← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 90

Sashe 28

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe labarin bakin ciki da tashin hakali ke nan yana tsimayen su su fito daga jirgi, wanda daga jin sa Saratu sulalewa ta yi nan take a kasa sumammiya.

*****

Cyril Stober ne tare da sabuwar Newscaster Hawwawu Gebi, ke karanto kanun labarun yau daga gidan talbijin na kasa (NTA Abuja), inda ya ce,

“An kama wadanda suka shiryawa kasa juyin mulki a ranar 5/5 wanda Benga Delsu da Bello Makarfi ke jagoranta. A yayin da aka shiga hasko fuskokin su daya bayan daya, kafafuwan su da hannaye duka daure cikin ankwa abin babu kyawun gani.

Suka kafawa Daddyn su ido kuriiii, abin tausayi tamkar sa zuko shi daga akwatin talbijin din. Cikin kwanaki biyu kacal ya rame, ya yi baki, ga wata kasumba ta tashin hankali da ta baibaye fuskar shi mai zati da kamala, kan shi a sunkuye, tun suna kuka kasa-kasa har suka rikice gaba daya da kakkarfa, Faisal ne ya mike ya finciko wayar T.B din ya hada ta da garu.

“Allah Daddy ba zai yi haka ba, wannan sharri ne, sharrin..�

Ya ma kasa karasawa saboda takaici da kunar zuci. Duk gidan ya koma tamkar gidan mutuwa, Inteesar tun zuwan ta da ta riski labarin, ta fadi ta sume, aka samu ta farfado har lokacin kudundune take cikin bargo tana rawar dari, zazzabi da masassara suka rufe ta, hakoranta sai karo suke da juna kawai ji ka ke kaf-kaf-kaf.

A ranar Najib da Bello suka iso, washe gari sai ga Nasir da Yasir su ma a gigice, Nasir mai raguwar zuciya nan falon Hajiya ya zube yana kuka riris shi da kananan kannen shi, ita kanta Anti ta fita hayyacin ta ba kadan ba, bata ko iya rarrashin su.

Najib ya ce,

‘Me zai sa Daddy ya sanya kan shi cikin wannan bala’i?�

Shi ko Faisal rantsewa ya yi da Allah ya tabbata Daddy ba zai taba aikata abinda ake zarginsa da shi ba, saboda president aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA a Jos suke tare har girman su har tsufan su ba a taba jin kan su ba balle a same su da wani sabanin ra’ayi, ya ya za a ce an hada baki da shi a kashe shi? Sun rasa ya za su yi? Sun rasa wa za su kai wa kukan su a yanzu ya dube su, yadda kasa take cike da su Daddy a wannan lokacin.

Sai Saratu ta share hawaye ta ce,

“Ya Najib, ni ina ganin mu taru mu yi ta addu’a da kan mu kawai, in Daddy ba laifn shi sai ka ga sun sako shi da kansu a lokacin da ba mu tsammana ba, amma duk inda za ku je a halin yanzun ba wanda zai saurare ku.�

Sai a yau Hajiya Nafi ta taba daga ido ta dubi Intisar a rayuwar ta, duba na mutum dan adam, ta ce, “Yarinya karama ta fi ku tunani, amma kun tsaya kuna ta koke-koken banza amfanin me ke gare shi?�

Washegari Najib ya nemo bisa din mutum biyar da shi da Faisal, Yasir da Hajiya sai Anti, suka dunguma kasa mai tsarki domin yin dawafi na musamman kan Allah ya fiddo mijin su/mahaifinsu cikin ruwan sanyi, suna addu’a fuskokin su jike da hawaye, tuni an manta da wani kishi, to ina wanda ake yin kishin domin shi?

Gidan farin ciki gidan Brigadier Bello Makarfi, komawa ya yi tamkar gidan makoki, dukkan harkoki da walwalar su sun karkatse. A satin Saratu da Nasir suka kamo hanyar kauyen Makarfi. Kallon fuskokin su kawai Baffa Sani ya yi ya tabbatar babu lafiya haka goggo Jimmai.

Nasir ba ya ko iya magana sai Saratu ce ta yi mai bayanin halin da ake ciki hawaye na bulbular mata a guje. Malam ya shiga rarrashin su yana tunatar da su duk wani soja haka ya gada, shiga hadarurruka ba yanzu Babansu ya fara ba, ya ma fi na wannan a baya lokacin da rikicin sojojin Amurka da Saddam Hussaini ya ritsa da shi a Baghdaza, da lokacin da aka kashe Major-General Aguiyi Ironsy ya kuma fito sumul kalau.

Tun a ranar ya tara malamai bila adadin ya raba masu abin sadaka suka dukufa rokon Allah. Duk wani shahararren malami da ya kwana ya tashi a garin Makarfi da wajen ta Malam Sani ya kai abin sadaka a taya su rokon Allah ya fiddo Bello, gudan jinin shi kuma bango abin jinginar su.

Nasir ya bude account din shi ya karowa Baffa kudi masu yawa.

Watan su Hajiya guda a Saudiyyah kafin su dawo. Gidan ya kuma komawa tamkar gidan mutuwa harkokin su suka kara katsewa, na makaranta sun kasa komawa, masu aiki su kasa komawa bakin aikin su, kowa na ji da yadda ya ke ji a zuciyarsa. Najib ya yi trying wayar Aminu, kwata-kwata ya daina amfani da layin, ya aika mai ta e-mail babu amsa. Da yamma ya shiga dakin Hajiya sai ya tarar da ita tafukan ta cikin fuska tana ta razgar kuka. A sanyaye ya zauna ya sunkuyar da kai ya ce.

‘Hajiya duk fa abin da ya yi zafi maganin sa Allah ne.�

Hajiya Nafi ta ce, “Na san da haka Najibullahi. Tunanin Al’ameen ke damuna, baya ko tunawa da mu balle halin da muke ciki. Mun yi da za shi Hull Unibersity, cikin ajiyana na banki na tattara na tura Ali dan kanin mahaifina ya binciko min Aminu a England, address din da ya bar mini ka san me ye? An ce kwata-kwata babu mai irin sunan shi a cikin shekarun da muka ambata da ya zo daga Nigeria.

Na rasa inda zan sa kaina in ji sanyi. Idan na rasa Aminu na rasa ubansa ina zan sa kaina?� Sai ta kara tsanannta kukanta.

Najib ya lankwashe kai abin tausayi ya ce, “Amma dai Hajiya kin san dai cikin kowanne hali Ya Aminu zai iya kula da kansa a ko’ina.

A ganina bai dace kisa damuwar inda yake a ranki ba har ya zo ya dame ki, hakan yana iya zamo miki illa, kuma a cikin wannan halin da muke ciki na kewar mahaifin mu ke ma mu rasa farin cikin ki akan ya Aminu shi kadai ransa? Tunda dai kin san ko ba dade ko ba jima zai dawo ne?�

Ta ce, “Ya kuwa bazan damu da inda Al’ameen yake ba, alhalin duk cikin ku babu mai kauna ta tamkar shi? Babu mai gudun bacin raina tamkar shi? Babu mai son abin da nake so tamkar shi? Ba mai damuwa da bakin cikina tamkar shi? Ya ya kuwa ba zan damu da inda yake ba?� Najib dai ya yi ta lallashin ta har ya samu ta yi shiru.

Washe gari ya zauna ya zanawa Aminu duk halin da suke ciki ta cikin yanar gizo internet yana rokon shi ya zo su taru su san hanyar da za su kubutar da mahaifinsu da ya tabbatar da ba ya da laifi. Ya tunasar da Aminu yanzu ne fa ya dace su nunawa ubansu kaunar da ya wanzar da rayuwar shi a nuna masu. Ya tabbata ya kammala koma wane irin karatu yake yi cikin wadannan dumbin shekaru amsu yawa da suka gabata. To amma me?

Daga Ameenu no reply har tsayin sati guda, wannan ya kara tunzura ‘yan uwan. Sai a kwana na takwas ne ya cillo wani matsiyacin rubutu don a ganin sa ai abin da ya jiyewa Daddyn kenan tun farko da ya yi ritaya amma shi bai jiyewa kansa ba.

Rubutun Al’ameen Bello, ya nuna bai damu ba, bai kuma da ranar barin inda yake, domin America, ta zama wani ginshiki na farin ciki da kwanciyar hankali a gare sa, ta yadda har bai jin wani abu da ya shafi gidansu zai sa ya baro ta. A takaice dai ga abinda Ameenu ya rubutowa dan uwansa Najib.

America teaches the cultivation of peace of mind to me, not as an escape from life into protected quiescence, but as a power center of which comes driving energy for constructing personal and social living. One is responsible for the outcome of what would be sealed.

Al’ameen Bello

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two

*@Takori*

Page4ï¸âƒ£

Najib ya fashe da kuka, ‘Faisal, anya wannan Yayan mu ne da na sani mai so da kaunar Daddy?�

Shi ko Al’ameen ba su san a halin bakin cikin abin da ya ke tunanin mahaifin su ya aikata ne ya furta wadannan kalaman ba, a ganinsa me Daddy ya rasa a rayuwa da zai tsunduma kan shi cikin irin wannan masifa in ban da rashin godiyar Allah? Har nawa duniyar take da zai bari neman mulkin duniya ya rinjayi imanin shi?

Kudi dai na gwamnati albarkacin aikin soja bai san wane iri yake so kuma ya yi ba. Ya manta cewa, “Kalmomi da alkawarirrikan da aka yi su cikin fushi, kamar cin wuta suke, ba za ka taba iya maida barnar su ba.�

Daga Faisal har Najib sun ce a kyale Ya Aminu ya yi yadda yake so. Allah zai fidda Daddy ne ba sai da taimakon sa ba.

Ranar Asabar Baffa na Makarfi ya zo da malamai kimanin guda goma aka bude masu nan sashen baki, sati guda suka share suna saukar Alkur’ani mai tsarki, an yanka raguna har ba iyaka an yi sadaka haka sauran abubuwan sadaka iri-iri iyalin Brigadier ba mai jin kyanshin bada ko mene ne.

Sai da Aunty Saratu ta zamo babu ko sisi a account din ta ta hada da saida bungles din ta na danyar gold. Haka samarin nan na Brigadier ba sa barcin kirki kowannensu kamar bai taba mallakar kwandalar kansa ba, duk sun jeme abin gwanin ban tausayi.

Hakika Bello Makarfi ya gina iyalin shi a bisa tubala na so da shakuwa da shi, ta yadda rashin sa ya zamo masu tamkar rasa rayuwar ne dungurungum. Mutum ne da ya iya zaman duniya kuma mutum mai nuna wa ‘ya’yan shi da matan shi kauna da kobo, lafiya da karfin shi.

Ya tsaya tsayin daka domin iganta rayuwar su ta yadda har sun fi kaunar shi a kan-kan su, dama duk wani abu da suka mallaka a duniya.
Chapter 28 · 0% Book details