Sashe 38
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Brigadier ya zame ya zauna akan kilishi yana girgiza kai ya ce, “babu laifi� ya tambayi Anti Saratu su Bappa Sani da su Najib tace kowa yana lafiya, su Najib kuma kowanne yana makaranta. Yace ita Saratu me ta ke a gida bata koma makarantar ba?
Sai kawai Antin ta rufe zancen da cewa ai sun gama makarantar ita da Khalil don bata son zancen yayi tsayin da ran ta zai baci, ya tambayi Hajiya ko ina motocin gidan bai ga ko daya ba? Daga nashi har na amfanin gida? Anti Saratu ta ce,
“Don Allah Babansu Khalil ka tashi ka kintsa ka huta, ba yanzu ne lokacin wadannan kananun maganganun ba.�
Bai ki ta tatan ba, sai ya mike ya nufi sassan shi. Hajiya na jifan ta da harara, lokaci guda kuma tana lallatsa nambobin su Najib tana gaya masu su zo gida ga Baban su Allah ya fito da shi.
Intissar na ganin ita ya dace ta yi wa Faisal wannan muhimmin albishir ko don ta gyara zumuncin su data wargaza. Ita kadai zata iya bada labarin halin kuncin da ta tabbata zuciyar Yayan nata na ciki a dalilin yin biris din da tayi da shi.
A hankali ta shiga danna nambobin shi wadanda suke tamkar karatun sallah a cikin kanta, zuciyar ta cike da farin-ciki maras misaltuwa.
Kai tsaye ta samu bugu daya layin ya shiga to amma me? Muryar mace ce take tambayar ta ko wane ne akan layin? Ta yi dan jim, kirjin ta ya soma harbawa da sauri-sauri, muryar ta wani iri, cike da zargi ta ce,
“Plz, ba layin Faisal Makarfi ne ba?� Ta ce,
“Shine dai, amman ya shiga wanka yanzun nan, ko zaki sake kira anjima?�
Saratu ta ji wani abu ya zo ya soke ta a kahon zuci, zuciyarta ta cunkushe kwakwalwar ta kasa rungumar abinda kunnen ta ke son ta fahimta. Me kenan Ya Faisal ke yi a kudun? Ba dai neman matan banza ba?
Ta yi jifa da kan wayar ta hadu da garu wanda hakan ya haifar da darewar ta gida biyu, kafin wasu hawaye masu gudun gaske su zubo a kundukukin ta, tayi saurin sanya bayan hannun ta ta goge dai dai lokacin da Anti ta turo kofar dakin ta shigo, ba tare da ta lura da yanayin da Intisar din ke ciki ba tace
“Saratu, Baban ku yace ki hada mai ‘vegetarian-meal� mai kyau (abinci wanda babu nama a ciki sai ganye) bai son girkin kowa a yau sai naki, gashi na ganki sai kumburi kike kina neman fashewa?�
Taja wani dogon tsaki, “Tsuuu!� ta girgiza kai ta sunkuyar, Anti Saratu ta kama baki
“Ke Saratu, lafiyar ki kuwa?� Sai ta kara tsuga tsakin, ta mike tana niyyar shiga bayi domin adana hawayenta, bata san me zata ce da Antin ba.
Anti Saratu duk da cewa ranta ya sosu da wannan sabuwar halayya ta Intisar da koda wasa bata taba yi mata ba, wai tsaki? Ta danne nata bacin ran don sanin halin ‘yan kayan nata sarai ba’a jin damuwar ta sai da dabara, don haka Faisal ya sabar mata.
Sai ta kada kai ta juya ta ce,
“Ai sai ki ce in je in ce da Daddyn ba zaki samu damar yi mai girkin ba, sabida wasu can sun bata maki rai, amma ba ki yi ta tsuga masa tsaki ba.� Tasa kai zata fita.
Da sauri ta kamo hannunta, gaba daya ta fiddo abnormal idanunta waje, zaka iya ganin matukar razanar da ta yi cikin kwayar idon ta, ta ce,
“Wallahi-wallahi Mamar mu ba haka bane, kai umh, ni abin ne ma na kasa ganewa Allah.�
“To menene in ba shi kikewa tsakin ba?� Ta ce (kaman za tai kuka),
“Haba Mama, haba don Allah Mamar mu, yaya za’ayi na yiwa Daddy tsaki ‘eben if I run mad (koda na haukace)? Wai Ya Faisal ne ke da budurwa? Kuma ba ki ji ba har tana ce mun ya shiga wanka? Ko a ina suke oho, da har zai shiga wanka a gaban ta?�
Anti tayi jim, ita dai wannan closeness wato (kusancin) na Faisal da Intisar na bata tsoro, na kuma tayar mata da hankali, domin abun har ya so ya zarta na wa da shakikiyar kanwar sa, kar dai Saratu kishin Faisal ta ke?
Ta ja dogon tsaki itama tace,
“To ke ina ruwan ki?
Kina tsammanin Faisal bai isa yin aure bane da zaki ce ba zai yi budurwa ba? Kina nufin ba zai yi aure ba kenan don yana matsayin yayan da ke son ki? To ke din zai aura koko in kin yi naki ne zaki sa shi a gaba ku je gidan mijin tare? Kin ga ni bani cikin shirme, ta so mu je?�
Intisar data auna maganganun Antin cikin ma’auni na hankali da tunani sai ta ji Antin tayi gaskiya. Sai dai ita kam a duniya bata taba kawowa kanta yin aure ba tunda kuwa zai rabata ne da Ya Faisal da Mamarta. Bata kuma jin zata iya har abada! Ita kanta ta rasa maiyasa budurwar Faisal ta tsaya mata a rai ya ciwon makogaro.
Sakwara ta shirywa Daddy da miyar egusi da aka wadatata da ganyen alayyafu sosai da gandar fatar saniya wadda ta dahu tai lugub, sannan da busashshen kifi, ganyen yaji sosai miyar tayi shar gwanin sha’awa musamman da yake da manja tayi amfani, sannan ta shirya faten dankalin turawa shima da ganyen a ciki da ruwan tumatur zalla. A karshe ta shirya farfesun hanta wanda shima ta wadata da ganyen alayyafun, kana ta shirya salad da ruwan salad cream, heinz-beans da mayonnaise (kalb) wanda ta fara cakudewa da kifin gongoni nikakke na (starkist) da bineger, tabi samanshi da adon cucumber, tomatoes, karas dafaffen kwai da sauransu.
Duk da dai Daddyn ‘vegetarian-meal� ya ce ta shirya lafiyayyen farfesun macen tolo-tolo mai rai da motsi, irin wanda ya dahu lugub din nan har tsokar ta salibe da kanta, tace a ranta in Daddyn bai son wannan ai Mamarmu zata so, har ila yau, tayi dafa-dukar spaghetti wadda carrot, greanbeans, kabeji da hanta yafi taliyar fitowa sannan ta matse mai ruwan guava kamar yadda ya fi so a kullum ta sanya a firji.
Tayi wanka ta shirya cikin atamfa (exclusive) fara mai ratsin shudi kinsan irin wannan ‘colour� a jikin farar mace karkiso kiga yadda ta kara haskaka ta, ta nannade gashin kanta kamar kullum cikin shudin ribbon ta jerawa Daddyn abincin a inda ya saba cin abinci.
Saratu ba sangartacciya ba ce, ta iya komi a wurin Mamar ta, don tun tana shekaru sha biyu suke shiga kichin tare tana kallon yadda Mamar ke hadawa Daddy ‘delicious� don haka ne in ta tsaya ta tsarama abinci ko na Nicon-Noga albarka.
Daddy na cin abinci suna mai hirar abubuwan da suka faru baya nan amma ba su gaya mai me sosa ran ba. Hajiya ta tashi fuuu ta fice da ta ji Daddyn na tambayar Saratu ‘glasses� dinta sun tsufa ya dace a je Jidda sabon wata mai kamawa a canzo wasu.
Ya tabbatar Hajiya ta saida gabadayan motocin sa da yayi magana tace lalurorin karatun yara ne, yace amma larurorin har sun kai na wadannan miliyoyin nairori sai cewa tayi itama gani tayi an fara shiyasa ta bi layi (tana nufin Anti Saratu da ta saida ‘yar motar ta bayan kuma tana da masaniyar cewa shi Daddyn ne ya mallaka mata da kansa), bawan Allah, bai son maganar tayi tsayin da har zata janyo bacin rai, sai ya ce Allah ya mayar masa da alkhairi.
Kan ka ce meye wannan gida ya cika da jama’a masu taya Daddy murnar kubuta, wani abu da ya basu mamaki duk wasu tsofaffin abokan sa na nesa dana kusa wadanda rabon su da kofar gidan tun ranar da aka ce an kulle Makarfin sai gasu wai duk sun zo taya murna, dan adam kenan.
Malam Sani da Goggo Jummai ma da yamma suka iso garin, kada ki so ki tona zuciyoyin wadannan dattijai, su Najib ma duk sun iso ana ta hamdala.
Nasir ne ya gayawa Faisal ta waya shima yace Insha Allah gashi nan tahowa. Daddy bai samu kubuta daga mutane ‘yan taya murna ba sai karfe goma na dare, don haka bai samu damar fayyacewa iyalin shi komai ba na daga zargin da ake mishi Allah ya kubutar da shi sai ko Allah ya kai mu wayewar garin.
Washegari da safe kuma sai ga ‘yan aikin gidan da suka gudu suna dawowa daya bayan daya suna aikowa wai a gayawa ranshi ya dade ga mai ban ruwa da mai tada inji nan sun dawo bakin aikin su, Aunty Saratu na jin sanda ya leka yace a gaya masu wanda suka yiwa iyalin shi da baya nan ma ya isa ya gode sai tayi dariya.
Da aka taru ana karin kumallo kamar yadda ya ke a tsarin gidan kowannen su matse ya ke da son jin yadda wannan ijaba ta Ubangiji ta sauka kan mahaifin su, zuciyar kowanne fari kal kamar an mai bushara da Aljannah.
Furkan ne ya kasa hakuri ya bara, “Wai Dad, ya aka yi ne?�
Brigadier yayi murmushi, ya san abinda suka matsu da son ji kenan musaman Saratu karama da ta kura mai ido kamar mai gadin sa kada a sake kame masu Daddy a kulle. Fuskar shi ta yi fayau don duk wata kasimbar wahala ya shareta tas da kyakkyawan saisaye, sai dai ba karamar rama yayi ba tabbacin ya wahala kwarai da gaske.
Ya dubi iyalin shi daya bayan daya kana tsoffin shi Baffa Sani da Goggo Jummai, sannan agogon da ke manne a falon, ya ce,
“Ya isa a ce Faisal ya iso, don ya gaya mun ya biyo jirgin kasa tun daren jiya sabida tafiyar dare tafi dadi a jirgin kasa sai dai bata lokaci.� Ya kai duban sa ga Hajiya ya yi murmushi ya ce,
“Dan ki, naso a ce yana nan.�
Ta sunkuyar da kai kawai don tasan Al’amin yake nufi, ita kanta a yau tayi kewar shi ba kadan ba, tuni idanun ta suka ciko da hawaye.