Sashe 4
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Al’ameen ya gaya wa iyayensa ya yi aure da Ihsan shekaru uku da suka wuce. Ba kamar yadda ya zaci za su karbi abin ba, matukar farin ciki suka yi, suka ce hakan ya yi kyau. Sun tabbatar har yanzu Al’ameen na bisa turbar Addinin shi, Islam.
Wunin ranar zungur kowanne na ba da labarin abin da ya shafe shi bayan rabuwa, amma yawanci labarin juyin mulkin su Daddyn ne ya fi yawa. Hajiya ta rasa ina-taka-saka-ina-taka-aje da Ameenun ta.
Da daddare ta same shi dakin Faisal da ke binsa wanda ke Birmingham a lokacin inda ya sauka, ta titsiye shi sai ya bata labarin surukarta Ihsan, fara ce ko baka, doguwa ce ko gajeriya? Sai ya ce, “In kin yi hakuri Hajiyana, da kafarta za ta shigo.�
Ta ce, ‘Har yanzu bata haihu ba?�
Ya ce, ‘Hajiya Ihsan fa kabila ce, Mamarta kirista ce, a bisa rashin sani na aure ta, ban san hakan ba sai yau din nan.�
Da alama zancen bai ko dada ta da kasa ba sai ta ce, “To me ye? Ai ba haramun ba ne, gaya min inda Addini ya ce kada a hada zuri’a da ita tunda ma ba ita ce Kiristar ba, ko itan ce Addini ya amince.�
Shi kam mamakin yadda Hajiya ta so Ihsan haka farat daya yake, tun ba ta gan ta ba. Ya ce, ‘Shin ina Aunty Saratu ne tun da na zo ban ji duriyar ta ba.�
Ya kashe wancan zancen kenan. Hajiya ta yi wani dan jimmm, kafin ta ce “Tana gidansu?�
Ya juyo ya dube ta ya ce, “Me ta ke yi?�
Ta ce, “Ta haihu ne tana wankan biki.�
Da far’arsa ya ce, ‘Allah Sarki Antynmu, sai yanzu Allah ya kara ba ta haihuwa again?�
Hajiya ta kyale shi. Ya ce, “Gobe in Allah ya yarda a Makarfi zan yi sallar Azuhur, me aka samu ne?�
Hajiya fa ta gaji da zancen su Saratu da yake ta yi mata, daurewa kawai take don kar ta bata wa Aminu rai daga zuwansa, amma da tuni ta zazzage shi, zagin da bai taba tsammanin wata uwa na yi wa dan da ta haifa da cikin ta ta shayar da mamanta ba. Amma lallai ya ce zai ci gaba da yi mata zancen su Saratu yanzun nan za su watse. Ya mike yana amsa call din Dr. Rehab babban likitan “meritime� cikin ‘yar masifaffar wayarshi da ba ta ma zo mana nan Nigeria ba, balle in san sunan ta, ya gama ya rufe ya dora bisa tebur ya wani irin juyo cikin slow motion hannuwansa duka biyu harde bisa kirjinsa ya yi facing din Mamarsa, muryarsa ta yi sanyi ainun kamar ya aro, a sanda yake cewa,
“Hajiya na manta in tambaye ki Inteesar, ina Intissar diyar Aunty Saratu?�
Hajiya ta hadiyi wani daddafan miyau da ya tokare mata makoshi, saboda zafin da kalamansa sukai mata a zuci, ta daure ta ce, ‘Tana makaranta a Riyadh.�
Ya ce, ‘Har yanzu ba ta yi aure ba? Na yi zaton she may be a mother of one, two …or three kids? (Tana da ɗa guda ɗaya, biyu ko uku)?�
Ta ce a dakile, ‘Har nawa Intisar din take ko sakandire bata gama ba.�
Ya ce, ‘Yaya lalurar idon da na jawo mata, na tafi na bar ta da shi?�
Ta girgiza kai da kafadu duka tare da yarfar da hannu alamar ko oho.
‘Ba ni da sani a kan wannan sam, kuma an ce da kai makancewa ta yi kwata-kwata?�
Ta kwabe baki kamar ta rufe shi da duka. Ya juya mata baya ba tareda sanin halin da yanayin fuskarta da ma zuciyar ta baki daya ke ciki ba, ya kai hannu ya shafi tausassan labban sa ya yi murmushi shi kadai ya ce,
“Na dade ina tunanin halin da na bar yarinyar nan, tunanin ta na daga cikin abubuwan da suka sa na ki kaina, na ki kasar haihuwa ta, da duk ‘ya’ya masu irin halina na taya iyayen su mata kishi.
Ban sani ba kuruciya kan ingiza mutum ga abin da bai dace ba, idan ya mallaki hankalin kansa abin ya zo ya dame shi. Na sha gayawa Ihsan labarin yadda na nakasta ta, na sha gaya mata irin hazaka da kwazon ta, har Ihsan ke ganina as a wicked brother (mugun ɗan uwa), haka na sha gaya mata irin kyawun Saratu tamkar ‘yar tsanar da ke motsi……�
Hajiya ta mike, domin abin ya ishe ta ta ce,
“Kai da Allah shashashan banza, ka cika min kunne da zancen hofi, Intasar din ta ci uwarta, uwar ta Saratu ta ci uwar ta, kakar ta Jummai ma ta ci uwarta, sai me?�
Ya dube ta sakale! Duk ta hade rai kamar ta mutu don bakin ciki, ya ce, “Hajiya me ya yi zafi haka?�
Ta ce, “Uban ka ne ya yi zafin, na gaya maka daga yau sunan yarinyar nan da na uwar ta ya fita a bakin ka, bana so!�
Ya russuna ya riko kafafun ta ya ce, “Hajiya ki tuna, mu fa mu kai laifi, don na yi nadama na tambayi kanwata da muke uba daya laifi ne? Kin san dai dole na nemi yafiyar Intisar a cikin hankalin kan ta tunda ta nakasa a hannuna?�
Ta ce, “Kalaman ka ne suka bata min Aminu, sai ka ce wani wanda ya yi kisan kai kuma ma dai ni bana son su a bakin ka kwata-kwata, don a duniya ba ni da makiya kamar wadannan mutanen amma ku kun kasa gane hakan, kun ki ku daina ambaton su.
Yadda ake shafe matacce a doron kasa a mance da shi, haka nake so ku manta su, amma kun ki, kun fi son su da ni, ‘yan uwanka yau shekara guda ba su neme ni ba saboda tsinanniyar yarinyar nan Intisar nima na kyale su, ina murna ka dawo, don kai ne kadai mai sona da duk abin da nake so, amma za ka fara kai ma daga dawowarka.
Ni Nafi na shiga uku! Saratu ta lashe min kurwar ‘ya’ya, ba mamaki, Intisar MAYYA ce, yo dama…�
Sai ta fizgo dankwalinta ta toshe bakinta da karfi, aurenta� za ta kashe da Bello Makarfi, wanda har yaumittakumi ba ta fata. Shi kadai take so, shi kadai take fatan su mutu tare, su rayu tare su tashi tare, sannan su fadi tare. Kishin sa ne yasa take duk abin da take domin ba ta son kowa ya rabe su ita da ‘ya’yanta, to amma ‘ya’yan kamar shegu shanyayyu, tana janye su, tana masu gata� suna nesantar ta zuwa makiyanta? Sai ta sa kuka.
Al’ameen ya juyo cikin karayar zuciya, ya russuna yana lallashin Mamarsa ya ce, “Hajiya ki daina fadar haka, ya ma za a yi mu so wasu fiye da ke? Kin kasa fahimtar mu ne, kar ki manta Intisar kanwarmu ce, jinin ta ke gauraye cikin gaurayen jikin mu, dole akwai wannan kaunar ta jini, don haka dole mu ji son ta ko yaya ne, amma kin sani, ko kowa na son Intisar BAN DA NI, har kullum ni Al’ameen ne dan Hajiyarsa�., yafiyar ta kawai nake nema, na hakkinta da yake kaina.�
Ta dago shi tsaye ta ce, ‘Na fahimce ka Aminu, amma ka yi min alkawarin ba za ka kara son Intisar ba har son zumuncin?�
Da sauri ya ce, ‘NI dama ina son ta ne? Amma jini ya rigaya ya hada mu ko? Dole mu’amala ta hada mu. Alkawari daya zan iya yi miki Hajiyana, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!�
Ta yi murmushi ta shafi kansa ta ce, “Aminu na, shi yasa na ke son ka fiye da kowa har kullum, me za ka ci gobe da safe in Allah ya kai mu in gayawa jikar Jummai tun yanzun?�
Ya ce, “Ni bana cin girkin tsoffi, idan ba naki ba ne, da safen zan shiga kitchen da kaina in dafa koko in soya kosai.�
Hausar shi ta ba ta dariya ta ce, “Ba a dafa koko damawa ake yi.�
Ya dan fiddo ido ya ce, “Hajiya ta, ni fa ba abin da Amrica ba ta koya min ba, ni nake dafawa kaina abinci, tun kafin in yi aure har kuma na yi auren, ni nake dafa mana duk abin da za mu ci. Matata lazy gal ce in ta yi min nata bana iya ci.�
Ta ce, “Wannan ‘yar aikin tawa in ta yi za ka iya ci, domin yarinya ce budurwa kuma ga ta da tsabta, hakan nan duk gidan nan girkin ta muke ci har baban ku, don tana da ilimin abun, don haka hutar da kan ka shiga kitchen.�
To Al’ameen duk sai ya ji yarinyar ta burge shi tun da karamar ta da ita har take girkin da Hajiya da Daddy ke ci su yaba, ya san ba komai ke burge Hajiyarsa ba da wuya a yi mata abin da za ta ce an yi mata daidai kwata-kwata ba‘a iya mata, sai yau da ya ji daga bakin ta, uwa uba ta ce yarinyar tana da tsabta don a sanin da ya yi wa ‘yan aikin Hajiya a sanda yake nan duk mugayen kazamai ne barin Asbi da Ladi, kuma wai har ilimin girkin gare ta bayan ya sha jin Ihsan na cewa da ta tsaya ya koya mata girki gara ya sake ta a kan abincin.
Kitchen bai fasa shiga gobe da safe in Allah ya yarda, in ya ga kwarai ta iya din ya kawo Ihsan ta koya mata, don yanzu ya amince shi kansa dole su canza tsarin rayuwarsu tunda kuwa rayuwar aure a Nigeria ba za ka taba hada shi da na Turai ba, inda culture (Al’adu) sun bambanta.
Ko da yake in har bai manta ba ita da kanta Ihsan din wata rana ta taba gaya masa hakan, lokacin da yake sangar tata da yawa cewa, don yana ganin ba su da kowa ne a can din sai junansu.
A lokacin bai yarda ba sai yanzu wai yake gayawa kansa dole Ihsan ta canza taku in har tana son rayuwar auren su ta tafi straight ba karkacewa. Ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi.