Sashe 12
Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunsan yadda Dada wasu lokutan Kam Jima ita daya a daki yasa Koda sukaga Bata fito ba Zuhra ma Bata neme taba, se wajen maghrib Zuhra ta fito bayan ta idar da sallah Dan zuwa Kama aiki a kitchen kamar yadda suka saba, tana Shiga ta Kai idanunta Kan stool din Dada ke Zama tana monitoring yadda ake hada abinci, taga wayam, ta dubi Baba ladi tace
" Dada Bata fito bane?"
Baba ladi tace
" Eh Amma tace Zaki zo ayi Dake"
Zuhra ta zauna har ishai aka Gama komai sannan ta nufi dakin Dada, Bata parlor se a bedroom ta sameta,
" Dada wani abu ya faru ne? Kinzo daki kin kwanta Kuma"
Ta Dan dago da fuskar ta me cikeda damuwa tace
" Babu komai, kiyi ma Abba setting table Zan shigo"
Ta danyi Jim kadan tana kokarin karantar Dadan Wanda fahimtar hakan yasa Dada tambayar ta ko Bata ji abinda ta fada Mata bane, se ta juya cikin damuwa tayi yadda tace Mata, tana cikin hadawa Abba ya shigo shi da Yaya Man da Kuma Yaya Muhammad, Faisal baya gari Yana Yola inda yake karatu.
" A'a auta Ina Dada ne?"
Muhammad ya fara tambaya Dan shidai seka tunanin Dan Dada ne, in har Yana Kano to tabbas daya daga cikin abinci uku da ake ci a Rana to a gidan Dada ne nashi, tun Mamaa na damuwa har ta zuba Masa idanu, a iya zuwan sa yasan wannan aikin Dada ne Bata Bari wani ya jerawa Abba abinci,
" Tana dakinta"
Abba da Bai Kai ga zama ba yace.
" Daki Kuma? Is she fine?"
Yaya Man Dake zaune yace
" Na sameta daki Bayan tafiyar Unaisa, she seems disturbed though nayi nayi tace ba koma"
Abba ya gyada Kai yace Zuhra ta kwashe kayan abincin zuwa bedroom din Dada, lokacin tana toilet har Zuhra ta Gama jera abincin, zata fita Dada ta fito ta kalli carpet din sannan tace
" Ina nace kikai abincin"
Abba Dake shigowa yace
" Ni nace a kawo nan"
Ba tace komai ba Zuhra ta fita shi Kuma ya karaso ciki Yana fadin
" Naga yau Jan aji ake min shi ne na kawo kaina"
Ya fada Yana dariya Wanda Dole ita ma yayi lightening mood dinta, seda Suka ci abinci sannan ya dubeta yace
" Me ya faru ? Wani Abu akai bayan fita ta?"
Ta girgiza Kai alamar Babu, sede ta kasa hada idanu dashi
Yace
" In six days zamuyi shekara talatin da aure, Zainab ko da hannu kike tafiya nasan kafar Dake Miki ciwo, ki fada min me ya faru?"
Tace
" Unaisa"
Se ya Dan kalleta da mamaki yace
" Me Unaisa tayi?"
Se tace
" Baka ganin kamar In Maharazu ce ta Haifa Unaisa? Abba kamar ta baci, Abba ni nasan Unaisa tsatson Innar maharazu ce"
Se yace Mata shima hakan ya gani tun a mota, to Amma yasan Allah ke halitta kuma Bai son ace yasa ta hopes dinta high shiyasa yake bincike. Nan Dada ta fada Masa yadda sukai da Unaisa yace zaiyi bincike.
Bayan laasar na karasa gida, da sallama dauke a bakina na Shiga, gidan shiru Babu kowa a tsakar gida hakan yasa na wuce inda muke aje containers din ruwa na daura alwala, dakin mu na wuce se na same su dukkan su a can, banma lura da tsohuwar Dake zaune gefen katifa ba, na gaida Anna sannan na amsa sannu da zuwan da suke min na zura hijab na tada sallah. Cikin sallar naji bakuwar murya na fadin
" Hassana da ace kinsan mahaifiyar ki da kin tabbatar da kamar da Unaisa ke Yi da ita. Allah me iko ai kamar tasu ta baci"
Anna tace
" Allah sarki! Ai tun tana karama idan Inna Zulai tazo Haka take fada, tace Kama suke sosae"
Matar tace
" Ai kamar ta baci hassanah, ko ku Baku Kama da ita kamar yadda take Kama da ita"
Lokacin na idar da sallah, na juyo na gaishe ta, fuskarta a sake ta amsa tana cemin nazo, Babu musu na karasa gurin ta, ta rike hannuna tana kallon Anna tace
" Duk sun girma mashaaa Allah!"
Anna tayi murmushi sannan tace min mamar babanmu ce, na tsura Mata idanu se Kuma Naga hakane fa ga Kamar su sosae ta bayyana. Na Kara gaishe da ita ban masan wazan tambaye ta ba. Se tace
" Hassana Babu Wanda ya tambayi Baban a cikin su"
Anna dake duba kayan da nuna Mata an bani daga gidan su Zuhra tace
"Eh saboda dama Basu Saba dashi ba, shiyasa"
Se tayi shiru, ni Kuma karfin halin ta nake gani, me ya kawo ta? Bayan shekara da shekaru se yau aka gadamar waiwayar mu kenan. Na mike na fita tsakar gida na shimfida tabarma, daya Bayan daya su Badi'a suka biyo ni, muka fara Hira kamar yadda muke, se itama Anna ta fito ta zauna damu tana sauraron dukkan abinda tace. Da daddare dukka munyi Shirin kwanciyar Anna tace na barwa Baba Fiddau katifata nazo dakin ta mu kwanta. Na shirya na dauka wayata da hijab Dina na musu sallama zuwa dakin Anna, already ta kwanta Nima na kwanta gefenta, Bayan na Gama addua nace
" Anna Wai me tazo Yi?"
Ta danyi murmushi da naji sautin shi tunda duhu ya mamaye dakin tace
" Wai tazo ta ganku ne"
Nace
" Uhmmm! Kuma se yau? Kinga Anna idan Kika Basu fuska zasu ta zuwa ne, zasu manta duk abinda Suka Miki"
Tayi dariya batace Dani komai ba, Nima se ban Kara cewa komai ba na lumshe idanuna a Haka bacci ya daukeni. Washegari Babu makaranta Babu me fita se bamu tashi da wuri ba se wajen goma, ni na fara tashi na fito tsakar gida, seda na tsorata da farko, tana zaune ta zabga tagumi hannun ta rike da casbaha da ba lallai tasan me take ja ba.
" Ina kwana?"
Ta saki murmushi tace
" A'a takwara kin fito?"
Se na fahimci Nuzla take nufi, na gyada Mata Kai na wuce toilet nayi wanka sannan na shirya lokacin kowa ya tashi,kaida se mun gyara gida munyi wanka sannan zamuyi breakfast, Anna ba ta Hana ba tace muyi yadda muka Saba, muka gyara gida kowa da aikin shi, Ina jin Badi'a da Nuzla na fadin
" Kalli yadda take Hamma kamar zata cinye mutane'
Badi'a Dake wanke mopper tace
" Kinsan a kauye 6am anyi breakfast Dole ai taji Yunwa"
Na danyi gyaran murya Dan su San Ina jin su, Nuzla ta kalleni tana dariya na girgiza musu Kai alamar su daina, se Sha daya na Gama breakfast muka baje kowa Yana cin abinci, ta dubi Anna tana fadin
" Hassana Haka kuke cin abincin safe da Rana tsaka? Ina ai Banga gurin Zama ba"
Badi'a tace
" Dan Allah Baba ki zauna ya Zaki tafi"
Na saki Baki Ina kallon makirar yarinyar nan, Basu Jima da Gama gulmar baiwar Allah nan ba"
Nuzla cikin turanci tace
" Badi'a what's this? Abeg allow this old woman to leave"
Anna ta Harare su, da gaske muna Gama Breakfast ta dauki Kaya muka Taya ta se bakin titi ta samu napep sannan ta tafi, da muka dawo Anna ta cemin gashi cikin ruwan sanyi anyi maganin ta, munafurci ya kawo ta tazo taga halin da muke ciki, Kuma tazo taga a yadda muke, wani me kudin Bai Isa fada Mana Jin dadin rayuwa ba.
Bayan sati daya Shirin tafiya hadejia kawai nake, duk abinda ya kamata Anna na siya min a hankali kafin lokacin tafiyar yayi. Kudin registration shima ta aje min tun da naci pre test, saboda kada nazo tafiya a samu matsala. Har na kwanta wayata ta fara ringing nasan Zuhra ce Dan ita daya nake anticipating Kira daga gare ta. Ina dubawa Naga ita dince kuwan, na dauka ina fadin
" Zuhra"
Ta amsa muka gaisa Amma se naji yanayin excitement din dake cikin muryar ta a Koda yaushe Babu shi. Na tashi na zauna nace
" Zuhra akwai wani abun ne? Naji muryar ki kasa kasa"
Ta danyi shiru se tace
" Dama Dada ce, tunda Kika tafi to gata nan dai dukka Bata Jin Dadi"
Nace cikin rashin jin Dadi
" Subhannallah! Me ya faru?"
" Wallahi Kinga tambayar ki zanyi, Anna tana da wata Yar uwa da Bata sani ba?"
Nayi shiru Ina tunani Dan ni a yadda na sani Anna Inna Zulai ce kawai Yar uwarta Bata taba Mana zancen wasu ba, nace
" Wallahi bansani ba Zuhra, just tell me me ya faru ne?"
Ta saki ajiyar zuciya me nauyi tace
" Ita Dada Fulani ne, to Kuma irin masu yawo dinnan ne Dan ita tace bata masan asalin garin su ba, tasan tana da Yaya namiji tun suna Yara ya tafi karatu, se kanwar ta Zulai Wai, to suna yawon sukazo Jahun, kinsan Abba Dan Jahun ne. Se baban shi kakan mu kenan se ya ganta se yace ya kamawa Abba, kafin su tafi akai aure su Kuma suka Kara gaba. To Kuma Basu Kara dawowa ba, Bata San inda suke ba ko sauran Yan uwan nata ba, tunda ita bayan auren Abba zai tafi karatu England ya tafi da ita acan tayi karatu"
Se naji ai irin labarin Inna Zulai ne, ga Kuma sunan Inna Zulai ya fito, nace
" Allah sarki Dada, to yanzun me ya faru?"
Tace
" Bayan kinzo kunyi magana kin tafi tace wallahi kamar ku daya da Babar ta, Kuma kema kinyi maganar Inna Zulai ai"
Nace
" Zuhra ki cewa Dada tazo ta samu Anna suyi magana, it can't be a coincidence all this, tunda ance da kakata maman Anna nake Kama, ga Inna Zulai"
Ta saki ajiyar zuciya cikin jin Dadi tace
" Allah yasa hakanne, I can't wait duk hankalin mu a tashe yake, duk ta damu"
Nace
" Ai dole, yanzun Zan cewa Anna kawai Dada zata zo, idan sunzo se suyi maganar"