← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nima balaraben ne da za ai mun gaye ko na miki kama da shasahashun samarin Faransa, wadanda mata ke masu yanga koko donni ba fari bane, da dai ba’a san asalin balbelar bane sai tace daga Makkah ta zo, da wasu idanun ki fiki-fiki kina wani lallankwasa harshe wai ke balarabiya nan ko fillo mai tallen nonon shanono ce.�

Dukkansu har ita basu san sanda suka tintsire da dariya ba har Intisar da ke ji da abinda ya ishe ta ta murmusa iya fatar baki, da suka dameta sai ta tashi tsam ta bar masu falon, daga baya Anti taji su sun sarke da hira ana ta darawa, tayi murmushi a zuciyarta tayi fatan abinda take zargi yazan tabbatacce.

An hadu har Daddy washegarin ranar ana karya kumallo kamar yadda yake a al’adar gidan, amma Najib da Hidayah sai aikawa juna kallo ake ana murmusawa duka Antin na hankalce da su tana dariyarsu, ta tabo Intisar ta nuna mata Najib da Hidayah na magana da ka, kamar kadangaru, da alama Hidayah rokonshi take ya daina kallonta Daddy na kusa da shi, shi kuma ya dage kai tare da dage gira alamar sai me in Daddy na kusa da shi?

Haushi ta shake Hidayah, sai kuma ta ga to me yayi mata zafi? In dai ‘ya’yan Hajiya ne gata nan gasu, wadda ba’a Haifa ba ma suna nan suna jiranta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.

Daddy ya aje kofi ckin natsuwa yana walainiya da idanunsa bisa makeken teburin cin abincinshi da Iyalinshi da yake ji incomplete har sai da yayi nasarar gano wanda bayanan, ya ce,

gasu, wadda ba’a haifa ba ma suna nan suna jiran ta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.

“Wai ina Faisal ne a gidannan?� Nasir ne ya amsa ya ce, “Na ke jin bai fito ba, kwanannan na rasa meke damun Ya Faisal Daddy, duk ya zama wani calm, cool and introvert (Shiru-shiru, sanyi-sanyi kuma mara son magana) ko murna ba yayi da samun aikin sa, har matsayin mataimakin D.G, kasan ba wai don qualification din shi ya kai bane illa kasancewarsa trained din England kuma ya nema a dai lokacin da shugaban NNPC yai retire mataimakin shi ya hau kujerar shi kuma aka bashi (Ass.Director) amma banga alamar yayi farin-ciki ba.�

Daddy yai dan nazarin maganan Nasir kana ya maida dubanshi ga Intisar data sunkui da kai, ita kadai ta san yadda take ji, ita kadai tasan halin da zuciyar ta ke ciki kan sauyawar rayuwar Faisal. Ai ita zata gayawa kowa Faisal ya canza, mutum mai far’a, raha, da hada-hadar jama’a (cheerful and passionate) shine a yanzu ya maida kansa bare a gidan ba tare da shiga harkar kowa ba.

Bata kai karshen tuninta ba ta tsinkayi muryar Daddy can tsakar kanta na cewa “Saratu-karama maza–maza kirawomun Faisal, ki gaya mai na ce kada a kara zama cin abinci a gidannan yana cikin gidan bai zo ba, ba na so!�

Ta mike tsam tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, tamkar mai tafiya bisan kaya kafafunta na harhardewa don sanin duk jama’ar falon ita suka zubowa na mujiya, haka kawai taji gabanta na faduwa fat-fat tana dosar sassan su bugun kirjinta na kara tsananta tamkar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi?

Hakan dai ta daure ta tsaya kofar dakin tai sallama ta yane labulen ta leka kanta kadan, don tunda take bata taba shiga dakin Faisal ba tun bayan tafiyar ta Riyadh, kuma koyaushe ta zo hutu yana makaranta, sadda ta same shi agarin kuma ana cikin tashin hankalin rashin Daddy wama yake ta wani neman dan’uwansa.

Da hankali ya natsa kuma ta dauki buhun fushi ta aza masa shida ‘yan uwansa kaf bakikkirin take ganinsu, bata kula su tunda kan su kadai suka sani sai Hajiyarsu, bayan fitowar Daddyn kuma ga abinda ya faru, inda Faisal ya bar kasar, to sai yau, don haka tana ta kissima me zata gani a dakin Faisal?

Karar zubar ruwa a toilet ya tabbatar mata Faisal na wanka ne, a hankali ta karasa shigowa da gangar jikin ta har tsakiyar dakin, sai kuma ta juya zata koma har ta kai bakin kofa kawai ta juyo ta karewa dakin kallo tsaf, haka kawai taji tana son yi mai kwa-kwa.

Tangamemen hotonta (window-size) tun tana shekaru takwas cikin ‘snow� wato kankarar Switzerland irin wanda ke dakinta na kuruciya, shine abinda zaka fara tozali dashi a gabas maso kudu na dakin.

Dakin babu wani shirgi komi tsaf cikin tsari da burgewa, dan matsakaici ne shimfide da marbles sai dan karamin chinese-carpet siriri a gaban gado (medium Italian-bed), da centre table na ‘row-glass� a gefe. Ba kujeru ko daya sai wadda ke jikin tebirin karatu da tulin takardu da jaridu zuwa magazines. Ilahirin dakin gauraye yake da parmanent watau tabbataccen kamshinsa na 5,000 dollar perfume tamkar kwalba guda aka rotse a dakin, nan ko tsabar kama komi nashi ne da turaren yayi, ma’adanar sanya kaya ta jikin bango da labulaye shara-shara farare sol sai sanyin raba ke kwarara harda kankara-kankara, don son sanyi irin na Faisal split biyu ce a dakin ta sama da ta kasa, ba wani kayan kallo sai allon kwamfuta har (Desktop, Mini, da Laptop) dake can wani corridor akan tebur na musamman makale da ‘yar kujerar kushin mai juyawa.

Cikin tafiyar nutsuwa ta iso jikin gadon inda ta hangi DIARY din shi da ya aza biro a tsakiya, da alama yanzun yai rubutu, sai ta zauna bisa (centre-table) ta soma bude shafukan cikin zakuwa.

Shafin farko wani dan karamin hotonta ne (pass-port size) shima tun tana kankanuwa, aji daya a makarantarsu ta Riyadh. Shafi na biyu maganganun da sukayi ne can baya kan Ronke Adeyemi. A kasan su yayi wasu maganganu da suka gigita ta inda ya rubuta;

Ya bar gida domin kar abinda ke ranshi game da ita Saratu ya tonu. Itace hakikanin yarinyar da yake so, yake kauna, take burgeshi yake kuma son ya aura da dukkan ruhi da zuciyarsa amma ba zai taba iya aure ba tana matsayin kanwar shi da suke uba daya?

Bayan wannan abubuwan da ya gamu da su ne a Birmingham, nasarorinsa da matsalolin da ya gamu dasu. Mu’amalarshi da wata yarinya Jean, saboda kamanninta da Saratun na sawa ya so ta.

Duk ta wuce wannan a gurguje jikin ta ba inda baya rawa zuwa inda ya rubuta matsalar karatunta, inda ya rasa kudin maidata Riyadh! Irin mawuyacin halin da ya shiga har Allah yasa Haj. Ta bashi kudi ya kai mata banki, yadda ya samo visa da su da yadda sukayi da Anti Saratu. Tun daga lokacin ya kudurce wa ran shi neman nashi: (neman na kan sa) don Saratu ta huta, don Saratu tayi karatu mai kyau irin wanda Mamar ta ke so tayi, don Saratu ta samu ingantacciyar rayuwa tamkar tasu, don Saratu ta samu rayuwa mai kyau koda mijin da ta aura baya da shi, shi ya zame masu komi. Ya alkawartama ranshi rashin dogaro da dukiyar Hajiya, dukiyar da Saratu bazata amfana da ita ba, bai ga amfaninta ba.

Akwai inda ya rubuta wahalhalun daya sha a Birmingham domin kokari da son fidda son ta. Amma abu kullun sai karuwa. Abinda ya kai shi ga kurba ‘giya� domin neman ‘relief�. Tuni hawaye ya wanke mata fuska. Ya cigaba da rubuta yadda giya tayi masa wata illa a huhu, babu wanda ya kula da shi sai Jean. Hakan dai a daddafe yayi-baya-yi-ba ya kammala karatun M. Sc bai ma tsaya yin Ph D din ba. Dawowarsa babu abinda ya fara karo da shi sai maganganun Anti Saratu masu kama da saukar mashi a kahon zuci. Cewa da ta yi,

“Insha Allahu duk wani jininsu sai ya ga tozarci a duniya.�

Tun daga lokacin ya yanke shawarar yayi baya da ita, don ya san Hajiya ta riga ta gama illata mutuncinsu a idanunsu. Idan ya cigaba da nuna mata kauna ba mamaki tsohon gyambon ya bare.

Abin mamaki, Yadda yayi nadamar dawowashi Nigeria ranar da Inteesar da Aminu suka fadi suka suma akan idonshi wai a matsayin suna son juna unknowingly ba tare da sani ba, yadda labarin ya gigitashi, tun daga lokacin ya ji ya tsani dan uwansa Al’ameen don yana ganin yaci amanarsa. A ganinsa shine mutum na farko da zai bada shedar so da kaunar da yakewa Intisar tun tana jaririya.

Ashe shima kansa Aminun bai san wacece yarinyar ba, bai san Intisar ce diyar Anti Amarya ba! Bai san yarinyar da yafi tsana fiye da kowa ce ba. Sai ya ta’allaka suman Aminu da cewa ‘shock� ne ba ‘so� ne ba, kuma daga ranar bai kara son ta.

Da zance ya bayyana cewa Saratu ba kanwarsu bace ya gigice, a lokacin ne kuma ya lura maimakon Aminu yayi dana sani sai ma warkewa da ya soma, wannan ya tabbtar masa da cewa Al’ameen na “love-sick� ne ‘rather than shock� kamar yadda ya tsammana, farin cikin ganin cewa zai mallaki Intissar din sa, daya shekara yana jiyyar soyayyar ta, (kura da shan bugu, gardi da amshe kudi), sai ya gwammace yin nisa da asibitin kada bakin ciki ya kasheshi kwanan shi bai kare ba.

Duk da haka ya zauna ‘in hope� ma’ana cike da burin sauyawar al’amuran, kaman yadda yake tsammanin shi kadai yafi kowa so da sanin ciwon Intisar diyar Anti Amarya. Amma a kwayar idon Al’ameen ya ga so tsantsa, ninkin-ba-ninkin na shi. Ya san Aminu Mai-nasara ne, ba kuma abinda ya taba sawa a rai bai samu ba. Ya san Saratu ta furta kin amincewa da auren Al’ameen ne only in frustration din (cikin bacin ran) kiyayyar mahaifiyarsu a kanta. Amma duba daya yayi mata ya gano babu inda bai amsa son Al’ameen a zuci da gangar jikinta!

How much do you like this story?
5/14/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three

*@Takori*

Page8ï¸âƒ£

A kalaminshi na karshe, wadanda kuma suke kalmomi na karshe a littafin da alama ma yanzun ya rubuta;
Chapter 61 · 0% Book details