Sashe 1
Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Documented by H.M.G
🧕UNAISA🧕
*A*
✍️Ayshatuuu
Na sauke wayar daga kunnena tareda sakin Murmushin jin dadi, bayan shekaru da na dauka Ina jiran wannan lokacin se gashi yazo, komai lokaci ne sede jiran se me karfin Imani. Na kalla gidan da komai na ciki Wanda nawa ne, na Kara kallon hoto Na sanye da Ash din Abaya ta idon duniya, fuskata dauke da Murmushin da ko kana bacin Rai ka kalla se kayi murmushi, Yana tsaye a bayana sanye da dakakiyyar shadda Ash sede nashi Ash din yafi nawa duhu, yayi kyau karshe Yana murmushi, na saki ajiyar zuciya Ina hamdalan cikar buri. Na aje wayar Jin ana kwankwasa kofa, cikin sauri na Nemo veil Dina dake ninke akan cushion gefe Dani na lulluba sannan na nufi kofa bayan na zura slippers a kafata, dama na aje ne saboda ko ta kwana. Seda na leka Amma banga ko waye ke knocking ba kawai se na bude, a take wata Mata da Kuma karamin yaron da Bai wuce shekara biyar ba Suka bayyana. Fuskar ta dauke da murmushi, matar ta girme ni sosae nesa ba kusa ba, kana kallonta kasan ta manyanta Kuma Yar gayu ce ta gani ta fada, nikam a rayuwata Ina son Yan gayu, take naji ta burgeni, ni din Yar gayu ce ta bugawa a jarida, ko lokacin da bamu da komai bamu da gata bamu da Mai taimako a hakan idan ka kalleni ba zaka taba kawowa a cikin wahala nake ba. I always mind how I look. Na Bata guri ta shigo tana fadin
" Amarya Bata laifi ko ta kashe Dan masu gida!"
Nayi murmushi tareda ayyana kada dai na kashe din. na karaso ciki na Mata tayi ta zauna tana fadin
" Ammar come and sit, baka gaida Anty ba"
Yaron ya zauna Nima na zauna Ina murmushi nace
" Zo nan boy"
Ya make kafada tayi dariya, na gaida ta ta amsa da faraar da tunda na bude take a fuskar ta, na Mike na shiga kitchen na dakko ruwa da juice, se su alkaki a karamin plate, na jera Kan tray sannan na kawo musu. Ta dubeni tace
"A'a harda wahala! Nagode sosae"
Nayi murmushi anxiously Ina jiran tayi min bayani
" Sunana A'isha, ni neighbor din ki ce ta baya, megidan ki yayi ma megidana maganar zuwan ki, shi ne na lallabo mu gaisa"
Na Kara fadada murmushi na ina shafa Kan Ammar da ya dawo gefena Yana Wasa da throw pillows din da na Gama jerawa, nace
" Naji dadi sosae Anty, sunana Unaisa. Nagode da ziyarar ki"
Tayi murmushi jin nace Mata ta ci abinda na kawo Mata, karshe tayi min bayanin yaranta uku bayan Ammar daya Tana karatu a Alqalam katsina, me bi Mata Yana UAE Yana karatu, se me bi Masa tana secondary ita anan cikin anguwar mu take yi.
" Amma Anty boarding Kuma? Na zata nan Bayan mu makarantar take"
Tayi murmushi tace
" Ai dukka boarding sukeyi, Kinga Ammar ma se yayi"
Nace
" Allah ya kaimu har na fara jin tausayin shi"
Kafin ta bani amsa se wayata dake Kan side table ta fara ringing, na saka hannu na dakko, jikin screen din kamar yadda nayi saving King, shi ya bayyana, saboda a duniyata shi din sarki ne, shi ke mulkin zuciyata. Na saki murmushi jin tace min
" Daga Kiran ki Mana"
Na Kara a kunne na Amma maimakon naji muryar shi se naji akasin hakan, naji wata muryar daban. A take yanayin fuskata ya canja nace
" Ina me wayan? Me ya same shi?"
" Hajiya idan Zaki iya zuwa kizo nan general hospital yayi accident ne"
Shi ne amsar, amsar data gigita ni, Bai jira me zance ba ya kashe wayar, already Anty Aisha ta iso inda nake saboda yadda hannuna ke rawa, kirjina Yana sama da kasa alamar Neman iska nake, ta riko hannuna tana fadin
" Me ya faru ? Me ya sameshi?"
Na dunkule hannuna Ina panting sosae, nace
" Anty shi ne Yana general Wai yayi accident"
Ta saki salati ta Mika min veil Dina tare da rike min hannuna Amma Ina tashi numfashi na ya fara sarkewa Ina Jan shi da kyar, nasan definitely I'm having an attack. Innanlillahi! Hakan da ta gani ya Kara rikitar da ita, inhaler ta na dakko Dake aje inda na dakko wayar Dan dama tun safe nake jin alamar attack din, shiyasa na kawo ta na ajiye. Nayi puffing inhaler na samu ya Dan lafa, zuwa lokacin fuskata tayi kacakaca da hawaye, hannayena Banda gumi Babu abinda suke, ita ta kulle gidan sannan ta zaunar Dani ta dakko mukulin mkta, gani nayi ta Dade Bata dawo ba, hakan yasa na Mike na fara tafiya, ban masan Ina nake wulla kafata ba, kawai dai Fata daya da nakeyi na tsinci kaina a emergency unit na general.
" Anty kina sauri"
Naji muryar Ammar Yana fada min se lokacin na gane Ashe hannuna na cikin nashi, nayi nisa naji an tsaya da mota a gefena, Anty Aisha ce ta fito ta saka ni gefen ta sannan taja motar tana fada min na dinga maimaita " Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!" Haka nata maimaitawa har muka Isa asibitin. Ya Rabbu! Ban taba ganin tafiya me tsawo irin wannan ba, ban taba ganin kafata na rawa ba se wannan ranar, cikin mintina kasa da Sha biyar na gigice na fita a hayyacina, kamar ba amaryar da tayi kwanaki uku gidan miji ba. Dukka na canja a lokaci kankani. Tana parking muka fito na nufi kofar shiga unit din gabana Banda faduwa Babu abinda yakeyi, zuciyata kamar zata fito ta kirjina Haka nake ji. Nayi shiru ina kallon yadda ake ta zirga zirga,mutane nata Kai kawo, marasa lafiya wasu akan bench sunata hankoran ciwo, ga nurses na ta Kai kawon ganin sun kula dasu. Na tsaya rooted to the spot Ina jin maganganun sun danyi nesa dani.
" Dan Allah accident din da aka kawo dazunnan? Ko zamu iya ganin shi?"
Anty A'isha ta tari wani Male nurse dake zaune a station Yana clerking patient. Ya dubi wani officer Dake cike Abu cikin log book yace
" Officer inaga familyn victim din sun zo"
Nayi saurin kallon su nace
" Yana Ina? How's he? Tell me he's ok please"
Na fada muryata na rawa Ina hade hannayena waje guda alamar roko, hawaye wani na bin wani, hannuna Anty Aisha ta Kama muka bi bayan su zuwa cikin casuality din, tundaga yadda ake Kai kawo naji kafata ta sage, I'm part of the family nasan menene a janyo sunction machine da oxygen. He's in critical condition kenan! Kamar zombie Haka na cigaba da daga kafafuna har muka Shiga ciki, Yana kwance Kan couch din ciki, hannun shi infusion na shiga ta cikin cannular, hancin shi sanye da oxygen, Haka Kuma ana sunctioning din shi. Wani irin jiri naji Yana Neman kwashe ni ya yar a kasa, gaba daya ya canja kammanni, farar shaddar jikin shi ta jike da jini, Wanda ya tabbatar min yayi bleeding sosae, kafar shi anyi packing tare da daure ta Amma still jini na ratsowa ta bandage, Haka Kuma fuskar shi ta bubbugu, na karasa Ina jin wani mummunan tashin hankali da bazai misaltu ba Yana mamaye ni. Ya ilahil alamin! Na karasa gurin hawaye wani na bin wani na Kama hannun shi se Naga Ashe jini ake Kara Masa banma lura ba, na saki kuka Ina fadin
" Ya Allah! What happened to you"
In charge din ya fara min magana cikin lallashi har ya samu na yadda na zauna Amma zuciyata Allah kadai yasan irin abinda ke ciki, Anty Aisha na ta tausa ta tare da fada min nayi Masa addua. Hope kowa ke bani akan zai tashi, why se sunyi min karya, zuciyata ta karye, bana tunanin he's going to make it, Police din yazo ya bani wayar shi da wallet dinsa da Kuma wristwatch dinsa, na kalla wristwatch din ni na siya Masa kyauta wani zuwa da yayi gurina, shi ya saka ranar daurin auren mu! Ya Allah ka tashi kafadun shi, kasa ya Mike kada na rasa shi! Shi ne abinda nake maimaitawa cikin kaina. Rike wayar shi ya tuna min Yana da wani family Bayan ni, Kuma hakkin su ne Susan meke damun shi. Hakan yasa na cire lock din wayar, Wanda kawai swiping ne. Na fara lalubo number dinta " First Lady" Haka yayi saving a wayar bugu daya ta dauka tana fadin
"Ango kasha kamshi!"
Na ayyana a raina Ai Jin muryar ta se hawaye ya kubce min na fara shehsheka, Jin Haka se hankalin ta ya tashi ta fara tambayar wacece? Lafiya? Amma na kasa Bata amsa seda Anty Aisha ta karba ta Mata bayani Ina jiyo salatin ta tana fadin Anty Aisha ta fada Mata gaskiya idan ya rasu! Fadar hakan yasa na dago kaina na kalleshi, se kawai Naga ana zare masa nasal prongs din hancin shi, na dubi kirjin shi yayi flat, ga oximeter da aka saka ta tafi flat Babu alamar pulsation a jikin, se Kara take alamar Babu pulse ba oxygen saturation, Wani yawu me dacin gaske ya gauraye min bakina, na Mike Ina ganin idanuna suna rufewa da budewa spontaneously na karasa gurin. Naji ance
" Time of death 4:05pm!"
" Ya rabbul alamin"