← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 90

Sashe 49

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakunan su Khaleel ko gyaransu ki tabbata sai suna makaranta. Dukkan ‘yan aiki an salleme su sai Dela da zaku zauna tare, itama aikinta shine kula da diba duk wani motsin ki a gidannan don ma kar kiyi tunanin bin uwarki kauye, kin gane ko?�

Kanta cikin cinyoyin ta tana girza kuka tace “na gane� Hajiya tace.

“Abu na karshe shine, abincin ki Saratu shine wanda Khaleel, Idris da Furkan suke rage, sai ko karshen tukunya. Idan kika ci wani bayan wannan, kin san wannan?� Sai ta nuna mata jajayen wayoyin lantarki a bude (ma’ana shocking) “shi zan hada miki, har sai ya zuke wannan farin jinin naki da kowa ke cewa yana son ki.

Kin san kuma in na kasheki na kashe banza, tunda Babanki cewa yayi idan na sassauta miki bai yafe mun ba� ta dubeta sosai tace “Saratu ko Intisar ki ke, bai dameni ba. Daga yau sunan da na san ki da shi shine jikar Jummai, duk wadannan sunayen naki guda biyu ina gaba da su.

Na farko shine Saratu, sunan makiyyata ne da bani da makiyi ya ita a duniya aka lankaya miki, na tsani Saratu, na tsani sunan Saratu da duk wani mai irin sunanta ma har ke. Shi ko dayan, ba Babanki ya yanka rago ya rada miki ba, da na ne.

Faisal ne ya sa miki suna ‘Intisar� don haka na kwace tunda mallaki na ne. Saura me? Ke jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratu. Daga yau duk wasu kaya da kika san mallakin ki ne, na ba ‘yan aikina da zan sallame su. Daga rana irin ta yau, ga kayan sawarki na har abada! Ina fatan kina fahimta na?�

Sai ta watso mata wasu dogayen riguna guda ukku, baka, ruwan madara da ja, babu wani ado a jikinsu haka suke zulum, kamar na masu sharar titi. Ta cigaba da cewa

“ba zan hanaki wanka ba, don tsaftar abincin mu, don haka zaki dinga wanka da wani sabuhu wai shi ‘Aura� da na gani a hannun su Dela, shi zan dinga aje miki sinki-sinki kiyi ta yi, har da brush da maclean don kar ki fesa mana warin baki cikin abinci.

Kar kiyi zaton irin maclean din kin na da, sam, wannan wani ne wai shi ‘madam� da na gani a dakin maigadi, bayan wadannan Saratu komi sanyi komi zafi ko (Vaseline) ba za ki shafa ba. Na ke jin kin fara jinin Haila, don haka ga panties guda biyar da auduga katon-katon na ajiye miki don kar ki bata mana kitchen, sannan ga Hijabi ki dinga Sallah don nima Musulma ce bazan hanaki Sallah ba.

Wajen kwananki shine dandaryar dakin nan nasu Dela. Zan yi miki mutuncin tabarma da Babanki bai ce a baki ba, kin ga ai ni na fishi mutunci ko?�

A wannan karon batace mata uffan ba, don zuciyarta ta gama zagwanyewa.

Ta mike tana cewa “Shikenan dama sabuwar rayuwar ki, ‘yar baiwa, ko ba haka naji Faisal na ce miki ba? Idan kunne ya ji. To jiki ya tsira. Sai mun sake saduwa.

Kodayake da kyar ne zaki dinga gani na, don zai kasance koyaushe ina tare da maigidana, babu shirmen rabon girki ko? haka sauran ‘yan uwan ki a da. Ranar duk da kika manta ki kai dogon barci ranar ne zaki ganni. Gobe da asuba zaki fara bautar ki. Saratu mai sunan Saratu, Jikar Goggo Jummai� ta fita tana murmushi.

How much do you like this story?
5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ___________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three

*@Takori*

Page3ï¸âƒ£

A takaice sabuwar rayuwar da Saratu Bello (Inteesar) ta tsinci kanta kenan a gidan tsohon Brigadier Bello Makarfi. Kullum aiki take tukuru kuma bil hakki, tun safe har dare hakarkarin ta bai ganin kasa, ta zo kwanciya baya yace bai san wannan ba, ta kuma kwanta a dandaryar kasa, ga sanyi da ake mai tsanani a lokacin kin san kuma sanyi irin na marbles, abinki da yarinya ‘yar hutu, bata dauki wata guda ba cikin wannan aikatau din kakkarfan ciwon kiriji da matsiyaciyar mura su kai mata mugun kaye, saida ta galabaita tsahon sati biyu kamin Dela ta watsa mata kwayar maganin da ta amso a (chemist) hakannan Hajiyar tace aiki ba wanda zata rage sai dai ma ta kara da wankin kayan Khaleel.

Khaleel hankalinsa ya tashi da ganin azabar da ake ganawa Intisar a gidan su, shikansa yana mamakin wai Daddyn su ne kuwa anya yake biyewa Hajiya yanzun? Yayi fiki-fiki kamar bai taba sanin kowa ba sai Hajiya, bashi da tunani sai na Hajiya.

Ya kira ‘yan� uwan sa a waya dukkan su ya gaya musu abin mamaki, don shi har zuwa lokacin ya kasa yarda ba shirin (film) ne yake gani ba yana faruwa cikin gidan, wai Intisar din Daddy? Ita ne ta zamo bolar Daddy? Kuma Daddy ya saki Anti Amarya, to a kan me?

A satin su Najib sukayiwa gidan zuwan bazata, kowannensu cike da mamaki. Najib na kuka ya shiga tambayar Daddyn su shin me Saratu ta yi masu shi da Hajiya? Idan rigima ta hadasu da Anti Amarya ne ina ruwan Inteesar, naîve and innocent?

Daddy ya daka masu tsawa yace “ku bana son zancen banza, ku fice min a gida ku koma inda kuka fito, ni za ku gayawa ya kamata? Wani cikin ku ya sake yi min zacen Saratu babu ni babu shi har abada!

Duk son da kuke mata yayi wanda ni da na yi cikin ta na haifeta nake mata ne? Na maida ta ‘yar aikin, kuma baiwa, idan wani cikin ku ya isa to ya maisheta cikin sa ya haifo ya ‘yanta ta ta zama ‘ya, tunda ni ban san darajar ta ba.�

Daga Najib har sauran ‘yan uwansa sun yi zaton Daddy ya gamu da ‘mental imbalance� ne, tunda har ya iya ya saki Anti Saratu, ya kuma maida ‘yar da suke kishin kaunar da yake mata baiwa, to amma fa an gaya masu yana yin komi cikin hankali a office, duk yadda aka yi gamo yayi, sai su dage da yi mai Addu’a.

Ba yadda basu yi su ga Saratu ba cikin gidan Hajiya ta hana, tace kuma in suka dameta zata dagawa kowannen su nono.

Sai Najib ya rubuta mata takarda a madadin su duka, hawaye na zuba masu sharrrr, sun san tabbas da Faisal yana nan da an yi wacce za’ayi, to su ya za su yi su taimaki Inteesar tunda kuwa ga abinda lyayen su suka ce?

“Gaisuwa mai yawa Sister mu. Ba zamu ce ya kike ba, don mun san ba za ki amsa ba. Amma ina so ki sani cewa mun yi duk iya kokarin mu Inteesar kan al’amarin ki, kamin mu fahimci ‘all our efforts are futile (duk wasu kokarin mu na banza ne), ba za su fidda ke daga halin da su Daddy suka sanya ki ba.

Amma ki kudurce a ranki duk wani kunci yana tare da sauki, haka duk wata daukaka tana tare da jarrabawa. Ki kaiwa Sarki Allah kukanki, shi kadai ya san me yake nufi da hakan cikin rayuwarki, hakannan muma abinda zamu dage da yi miki kenan, domin al’amarin ya wuce tsammanin ki da duk yadda mu kai tunanin shi.

Sai dai ina so ki fahimci wani abu daya, wallahi ko kadan kada ki kullaci Daddyn mu, don na lura kwata-kwata ba a hayyacin sa yake ba, har yana ikirarin rabuwa da mu muma, in muka sake sa baki a maganar ki.

Ki tuna son da Daddy ke miki, fifitaki da yake a cikin mu, ki tuna ke ce abokiyar shawarar Daddyn mu kuma ‘ya mafi soyuwa a gareshi, tabbas wannan son, ba zai taba rikidewa ya koma kiyayya ba.

Inteesar jikina na bani ke wata ce a cikinmu. Kada rashin komawar ki karatu ya sanya zuciyar ki karaya. ‘When there’s life there’s hope, so always edpect success no mater how worst things seem to be in your daily life.�

Ni na tabbata wani babban alkhairi da farinciki ne zai sameki, har nan inda kike, har (kitchen) din da aka zabar maki rayuwa. Don haka ki cigaba da hakuri Allah zai kawo miki ‘dauki� Insha Allah. Da wuya mu sake zuwa gida nan kusa, sabida idanuwanmu ba za su iya jurar kallon irin ukubar da kike ciki ba, kuma daga mahaifiyarmu wai ido da kunya. Amma Insha Allah za mu nemi Anti don tattauna mai yiwuwa.

With much sympathy from your brothers.

(To amma su kansu fada suke, sun san bazasu iya dosar Antin su gaya mata halinda Intisar din nata ke ciki ba).

Kamar ko yaushe, sai ta kifa kanta cikin cinyoyinta ta shiga jera kuka mai tsananin ban tausayi. Wai haka kowa ke rayuwa? Ko ko ita kadai din ce? A duniya akwai wanda rayuwar sa ke da obstacles kaman ita? Koko ita bata da dauwamammen farin-ciki ne a rayuwar ta? A ina ta kuskuro Daddy, me tayi masa haka da zafi? Bata sani ba.

Kenan dole ta rungumi kaddarorin duk da zasu sameta in har da gaske ta amince ita tana son daddy har kuma karshen rayuwar ta tana kaunar sa duk da a yanzun shi din ya tsaneta fiye da kowa a duniya.

Da yamma ta shiga dakin su Khaleel kamin lokacin dawowar su makaranta tasa injin shara tana sharewa tare da killace masu takardunda suka wargaza.

A lokacin Khaleel ya shigo, ya aje file din da ke hannun sa ya zauna bakin gado yayi jugumm yana kallon ta kaman yace wayyo Allah!

Amma ita din bata ko dube shi ba aikin ta take tukuru cikin gwanin ta da sabo, ya mike yace ta bashi ya karisa yafi sau goma in injin sharar ya amsa to itama Saratu ta amsa. Alkawari ne ta dauka tsakain ta da Allah da kuma Hajiya cewa daga ranar da Hajiya tace ba ita ba ‘ya’yan ta to har ta mutu, in Allah ya yarda babu abinda zai kuma hadata da su koda gaisuwa.
Chapter 49 · 0% Book details