Sashe 83
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga can ta hango shi cikin motar sa porsche kafarsa daya a motar daya a waje, sanye cikin lallausar shadda yar Indonesia ruwan kasa-kasa dinkin Tazarce, fatar agogon roled da ke hannunshi ma ruwan kasa kasar ce haka takalmin fata na kasar Italy dake kafarsa ruwan kasa ne mai duhu. Ya rame ainun hakannan kyawawan idanunshi masu narkar da zuciyar ta sunyi ciki sosai ya kara fari, haka lallausan fatar shi ta kara gogewa sosai fiye da sanin da ta yi masa a baya.
Waya ce yake amsawa cikin lumshe ido, da gani zaka san kalaman da a ke gaya mai cikin wayar ba karamin dadi su ke mai ba, don har kwantar da kujerar motar yayi da alama dai cikin matsanancin nishadi yake. Zuciyar ta ce ta shiga harbawa da sauri da sauri don tuni ta fassarawa kanta koda wa yake maganar kawai Ronke Adeyemi.
Ta ja murfin tagar da karfi ta rufe garam, tare da zuge labulen gaba daya, ta durkushe a nan ta yi kukan ta mai isar ta. Ta tabbata a yanzun kam Faisal ya daina son ta! Duk wani so, duk wata kauna daya ke mata ya zagwanye sakamakon rashin maida mishi martanin dimbin soyyayar da ya shekara yi mata.
Ronke yake so tun-tuni har yanzu kuma bai daina ba, har ta zama bazawara uwar yaya uku still ya na son kayar sa. Ita kuma haka Allah ya so da rayuwar ta? Ba zata taba cin riba a soyayya ba. Allah Sarki!
Wai yau ita Intisar ce Faisal ya ke neman maraba da ita. Ita din da a da, baya da abin so da gani tamkar ta. Ita din da a da, in bai gani ba baya iya nutsuwa amma a yau rashin ganin ta shine nutsuwar sa, kwanciyar hankalin sa kuma abinda yake matukar so.
How much do you like this story?
5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four
*@Takori*
Page9ï¸âƒ£
Hunainah ta dafa kafadun ta, ta dago a hankali ta dube ta, sai ta rungume ta da karfi tayi kukan ta mai isar ta a kafadun yar uwar ta. Ta ce,
“Hunainah ni kuma haka Allah ya so da ni? Soyayyar yayan Daddy ne zata kai ni kabari na. Hunainah ya Faizal ya daina so na, leka ki ga da Ronke yake magana, ni kuwa ko gani na baya son yi.�
Ta ci gaba da kuka sosai yayin da Hunainar ta shiga taya ta suka yi tayi kamar wasu yaran goye.
Ta ce, “Ni wallahi zan je yanzu in bawa Ya Faisal hakuri, in gaya mishi hakikanin abin da ke zuciya ta. Idan ya auri Ronke din nan Allah Hunainah mutuwa zan yi nima in bi Alameen sai mu yi auren mu a can.�
Hunainah ta yi murmushi duk da hawayen da ke zuba mata, ta tabbata yar uwar ta bata cikin hayyacin ta, soyayyah na neman zautar da ita ta ce, “Aah, baza ki je ki bashi hakurin ba, me ki kayi masa? Laifin da kasan kayi shine kake bada hakuri a kai amma ba wanda baka san ka aikata ba. Ai ko Allah baya kamamu da laifin da muka yi a bisa kuskure. Mutun mai laifi, shi yake kama kansa da kansa ta nuna cewa ya san da wannan laifin. Ki bar shi ya je ya aure tan mana, sai me? Sai aka ce daga kansu babu sauran mazan aure?�
Ta share idonta tana murmushi ta ce, “Akwai maza da yawa a duniya. Amma a zuciya ta babu kaman Faisal! Ni kadai nasan shi ko wanene? Alkhairin sa da karimcin sa masu yawa ne a gare ni. Yafi karfin komi a waje na. Ina tabbatar miki Faisal ya fi so na da komi na duniya.
Duk wannan son da kika ga Alameen ya yi mini, wallahi wallahi Faisal yafi shi so na. Illa cewa shi Alameen baya iya boye abinda ke zuciyar sa kuma baya iya controlling din ta akan abinda yake so.
Sabanin Faisal da ya kasance mai juriya da karfin zuciya, ta yadda ko da a ce son zai kashe shi zai iya jurewa ba tare daya nuna ba. Ki taimake ni Hunainah in ganar da shi irin asalin kaunar da nake mishi yafi gaban duk wasu kananun zargi daya ke yi a kaina.
Ko me zan fada niki game da ni da ya Faisal ba zaki gane ba, da dai a ce kinsan irin rayuwar damu kai a baya ne. Abinda nake so kawai ki gane shine Faisal, wani mutun ne precious wato mai darajja da kima a zuciyata da girman sa da darajar sa da na ke gani ya zarta na kowa in kika dauke Daddy da Antina.
Ronken nan da kika da kika ji ana ambato ba son ta ya ke ba, zai aure ta ne kawai don ya rama tozarci da cin amanar kaunar da yake tunanin nayi mishi�
Ta sa gefen dankwalinta ta share idon ta, ta fyace hancinta ta yi murmushi cikin takaici ta ce,
“Hunainah, a lokuta da dama wasu alamura na rayuwa kan zo wa mutum ba a yadda ya tsammana ba. Na so Faisal tun yana a yaya na jini haka a gaba dayan rayuwata son shi nake ni din ban sani ba.
Soyayyar Alameen irin soyayyar nan ce da ke shigar mutum farat daya, ta rugurguza duk wani tunanin hankali da ya mallaka, kasancewarsa wani irin mutum na daban a cikin alumma, komi na shi ya kasance in style yadda babu zuciyarda ba zata kwadaitu da kasancewar sa abokin rayuwarta na har abada ba.
To haka ta ragargaza min zuciya ba tare da tsammani na ba, wanda a lokacin ban taba tunanin zan so wani da namiji a duniya bayan wannan ingantaccen son zumuncin da na ke wa Ya Faisal wanda a wani bangaren ba haka ba ne; so ne na soyayyah, na shaawar komi na shi.
Sabanin kaunar Alameen mai shigar mutun farat daya, soyayyar Faisal a hankali ta shige ni, ta bi jinni da tsoka, kasuwa da bargon jikina tun ban san kaina ba, ta yadda ko muryarsa na jiyo daga waje jikina ya fara tsuma kenan, haka zuciyata zata fara rawa ina dai kokari ne ina boyewa saboda Anti, da sanin cewa hakan ba dai-dai bane haramun ne, haramun din ma wanda Allah ya yi kakkausan hani a kai. Shima kamar ya san hakan, sai ya tafi.
A lokacin ne na samu nayi jinyar zuciyata har ta warke. Sai kuma Alameen ya zo, shi kuma da wata irin masiffafar soyayya mai shiga rai a lokaci daya. Duk da haka ina kokarin in tuno Faisal da dinbin karimcin sa. Ko a sanda na shiga wannan daumuwar da kukan zuci, bayan fitowar mu daga asibiti, kuka kasa gane hakikanin me ke damuna har kuka yi fushi kuka ce zaku tafi?
Wallahi ba komi bane damuwa da halin da Faisal ke ciki ne, damuwa da alamarin sa ne da ganewa da nayi ashe shima irin son nan da nake masa ya ke yi mun. A hakan sai na samu kaina cikin halin dimuwa da rashin abin yi. Duk da cewa kaunar Alameen ta fi rinjaya na alokacin amma na tuna Faisal, na tuna alkhairinsa, na tuna karimcinsa, na tuna kyautayin sa da jin kansa a gare ni.
Babu abinda mahaifiyar sa bata ce da shi a kaina ba, babu irin wulakacin da bata yi masa a kaina ba amma yace ya ji ya gani shi mai kaunar mu ne da ni da Anti na. Sanda ya tambayi Hidayah cewa wai ko zata iya aurensa, baki ji yadda na ji a raina ba.
Na ji tsoron in tace eh, to ni ya zanyi da rayuwata, yaya zan ji a raina? Sai na gode Allah da tace aah duk da nasan ni din bazan hada yanuwa biyu in aura ba. Ke Hunainah in nace zan gaya maki matsayin Faisal a zuciyata sai mu kwana mu wuni ban gama ba. To don Allah meye laifi na a nan? Ta ina naci amana? Yaya yake so in yi da raina? In banda ke ba wanda zan iya budar baki in gayawa zuciyata Hunainah, ki taimakeni in ganar da shi abinda ba zai taba ganewa ba, ba tare daya saurare ni ba. Ta cigaba da kuka mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta.
Hunaiah ta ce,
“Duk na ji, amma wallahi baza ki je ki wulakanta kanki a gabansa ba. Idan kika gaya masa hakan a yanzu cewa zai yi don kin rasa Alameen ne ba zai taba yarda da ke ba. Ki barwa Allah alamarin ki roke shi zabin alkhairi cikin rayuwar ki.�
Hakika nasihar yar uwarta tayi tasiri a gare ta, ta samar da nutsuwa a zuciyar ta. Ta ce Allah gani gare ka, na baka zabi ka zaba mun da mafi kyau.
To a gaba daya kwanaki biyun da su Hajiya suka yi a gidan bata kara ganin Faisal ba. Akwai wani abokin sa Tajudden mutumin Kano a unguwar Yan kaba can wajen sa ya ke wuni, tun safe yake ficewa bai taba cin abincin gidan ba. In banda Najib, Hidaya da hunainah babu wanda ya san me su ke ciki. Haka Najib ya yi iyaka kokarinsa don ganin Faisal din ya zauna ko na awa daya ne a gidan don su dai-dai ta da Intisar din amma ya nuna baya bakata kai ko son ganin ta ma ba ya yi, ya matsu lahadin ta zo su tafi don dai baya son iyayen su tuhume shi ne amma da tun jiya ya yi tafiyarsa.
Hidayah ta tabo Intisar da kafarta tana nuna mata Hunainah data rakube a gefe tana amsa waya sai kwasar dariya take cikin nishadi, ta ce cikin rada,
“Wai wannan saurayi ta yi ne?�
Ta yi murmushi ta ce, “Ke sai yanzu kika lura? Ai jiya abinda ta kwana yi kenan sai da na sa tissue na toshe kunnuwa na don dariyar ta ta hanani barci kamar wata shashashar madina�
Hidayah ta ce, “Ina ruwan farin shiga�
Suka yi dariya suka tafa. Ta sha jinin jikinta, ta dan juyo ta kalle su suka juyar da kai suna wata hirar daban, ta juya ta cigaba da hirar ta.