← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 78

Sashe 63

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka amsa Amin ya Ciro wayar shi ya Kira Nanah se gata ta fito dauke da yarinya a hannun ta, yace

" Amour ga kawa nayi Miki"

Kusan saanni muke da ita, muka gaisa sannan muka shiga ciki yayunta masu kirki nayi barka mukai exchanging contact da ita na fito, se Hira suke, Yana ganina yace

" Har kin fito?"

Nace

" Eh kazo ka tafi kada dare yayi"

Yayi ma Abba Prof sallama sannan muka tafi Yana ta bani labarin shi, da yadda sukai aure salin alin ba wani problem. Nace

" Shi yanzun daga zuwa karban Kaya shi ne ya aureta"

Yace

" To laifi yayi?"

Na girgiza Kai Ina dariya a hankali. Mukaje Tasha na sama Masa gaba na biya kudin sannan nace ya fito ya shiga, na aje Masa ledar nace

" Thank you for coming, Allah ya kiyaye Hanya I love you"

Yayi ta murmushi har na Gama magana sannan mukai sallama na koma gida Ina jin kamar Ina yawo saman gajimare!

UNAISA is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

[6/24, 1:18 PM] Hauwa Galadima: *B³*

Yadda kwanakinnan ke gudu shi Kan shi abin tsoro ne, da zarar ance Monday tayi inshallah zakiga har Friday tazo, kana zaune Babu abinda ka tsinana. To Haka rayuwar take yanzun, a bangaren mu lokaci ya tafi sosae, a shirye shirye kullum Yi Mike Yi, kowa kokari yake wajen ganin anyi yadda ya kamata. Kamar yadda ala'ada take an kawo lefe na, high class one Dan Baku tunanin cewa simple zaayi? Duba da Wanda Zan aura da Kuma irin son da yake min. Anty Salma da kanta ta kawo daga can inda take zaune, Yan uwan shi Suka gaggani sannan aka saka Rana aka kawo gidan Abba, Anna Bata je ba tana gida Amma ta fadawa Baba Fiddau ta turo wasu daga cikin Yan uwan mu na Masaya. Yadda ake zuzuta lefen kadai ya Isa. Ko da na dawo naje na gani abin baa cewa komai sede fatan ayi Zama me daurewa Wanda baa samu anyi ba, Kai Allah sarki Abiey, ta Ina Zan taba kawowa zai rasu? Ta Ina Zan taba tunanin hakan zata faru? Ai abune da yazo min a bazata har na mutu bana tunanin Zan daina jin dacin mutuwar shi. Bayan nan aka je ganin gida Wanda ke cikin babban Birnin jigawa wato Dutse, shi Kan shi gidan komai taste Dina ne, Kai hatta tiles ni na zaba, idan ya turo wani abin zai saka idan nayi complain

" Abiey abin Yana komawa extravagance fa, why are you doing this?"

Se yayi dariya yace

" Beautiful! Inada kudi, dama ce kawai nake amfani da ita, komai so nake ya Zama Wanda kike so saboda akwai ranar da zakiji Baki son ganin fuskata, akwai ranar da Zan Bata Miki Haka aure yake, Amma Ina son idan kkin kalla gidan kiyi farin ciki"

Shi dai maganar shi daya biyu, to ta uku farin ciki ce, Anna tayi namijin kokari Dan kuwa kayan da tayi min ko Yar wani hamshakin se Haka, nayi ta Mata complain nace

" Anna akwai abubuwa a gaban ki, ya Zaki dinga siyan gado na over million, su Kuma su Nuzla fa?"

Tayi murmushi tace

" Unaisa kaf din ki Babu Wanda yasha wahalar da Kika Sha, Dole Zan Baki abinda nake dashi"

Abiey shi yayi furnishing sama, Anna tayi na kasa, Abba yayi min gara, Dada ta saya min dukkan abinda ke kitchen dina, Zuhra da Yaya Man da Yaya Faisal dasu Yaya khalifa da yayan Inna Zulai suka hada kudi me tsoka Suka bawa Anna, komai dai na biki ya kammalla, Nima nayi playing role don duk abubuwan kawata gida na decorations da kaina na siya, tunda ai inada kudi Nima. Ina ta zuwa gyaran jiki, ga Wanda nakeyi Kuma shiyasa nayi wani irin kyau kamar mudubi saboda glowing, kunsan dama dai can ni me gyara ce balle yanzun dalili yazo ai Babu Zama.

Ana saura sati biyu na Gama karbo duk dinkunan da zanyi amfani dashi a biki, se Muka dauki wasu na cikin lefe muka Kai dinki, Bayan mun zauna tailor din ya dakko littafi Yana Jin styles din da zaayi min, Zuhra ta ware wasu ta nuna Masa hade da fadin

" Kana ji tailor, kaga Wanda na ware dinki zaka Mata na amare, Wanda idan ya kalla ko yawu bazai iya hadiya ba"

Tailor ya fara dariya yace an Gama, ni tsabar mamaki se na kasa magana seda muka fito muka shiga mota na daka Mata duka nace

" Ke Abiey baban ki ne, shi kike yiwa Haka"

Ta kalleni tace

" I'm a good daughter, Ina son babana yayi farin ciki, by the way yanzun shi abokina ne tunda zai aura kawata"

Na bude Baki kamar sokuwa Ina kallon ta nace

" Zaki maimaita a gaban shi"

Tayi Rolling idanun ta zata tada mota taga Ina Kiran shi, tayi saurin warce wayar Amma har ya dauka se kawai ta Kara a kunnen ta tana harara ta, ni Kuma Ina dariyar mugunta

" Abiey Ina wuni! Zuhra ce"

Daga dayan bangaren yace

" Daughter ya family? Kuna tare kenan?"

Tace

" Eh Abiey, ya shirye shirye Allah ya Sanya alkhairi"

Yace

" Amin Amin nagode, na Mata maganar kudin kunshi da makeup ko? Har yanzun Bata ce komai ba"

Zuhra ta Harare ni Nima nayi glaring din ta tareda maida kaina kallon window tace

" Zan Yi calculating, Zan Kira ka Inshaaa Allah"

Daga Haka sukai sallama, ta Miko min wayata, na karba kamar wata jelly Haka na narke d a yace

" Hello beautiful?"

" King dina, Ina wuni?"

Ya amsa ni sannan ya tambayeni inda muka je, nace

" Na Kai dinki, kasan me Zuhra tace"

Ta daka min duka na saki Yar karamar Kara nace

" Abiey ka ganta ko tana duka na, Kuma Allah da zafi"

Yace

" A'a Kar ta Kara, sorry kinji rabu da ita"

Daga nan mukai maganar zuwa screening, dukda munsan status dinmu Amma ya kamata muyi presenting mutane su gani su San we're compatible kafin ayi auren. Bayan mun koma gida da kwana biyu muka shirya bisa umarnin Abba naje muyi screening, na shirya cikin onion Abaya, wadda akai embroidery da touches din Maroon. Nayi kayi sosae na saka glasses Dina ko da Zan fita Nuzla tace na tsaya tayi min hoto tayi min sannan ta rakoni kofar gida inda yake jirana mu tafi, Yana cikin mota Bai fito ba, driver din shi ya bude min kofar gefen shi na shiga, anan idanun mu sukai locking na juna, it's been a while actually, min Jima bamu hadu ba, na zauna Ina murmushi nace

" Ina wuni?"

Yace

" Kinyi kyau you look beautiful as always"

Na Dan dago Ina murmushi shima Murmushin ne a fuskar shi, yayi disguising Kan shi cikin kananan Kaya, yayi kyau sosae shima, nacs

" You look good kaima"

Yayi dariya se Muka fara deep conversation,abubuwa yake fada min Wanda su ne expectations dinsa akaina, abubuwan da yake so da Wanda baya so, yadda zamu tafiyar da rayuwar mu cikin aminci, Ina ta sauraren shi har ya Gama nace

" I'll not let you down King, Zan zame maka sanyin idaniyar ka, na zame maka farin cikin rayuwar ka'

Yayi dariya yace

" Ai ke din sanyin idaniya ta ce, ko Dan I'll sure that I truly love you"

Asibitin abokin shi ne Dake running nashi private business, munyi test kalakala to show that dukkan mu mun lafiya, aka Bari akam wasu se washegari zasu fito muka dawo gida, Amma kafin mu dawo seda yasa mukai yawo sosae a Kano kafin ya maida ni gida. Bayan na shigo gida Sega message din shi

_Baby I love your scent and I love you!_

Har wani blushing nayi, nasan kamshi nake Babu Wasa, saboda yadda ake murje ni da turare.

Ranar Friday zaa daura aure, tun monday muka tattara zuwa gidan Abba, dukda Anna ta so tayi bikin anan Amma Abba yace auren Yar shi ne Dan Haka acan zaayi. Tuesday naje ni da su Zuhra dasu Nuzla kunshi, se dare muka dawo, na gaji ga Yunwa da nake ji Kamar naci Babu, Ina shigowa Dada tace naje ayimin turare, banyi musu ba na wuce sama na puffing inhaler ta saboda hayaki na saka mask na wuce inda ake yimin. Aka Yi sannan na dawo na karba tea nasha, se bacci. Washegari Wednesday shi ne na hada the only Ladies gathering tun Rana nake gudawa Amma ba Wanda na fadawa, na cigaba da harkata, time ya kusa akai dolling fuskata beautifully, Dake abin Mata ne kawai se nasa wata flowing gown me kyau, aka gyara min gashi na aka nada min turban, ya Allah karku so kuga yadda nayi kyau. Bayan na zauna Ina kallon cousins Dina su A'isha, kawayena musamman na hadejia da mukai training tare, se kalilan da mukai secondary Suma Nuzla ta kwakulo su only God knows how? Se Kuma yam comments section da yawan su, wasu Basu samu zuwa ba, , Nayi farin ciki a wañnan ranar, na Kuma yadda da akace komai timing ne, when the right time comes it occurs naturally! Bayan mun Gama Muna ta pictures da mutane se ga Hunainah ta kawo min wayata, na duba Naga alert ne guda uku, na farko daga dukkan Yan comment section dinmu be, suka hada min gudunmawar shiga gidan Abiey, na biyu na Ahmad ne, na uku Kuma Aseey! Na rike wayar da kyau Ina Jin idanuna sun ciko da kwalla, na karanta message din Aseey!

_Ina fata kina cikin farin ciki kamar yadda ya kamata, ga sako nan Babu yawa. Sannan kiyi hakuri abinda ya faru na fahimci komai mukkadari ne.._

Na Dan dafe kaina Ina jin wani irin yanayi a tare dani, what happened da ya saka su sakkowa Haka? Se na tuna jiya munyi magana da Abiey nake ce Masa

" Abiey Dan Allah ka daidaita da duk Wanda kuka Dan samu rift tsakanin ku saboda ni, kaga rayuwar nan is short kada mu mutu azo ana Dana sani"
Chapter 63 · 0% Book details