, idan kaga na janye, Beautiful da kanta tace Bata Sona ba zata aureni ba, a wañnan na maka alkawarin fita harkar yark And please check on her she must be disturbed now, I want to see her!"

Abba ya jinjina Kai, baya tunanin yayan shi zai janye wannan maganar, yadda yake tunanin abin da sauki to ya wuce Haka, ya mike ya dafa Shi yace

" Kayi hakuri Doctor! Kayi hakuri Zan baka Unaisa da yardar Allah, Amma ko zaka samu zainab ka fada Mata"

Babu kunya ya saki murmushi yace

" Tana ciki ne?"

Ya girgiza Kai yace ta fita, ya Masa alkawarin dawowa da dare Dan magana da Anna, Suka nufi sauka daga stairs shidai Abba har lokacin Yana cikin mamaki ne, Haka Kuma ya rasa yadda zaiyi, ya lumshe idanu Yana ambaton Allah ya kawo Masa dauki. Har sun sauka kasa se ya juya yace

" Ka Kira min ita please!"

Ya fada Yana hada hannayen shi biyu yace

" Tunda yanzun ka Zama siriki na!"

Sukai dariya dukkan su, Abba ya juya yana Kara gaskta tsarkin mulkin Allah, waye zai kawo wannan mutumin zai so yarinyar Yar karama Haka? Ya tuna lokacin Samartakar su, lokacin yaje London yayi medicine ya dawo, shi Kuma Abba ya Gama accounting and finance a Spain, Abiey Suka dawo baban su yace su fitar da Mata suyi aure. Tun can su masu arziki ne, tamkar arziki gada sukai Haka abin yake, baban su me kudi me Dan Boko Kuma shiyasa duka har Mata Yayan shi sunyi karatu. Abba yace baida zabi saboda shi baida shiga mutane, Abiey ya zabi Mamaa ita Kuma Yar abokin baban su ce da tunda Suka taba zuwa Jahun take yawan zuwa har Suka fara shiri sosae da Abiey har dai kowa yasan soyayya suke, tana da kanwa Shamsiyya ita take binta, tunda aka saka rana ta fahimci Abba bashi da budurwar da yayi presenting take cusa Masa Shamsiyya Abba yaki, daga karshe yaga Dada kallon farko ya fadawa Baban shi akai aure, shi ne dalilin da yasa Mamaa ta tsani Dada, ganin ta da tuni ita da Shamsiyya ke juya gidan. Abiey na da high taste akan mace idan yace Yana son wannan abin to ka kalli abun tabbas yakai, to yanzun ma Abba baiyi mamaki Dan Yana son Unaisa ba, Dan kuwa yasan se namijin da ya San kanshi zai gane cewar Unaisa ta dace dashi.

Gabana ya cigaba da faduwa Ina jin sallallami da salatin Zuhra kafin Kuma ta kashe wayar, whta do you expect? Ta amince ta goya min baya na auri kawun ta, na Zama kishiyar uwar favourite cousins dinta? Na lumshe idanuna Wanda ya bawa hawayen idanuna damar sauka kuncina, wani iri nakeji, me yasa kaddarata take da tsauri? Astagfurillah Allah na tuba Ina Neman sassauci. Na kasa shesheka se hawaye dake gudu Ina hango Ahmad da dariyar shi da fara'ar shi gare ni, se na saka Masa da aurar ubansa? Nasan banida laifi Amma ya zanyi yanzun? Sallamar Abba tasa nayi saurin mikewa, ina goge hawayena, ya kalleni cike da tausayawa yace

" Ki daina kuka, kiyi addua Allah ya zaba mafi alkhairi"

Nace

" Abba ban taba sanin he's Aseeys' father ba, wallahi ban sani ba"

Yace

" Na sani, is not a crime kinji, ki daina jin kamar kinyi laifi, as far as kina son shi I'll support you, I'll Marry you off to him kinji"

Se naji sanyi a raina ko ba komai na samu mahaluki daya ya goyan baya na. Na share hawayen Amma Ina tuna Anna, dasu Ahmad ya zasu ji, me Zan fada musu? Innanlillahi!

" Kizo Yana Kiran ki"

Nayi sauri na girgiza Kai na, Abba yayi murmushi yace
Chapter 52 · 0% Book details