Sashe 10
Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai fa se muka fara dariya, ta mike ta dauke tray din, Anna tayi dariya tana binmu da kallo me cikeda farin ciki da kauna, wannan matar ladan ta a gurin Allah ne shi daya, tunda Baba ya saka kafafun shi ya tafi Bai Kara waiwayar mu ba Haka muma ko da Wasa bamu sake maganar shi ba, ni ce ma lokaci zuwa lokaci nakan tuna dashi bawai Dan ya dawo ba a'a se Dan mamakin karfi Hali irin nashi da nake da Bai taba juyowa ko ba Dan Anna ba danmu Yayan shi, gaba daya rayuwar nan se a hankali se yasa nake Kara tsoron attachment a rayuwata. Se dare sannan Yaya Yusuf yazo, ya kawowa Anna scholarship din da ya samu zuwa Sudan Dan yin karatu, gaba daya muka taya shi murna anan yaci abincin dare sannan ya Kara nanata min nayi karatu da kyau Dan makarantar da zanje kora suke Babu ruwan shi.
Bayan sati daya Ina zaune Ina saka wani set din kayan sanyi na babies da aka kawo daga makwabtan mu danta ya haihu suna hada kayan barka, na Gama saka riga da wandon da hula, se shawl din da socks kawai suka rage, Badi'a na gefe tana hada hulunan da Nuzla tayi, Hunainah Kuma ta fita da Anna se Nuzla na girki. Kamar daga sama se Jin sallamar Zuhra nayi, na aje knitting pin din Ina mikewa se kuwa gata ta shigo, na saki murmushi Ina jin Dadi, ta shigo ta zauna tana fadin
" Wallahi wayarki batada amfani, kinsan irin Kiran da na dinga Yi Miki kuwa?"
Na dubi Badi'a Dake gaisar da Zuhra nace
" Badi'a Ina wayata?"
Ta mike nace da Zuhra
" Ayya ai bansani ba tun dazun ta dauka sannu da zuwa, sannu Ina Dada da Abba?"
Ta gyara zamanta tace
" Duk suna lafiya suna gaishe ki, Ina Anna? Ko Dan tace min taje unguwa ko?"
Na gyada Mata Kai, Sega Nuzla tazo suka gaisa ta kawo Mata ruwa sannan ta Bata hakuri Akan an kusa Gama abinci, murmushi kawai tayi muka cigaba da Hira, tace
" Wai duk sakar nan ke kikayi? Gaskiya you got talent Babu abinda na iya se surutu"
Aikuwa na kwashe da dariya jin tayi admitting cewar ita din me zance ce, ta Ciro wayatta tace Wai albishir tazo tayi min, na aje pin din na karba dogon list ne na Wanda sukai nasarar cin entrance exam din da mukai, na saki hamdala ganin sunanta sannan na tafi lalubar nawa se kuwa gashi, na rungume ta Ina fadin
" Alhamdulillah Zuhra we made it!"
Ta gyada min Kai tana dariya tace
" Kinga da Abba yace na Bari kawai naje Nile University nayi BSC acan saboda can Aseey zataje"
Se naji banji dadi ba, na aje wayar Ina sauraren ta
" Amma nace ni fa can hadejia zanje gaskiya, na riga na hadu dake"
Se nayi murmushi nace
" To me Abba yace?"
Ta yaye veil dinta ta aje can gefe tace
" Ya yadda of course, Aseey zata wuce wani satin ita"
Na gyada Kai dukda bansan wacece Aseey din ba, ban Kuma tambaya ba. Nan muka ta Hira har Ina mamakin kaina sannan muka ci abinci, se yamma Anna ta dawo da dealolin gwanjo da aka Aiko Mata, me napep din ya shigo dasu, ta zauna a gajiye Zuhra ta kawo Mata ruwa tana Mata sannu da zuwa, seda ta nutsu sannan ta fada Mata cewar ai munyi making exams dinmu, ba karamin Dadi taji ba. Tana zaune aka bude dealer farko wadda duk blazers ne, skirts da Kuma tops, muka Taya Anna ta shirya su se yamma sannan aka kirata akan anzo daukar ta, ta dubeni Bayan ta tashi tace
" Ina jiran ki kizo kema"
Na dubi Anna da tayi murmushi tace
" Zata zo Inshallah"
Da idanu Anna ta nuna min ledar ta ware Kaya ta min alamar na bita dashi, na dauka muka fito muka tarar da Yaya Saif ne yazo tafiya da ita, muka gaisa dashi sannan mukai waving juna bayan na wulla Mata ledar a backseat nace inji Anna, nayi ta dariyar hararar da take min na Zan Kama ki dinnan. Seda taje gida taga kayan sannan ta kirani tana ta godiya ta Kira Anna na.
Rana daya akai Mana fixing ranar da zamuje interview, tun dare kamar yadda na Saba idan zanyi tafiya na hada kayana har credentials Dina, washegari da wurwuri nayi wanka na shirya cikin Ash din atamfa me design din pink a jiki, dinkin skirt da riga, ban daura dankwalin ba se na saka hula Dan hijab nake son sakawa, awara na.soya na hada sauce na Kuma juye cikin flask sannan na dawo Kan fuskata, nayi scrubbing na wanke ta tas se glowing take sannan na shafa Mai da powder, nasa kwalli na gyara gashin kaina da Kuma na gira, na duba madubi Naga I'm good to go! Ina saka hijabi na Se naji sallamar ta, ta shigo sanye da bakar Abaya me wasu sparkling stones, ta rufe kanta da veil din,
"Bari na gaida Anna nazo mu tafi"
Anna ta fito.da sauran yaran Dake midterm break, Suka gaisa sannan muka wuce, wannan karon driver ne muka gaisa dashi sannan muka dauki Hanyar hadejia. Muna zuwa ana farawa, se wajen Sha biyu aka Kira sunana, na gyara zaman hijab dina, na dauka file case Dina na shiga, kowannen su a zaune, wasu sun manyanta yayinda wasu suke a young age din su, na gaishe su aka min tayin kujera na zauna, na Mika musu takaddu na kamar yadda suka bukata, wasu na going through yayinda wasu Kuma ke jefo min tambaya. Ina ta amsawa se a karshe suka tattaro min takaddu na Suka ce naje, Haka na juya da karfin gwiwa ta na fito bayan na musu godiya. Se bayan azahar Zuhra ta shiga Tana fitowa mukai sallah muka tafi mota muka ci abinci sannan muka dakko Hanyar dawowa gida. Duk yadda muka kwaso gajiya Bai hanata shigowa ta gaida Anna ba, dama tun a hanya take min korafin ni naki zuwa na gaida Dada, a gidan su kullum se anyi Mata dariyar har yanzun ban zo ba. Na danyi dariya nace
" Zan zo fa"
Tace
" Se yaushe?"
Na danyi shiru kafin nace
" Zan kiraki idan zanzo"
Se ta gayda Kai ta fara rubuta min address din cikin note din wayata, tun a hanyan take bani labarin su
" Mu Yan Jahun ne, Abba engineer ne ita Kuma Dada accounting tayi, tana aiki itama, Yaya Man shi ne babba se Yaya khulthum ita tayi aure da wani cousin din mu, se Yaya Faisal se ni"
Nace
" Wow auta! To wannan da kuke video call dazun fa?"
Tace
" Oh! Yaya Ahmad he's a cousin. Baban shi yayan Abba ne Abiey. He's my favorite cousin"
" Dada fa? Ita Yar Ina ce somehow kina min Kama da Fulani"
Tayi dariya tace
" Abin mamaki Dada bata San asalin garin su ba, kinsan kakkani na are very funny, Wai kawai sunzo wucewa Suka yada zango garin su Abba suka bada auren ta, guess what Basu Kara dawowa ba"
Na bude idanuna see a similar story to that of Anna, nayi dariya Nima nace
" Haka family Anna sukai, ba fulanin daji bane? Ai su dai se su"
Muka hadu muka saka dangin Anna da dangin Dada da duk sauran fulani a tray muka tsuye su, not minding mu dinma fulanin ne, nakan ayyana dama Zan iya Dana fada Mata namu labarin Amma bazan iya ba, na cika zurfin ciki da rashin yarda.
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/13, 2:49 PM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕
*J*
Ayshatuuu
*Last free page*
Ban cika alkawarin da na daukawa Zuhra ba na cewar zanje gidan su, ni din bame yawan son fita bace balle Kuma har naje gidan su Zuhra da ko skin dinta ka kalla ba se an fada maka cewar ita din Yar masu kudi bace, kana kallon ta kasan hakan, to ni bana son na fiye shishigge mata sboda inada gudun wulakanci. Tun tana korafi har ta fahimci bazan je bane se kawai ta kyaleni, Amma Kuma Bata Kara zuwa gidan mu ba Haka Kuma ta daina Kirana Wanda hakan ba karamin abin mamaki bane, hakan sabon Hali ne data zo dashi, hatta Hunainah seda tayi jigiyar ta.
Da yammaci Ina sanye da skirt da top na gwanjo, kaina a barbaje Ina tajewa Ina ta yatsina fuska saboda yadda ya Kara tauri, Dan tun asali Kan nawa tauri ne dashi, seda na Gama Ina jin kamar nayi ihu saboda dukan Kan ya daure hatta scalp din ciwon tazar yake. Na daura Leda a hannuna na fara diban home made hair mayonnaise, dukda warin man shanun dake bugata Bai dameni ba as long as kaina zaiyi laushi an wuce wurin, na Gama sawa tas hannuna har ya kage saboda yawan gashin, Anna ta fito lokacin Ina zura bakar Leda a Kan Dan ya Dan narke. Ta samu kujera ta zauna tana fadin
" Har kin gama? Ai da kin sakawa Hunainah Dan itama irin gashin ki ne da ita"
Na kalle ta tana zaune acan gefe tana Wasa nace
" Seda nace tazo na saka Mata yarinyar nan ta gudu"
Anna ta girgiza Kai kawai tana murmushi tace
" Wai kin fasa zuwa wajen Zuhra dinne?"
Na Dan yamutsa fuska nace
" Ni fa kawai bana son zuwa,kada aga kamar kwadayi ne"
Anna ta gyada kanta tace
" Kinyi magana kema, Amma ya kamata kije say daya daga nan shi kenan. Zuhra ai mutum ce"