← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 78

Sashe 23

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yadda abubuwan suke tafiya yasa ban wani maida hankalina akan Al'amin ba, se bayan Dana tabbatar komai ya Zama daidai sannan na nutsu na dawo hankalina, munyi magana da Anna tace min Baffa yace taje Masaya ta sanar da Alhaji Yahai cewar zata ma Badi'a aure, ko da Bai Mana komai ba matsayin mahaifin mu to duk da Haka yana da right din yasan me yake faruwa akan mu, Kuma su din basuda ikon daura Mata aure se dangin Alhajin.

Ranar Monday da wurwuri na Gama shiryawa cikin farin uniform Dina na student nurses, a karshen hannun akwai brown layette wanda yake tabbatar da cewar ni student ce. Na feshe jikina da turarruka masu Dadi sannan na zura abaya a saman uniform din, na kawo black duty shoe Dina na saka na dauki jakata all set. Anna na tsakar gida yayinda Nuzla Dake level one a maitama sule itama ta Gama shiryawa, Badi'a na daki tana bacci se Hunainah da zamu fita tare da ita.

" Anna yau din Zaki je Masayan?"

Ta girgiza Kai tace

" Na Bari zuwa asabar se mu tafi Dake ko?"

Na danyi murmushi nace

" Allah ya kaimu, to mu zamu wuce"

Ta tashi tsaye tana Mana adduar nasara da Kuma taari tare da tunatar damu muyi addua mu Kuma kula da kanmu, hakanne a kullum se ta maimaita sede idan ba fita zamuyi ba ko Kuma bamuyi waya ba idan Ina hadejia. Ina fita wayata cikin pocket din Abaya ta ya fara ringing, nayi saurin cirowa na duba kamar zuciyata tasan shi ne, Dan Zuhra kawai ke Kirana da sassafe, to Kuma yau tasan ba tare zamu tafi ba.

" Good morning"

" Mhmm! Yau kinyi niyya kin dauka kenan?"

Na Dan harara wayar nace

" Haka ma zakace"

Yayi saurin fadin

" No! Ba Haka nake nufi ba. Ya Kika tashi? How was your night?"

Na Dan yatsina fuska nace

" Alhamdulillah! Naji kamar kana Hanya aiki zaka je?"

" Yeah! Aiki zanje nasan kema kin fita ko, Salis told me you're very punctual and I like that"

Na danyi murmushi bance komai ba,

" Ba Wai tambayar shi na dinga Yi bafa, kawai Bayan kin fita he commended you"

Nace

" Ayya!"

Se yace

" Zan shigo Kano anjima, can I see you?"

Na danyi shiru Ina ayyana to dama baa Kano yake ba Amma se nace

" Allah ya kaimu"

Se mukai sallama na rike wayar a hannuna, ba laifi Yana da dadin hira Nuzla tace

" Adda waye? Yaya Ahmad ne?"

Nayi saurin kallon ta nace

" Ahmad Kuma? Haba dai"

Tayi dariya tace

" Meye abin haba dai? Is it a crime?"

Nace

" Yeah! It's karki Kara"

Se tayi dariya har muka karaso kowa ya Kama hanyar shi. Ina zuwa nayi signing sannan na wuce can ward dinmu, baa fi minti shida ba Sega Zuhra, she looks excited nace

" What's the news? Ban Nasha"

Tace

" Doctor zai zo anjima"

Nayi murmushi nace

" Ok! Ya zaayi kenan?"

Tace

" Na fadawa Anna zamu wuce can kawai, yace Wai dama yana son zuwa kinsan tunda ta dawo Basu hadu ba"

Na gyada Kai Dan lokacin data dawo yaje wani course India shiyasa Bai ga karamar uwar tashi ba. Wajen karfe Sha biyu na Gama dressing Ina wanke hannuna naji chief dinmu tana Kirana, nayi saurin karasawa tace naje preceptor na Kirana, there and then na gane Al'amin yazo kenan, na Dan goge fuskata da face wipe din Dana dakko daga cikin jakata, na saka wayata Ina haskawa har na goge ko Ina, Babu wani datti a jiki, to ta Yaya zaayi aga datti yadda nake bautawa jikina. Balm na lakuto na shafa a lebe na, wata sister Rahma tana zuane tana ta kallona tace

" Unaisa ko dai keda Salis?"

Nayi saurin rufe fuskata nace

" Ba Haka bane ba fa"

Tayi dariya tace

" Cigaba da kwalliyar ki , Haka ake son mace"

Dole na maida balm din na fita Ina zumbura Baki, ta Yaya ma preceptor da ya kusa ya Dani, tab Allah ya kiyaye min na aure tsoho, nafi son na aura yaro muyi kuruciya tare. Rayuwa kenan, this has always been my dream Amma da na hadu da honorable se na manta abinda nake so da Wanda ba naso, a son shi kaina ne kawai ban manta ba. A kofar office na same shi Yana kallona har na karaso na gaishe shi yace na Shiga ana jirana. I felt ashamed da ban tambayi waye ba kawai na shiga. Yana zaune Yana kallon kofa wayar shi Kare a kunnen shi, sanye yake da wani men lace Blue me haske irin sararin samaniya, plain aka dinka shi Babu wani kwalliyar, Amma believe me ya Yi Masa kyau hade da Kara haskaka fatar shi da take da Dan duhu Amma ya fini haske, kanshi sanye da hula da ta kayatar da shigar tashi. Muna hada idanu ya sakar min murmushi Wanda dama a fuskar tashi yake

" Mummy na samu kina bacci shiyasa ban tashe ki ba, Kuma Amra tace kanki na ciwo shiyasa Baki fita ba"

Ya shagwabe fuska Wanda yasa na kawar da Kai saboda tsaf zai iya charming Dina da hakan

" Haba Mummy, bazan Jima ba Zan dawo Allah"

Ya Dan zaro idanu yace

" Noooo! Mummy haba dai ai Dake Zan fara fadawa."

Se Kuma yayi Mata sallama ya kashe Yana Dan dariya yace min

" My mother kinsan Wai cewa tayi Wai ko wajen budurwata nazo? Na fada Mata?"

Na kalleshi a karkace nace

" Ni budurwar ka ce?"

Yayi murmushi yace

" Hajiya Unaisa zauna Mana"

Na noke kafada nace

" Ni sauri nake, lokacin medication ya kusa"

Na fada Ina kallon wristwatch din hannuna,

" Zauna na fada Miki relationship din mu"

Na samu na zauna kujerar dake kallon shi Tate da bashi dukkan hankalina, nasan zakuyi tunanin Ina son yace Yana Sona ko? A'a bansan me yasa ba hakan Bai zo kaina ba kawai abinda nake son sani menen ya daukeni.

" You're my best friend, my Buddy"

Na danyi murmushi nace

" Da gaske?"

Yace

" Da gaske fa! Kinga tunda mu kawaye ne zamu dinga fadawa juna komai Babu boye boye. Haka ne?"

Na gyada kaina se yayi dariya tare da mikewa yace

" Bari na gudu, Mummy Kar tayi fushi"

Nima na Mike tsaye nace

" Aikuwa dai ka gaishe ta"

Ya saki murmushi Jin Dadi yace

" Mummy zata ji take care se munyi magana Friend"

Na gyada Kai na muka fito tare, na wuce ward ya wuce wajen SOPD. Ni na fara fitowa wayata a hannuna Ina kokarin dialing number Al'amin, a ganina ya kamata na ji yadda yaje gida, tana fara ringing nayi saurin katsewa Ina tuhumar kaina dalilin da zaisa na kirashi. To Amma ai ni dashi abokai ne Kuma a friend should stand for a friend. Ward dinsu zuhar naje muka taho tare se gida. Muna zuwa gidan ya kacame da aikin tarbar Yaya khalifa, Muna shiga Anna tace

" Karku sake kusa Mana hannu, ku wuce can kuje kuyi wanka Banda warin asibiti Babu abinda kike"

Aseey ta fara dariya, na Harare ta, Zuhra tace

" Ke Kuma yaushe Kika zo?"

Tace

" Naje gida Dada tace kina nan ai"

Muka wuce daki, ita ta shiga toilet din Anna no na shiga na dakin mu, kafin wani lokaci mun fito, ta shirya cikin lace me kyau me duhu kasancewar ita fara ce Amma fur Taki yadda na shafa Mata powder. Na kwallawa Anna Kira da ta amsa nace

" Anna Wai ba zata shafa ko powder ba"

" Zuhra karki barni nazo ranki zai baci, Haka Zaki je gaban shi kamar ta bargazuzu"

Me zamuyi Banda dariya, ta Bata Rai ita a Dole ta kulu seda na Mata Yar karamar kwalliyya se tayi kyau. Anna da ta shigo tace

" To ko kefa? Ai idan kana da kyau ka Kara da kwalliyya idan ba Haka ba na bashi Asiya"

Aseey ta kwalalo idanu tare da fadin

" Allah Anna Nima Ina da saurayi na fa"

Mukai dariya, Bai Jima ba yazo bayan munje min gaisa muka barsu tare muka dawo gyaran gida, ko Ina ya koma das sannan muka koma daki muka zauna anan na tarar da call din Al'amin da nayi missing, Kuma lokacin na tuna Ashe na Kira shi

" Unnie! Ina Kika jefar da wayar?"

Shi ne abinda ya fara tambaya Bayan ya dauka nace

" Kasan meye Unnie?"

Yace

" Menene?"

" Ana nufin sister in Korea"

Ya danyi dariya yace

" Har wani yaren kikeji, you really are amazing. Amma kinsan kawai short din sunanki ne"

Na gyada Kai alamar na fahimta, muka gaisa na tambaye shi Mummy yace tana lafiya sannan nace ya Bari muyi magana anjima Ina da Baki.
Chapter 23 · 0% Book details