Sashe 88
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce, “To me kuke shirya mana ne don ku ne yammata. Mun gayyato bakin kunya da yawa daga MERITIME da Florida, ya dace ku tsara activities masu kayatarwa? Ta kyabe baki ta mike tana cewa oh-oh, wannan ba da ni ba, tambayi wannan masu auren soyayyar, ni da angon ke gudu na kar in cinye shi? Ai ni auren hakuri zanyi ba auren so ba.�
Washegari aka yi kamunsu ita da Hunainah a Makarfi cikin dakin Goggo Jummai. Hidayah na asibiti likita yi bata bed-rest domin girman cikin ta abin tsoro ma ya koma, sannan ta shiga matakin karshe. Duka sun damu da condition din ta suna kuma tsananta addua kan Allah ya sauke ta lafiya.
Washegari Jumaa bayan sallar Jumaa Daddy, Dr. Argungu da tsohon Ambasada Bashir Sambo suka daddaura auren yayayan su a babban masallacin Abuja a kan sadaki naira dubu goma-goma kacal domin neman albarka inda aka zarce da walima a fadar shugaban kasa. Ta koina abokan arzuka ciki da waje sun sake barkowa ta kowanne bangare domin nunawa wadannan mazan jiya na kwarai da suka bada gudunmuwa ta hakika a rayuwar su domin cigaban kasarmu Nigeria.
To Faisal bai zo ba sai daren ranar da shi da Taju. Duk wasu abubuwa daya dace a ce shi yake yi Najib ke gabatar da su. Daddy da Hajiya sun hadawa Intisar lefe na gani a bada labari da Hidayah bata samu rabin rabin sa ba. Manyan sarkokin white-gold da duwatsu masu daraja da Hajiya ta dankara mata a kit kadai abin tsoro ne, cewa take in bata yiwa Intisar ba a yanzu wa zatayimawa?
Shi kuwa Najib mota ce sabuwa dal a cikin tamfol ya danka mata kirar kia 407 haka sauran samarin Brigedier kowa da irin gudummuwarshi mai gigitarwa, shi kuwa auta Khalil dirkekiyar teddy ya danka mata yace akan kwantar da wannan teddin, kika zama mai gilashi. Sai da tayi kuka da wasu irin hawaye masu zafi amma a yau, zafin farin- ciki ne.
Dr. Hajjo kuwa gudunmuwarta shine ta dage wurin gyara yayanta ta yadda zasu zamo ababen so ga mazajen su (ina ruwan yar Maiduguri). Duk wasu activities da Hunainah da Ehsan suka tsara da ita, ta soke kanta, tace walimar da su Daddy su kai ta wadaceta, albarka kawai take nema cikin rayuwar auren ta.
Su kansu sai jikinsu yayi sanyi suka rage wasu abubuwan da basu zama dole ba. Ko kuda bata gayyato ba banda Raadhah, mutuniyar Jerusalaam (Israel) kawarta ta (Kingston College), uwar yaya biyu a yanzun kuma likita a asibitin (Doctoor Sulyman Fakeeh) dake Jeddah.
Ranar asabar da daddare Daddy ya tara su ya yi masu fada sosai da nasihu masu sanya tsoron Allah. Ya dubi Intisar idonshi cike da kwallah, don ji yake kamar daga ranar ba zai kara ganinta ba, kai kace ba Faisal ya aurawa ita ba. Ya ce,
“Biyayyar nan da kike yi mun, ban taba cewa eh, kin ce aah ba, a yau na roke ki, ki yiwa mijin ki ninkin wadda kike mini. Ina kara cewa Allah yayi miki albarka Saratu. Duk wasu burirrika na a rayuwa a yau sun cika. Saura in ga yayan ki na gudu cikin gidannan wanda na san da kyar ne, domin mu mazan jiya ne ba na yau ba, shekarun sun tura sosai.
Ta kwaye laffayar da aka rufe mata ido da shi, idanunta jage-jage da hawaye, tasa hannun ta daya da ya sha adon kunshi ta toshe mishi baki, cikin muryar kuka, ta ce,
“Insha-Allahu Daddy har jikokina zaka gani ba yayana ba.�
Ta juya da gudu ta rungume Mamar ta, tace,
“Mamar mu yanzu daga yau shikenen na daina ganin ki a karo na biyu? Ta cigaba da wani irin kuka mai karya zuciya, ta ce,
“Mamar mu idan na taba bata muku, tun daga ranar da kuka tsinto ni, har zuwa yau da kuka aurar da ni a hannu nagari, na rokeku ku yafe mini kuyi min aikin gafara. Bani da bakin da zan gode muku sai dai in biku da fatar alkhairi da kyakkyawar addua har zuwa ranar da na daina numfashi. Kun shiga wahalhalun rayuwa iri-iri da bakin ciki kala-kala a saboda ni. Na rasa ku ko wadanne irin mutane ne masu karimci da dimbin alkhairi. Har yau, har gobe har kuma jibi, ban ga mutane masu kyautayi da kyakkyawar zuciya irin Daddy da Mama na ba�
Duk kokarin da Aunty Saratu ke yi kada Intisar taga hawayenta ta kara rikicewa sai da hawayen suka zubo a kafar Saratun. Ita kadai tasan me take ji, ita kadai tasan irin kuncin da take ji na rabuwa da Babyn ta. Rabuwa bata zuwa makaranta a dawo karshen shek`ara ba, rabuwa bata a je Kano a dawo bayan sati daya ba, rabuwa bata tana Makarfi tana Abuja ba, aah, rabuwa ta har abada sai dai azo da yawo. In banda aure yakin mata wa ya isa yayi masu wannan yankan kaunar?
A yau ma Hajiya Nafi matsowa tayi tana kara neman gafarar Intisar, tana kuka a gaban Daddy da Mamarta, don gani take har yau da sauran tabonta a zuciyar yarinyar.
Bata sani ba, ita wata irin halittar Ubangiji ce (ba daya take da sauran mutane ba). Idan tace eh, bata taba dawowa tace aah! Bata taba yin abu da zuciya biyu; a kullum kalamanta na nufin abinda take nufi ne.
Gidan da Daddy ya dankarawa Faisal a nan Maitama ne kusa da gidan Najib amma yace sai dai in ita zasu ajiye a nan, shi kam ba zai baro flat din shi dake cikin NNPC Krts. ba dake Lagos, akan wani auren da ba son shi ake ba.
Hakan dai suke ta biye mishi suna lallabashi yadda yake so. lntisar na kara tausar zuciyar ta da danne bacin ranta. Washegari Ihsan da Rehab suka koma Miami inda zata karasa karatunta tsayin shekara guda, sannan su dawo su jagoranci MERITIME. Hunainah kuma an kai ta Katsina (family house) na su Hashim a unguwar Shaiskawa kamin su kare hutun su.
Dr. Hajjo da Aunty Saratu sun kulle Intisar a daki suna ta kus-kus din su, Hajiya Hadiza na kofar falo tana latsa waya amma kunnuwan ta na kansu, tayi dariya a ranta tace har yaran yanzu ne zaa koyawa dabarar rike miji? Balle wadannan su Intisar da babu inda basa jefa kafa a duniya, suka kuma tashi da larabawa sarakan soyayyah?
A ganin ta Aunty Saratu da Hajjo na bata lokacin su ne kawai amma su Intisar, sun fi su sanin sirrin soyayyah.
Aunty Saratu tace ke gafara nan solobiyon banza, kin zauna kina ta asarar hawayen ki a banza kan wani shirmen Faisal! Kina mantawa Ya Faisal din ki ne fa?
An ce da ke soyayyah ta gaskiya na fading (kodewa)? Dubi yadda Hidayah ke gara Najib inda ranta ke so kaman ba shi ba bayan ke kin fita komi ma, amma kin zauna kina kukan banza wai baya son ki, karya yake! Yafi kowa farin-ciki a yau kuma yafi kowa cika burin zuciyar shi kawai yana pretending ne. In kuma kina ganin ba dai-dai na fada ba kiyi karyar rashin lafiya ki gani. Hajjo ta kyalkyale da dariya amma Intisar kuka kawai take yi.
Sun dauko hanyar air-port inda zaayi masu rakiya zuwa filin jirgi, motoci har guda goma a jere reras (in coboy). Faisal ya na tare da yan uwan sa cikin bakar Jeep din Daddy, ita ko tana cikin motar Haj. Saratu tsakiyar Maman da Hajjo, sai Goggo Jummai da Goggo Jami aminiyar Goggon a gaban motar yayinda Khalil ke jan motar. Ta dan dago ta dubi Anti Hajjo cikin muryar kuka tace
Aunty Hajjo ina son zuwa Shanono, duk da an ce Babana ya rasu ina son ganin wani abu da ya shafeshi koda kauyen ne kawai.
Hajjo tayi murmushi tace Mal. Ibrahim bai bar kowa ba, amma bazaa rasa Dattijan da suka san shi ba, kuma har gidan shi zan kai ki har gidan Hakimi mai ci a yanzu ya baki tarihin mahaifinki.
Malam Ibrahim mutumin kirki ne duk wani dattijo da ya kwana ya tashi a Shanono ya san shi, zai kuma baki kyakkyawar shaida a kansa da yadda mutuwar sa ta taba zuciyar alummar Shanono.
A filin jirgin saman Abuja, Daddy ya kamo hannun Faisal da Intisar yana murmushi ya dunkule su wuri guda, kana ya nuna masu hanyar matattakalar jirgin, ya girgiza kai ba tare da ya ce komi ba.
A haka suka juya suka shiga taka matattakalar idanun su cike da hawaye, suna yi suna waiwayen su. Hawaye suka zubowa Anti Saratu, har ga Allah bata ji dadin yadda auren ya zo wa Intisar dinta ba.
Murfi
A cikin jirgi Faisal na karatun jarida, Saratu na karatun Alkurani, motsi kadan ta juyo ta dube shi tayi murmushi ta juya ta cigaba da karatunta. Amma shi tunda ya daura idon shi a Daily Trust bai sauke ba, balle ya san Allah ya yi ruwan tsirar ta a kusa da shi. Service ta zo ta aje masu abinci tayi gaba abinta.
Intisar ta mike da zummar zata je ta rage mara bayan ta a je jikarta (channel) a kujerar ta, ta shiga toilet ta samu kan masai tayi zamanta tana tunani kawai, aranta tana kissima ko wanne irin rayuwar aure za su yi a hakan? Don ita kam ba wani fitsari da ta ke ji kawai dai tana ganin in tana zaune a wurin ba zai ci abincin ba kada ta samu hanyar da zata shiga sabgar shi shi yasa ta taso.
Shiru shiru Faisal yaga bata da niyyar dawowa ya dan soma duba agogon shi locoste yana mamakin dadewar da ta yi a bandakin sai kace mai nakuda ko kallon abincin da aka aje masa bai yi ba. Idan yi duba agogo sai ya maida kai a Jarida, can anjima kuma ya maida idon shi bisa hanyar tahowa daga toilet har aka soma shelar a daura belt jirgi zai sauka a birnin Ikko. Yayi tsaki tsuuu, ya aje jaridar ya mike ya bi bayanta, nan yaga wani shirgegen Bayerabe a kofar (toilet) din da alama shima ita yake jira ta fito, wani haushi ya sake kama shi ya kwankwasa kofar da yatsun shi ukku da dan karfi sannan ne ta bude ta fito.