← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juma’a, 1 Ga Watan Sha’aban
Tun da duku-duku ta tashi ta soma shara da goge-gogen gidan. Ta zuba Omo Aerial cikin ruwa zata goge gidan bata san robar ta fashe daga kasa ba ruwan yana zuba, santsin Omon ya kwashe kafar ta ta fadi da fuska kafafun ta suka bada wata irin kara mara dadin ji, tsautsayi dai da baya wuce ranar sa, tun daga lokacin bata kara sanin inda kanta yake ba.

Sai da safe Hajiya ta sauko daga sassan Daddy ta diba ko’ina ta ga ba inda aka gyara, ta lelleka kichin, jakar tasu ba abinda ta daura masu na karin kumallo. Ta kwantsama ashariya tace “Saratu!�

Tayi kiran fiye da sau biyar bata ji ta amsa ba. Ta kira Ado direba tace “maza-maza samo mun kebur ka gani� cikin mamaki yace “Hajiya wane irin kebur?� tace “irin wanda ake daure Itace da shi� bai tsaya tambayar ta me zatayi da shi ba ya tafi, amma zuciyar sa cunkushe da zargin ko matar na da tabin hankali ne?

Da kyar ya samo don sai da ya shiga kanyen wasu Gwari tukunnah, ta yi mai godiya harda bashi kudi, ta shiga neman Inteesar kusufa � kusufa cikin gidan, a tsakiyar falon yara ta same ta a kwance, tsammanin ta barci ta ke don ta yi aiki ta gaji, ta shiga tsula mata daurin kebur tun tana ihu tana motsi har ta kasa hassala komi. Sai ta juya tana murmushi ta ce,

“Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!�

Dela mai aikin Hajiya, duk akan idonta Hajiya ke dukan Inteesar, duk da cewa wata babbar lalura ce ke damunta, da ganin irin kwanciyar da ta yi ka san bata lafiya bace.

A da, Dela bata damu da harkar yarinyar ba tana ganin ko ba mahaifiyarta ai akwai Ubanta cikin gidan da yakamata yasa ido a kanta, amma a yau sai ta ke tambayar kanta ko me ‘yar kyakkyawar yarinyar nan ke ma Hajiya?

Ko ma meye da laifin Maigidan, ko ba ‘yar sa bace bai kamata yayi mata irin wannan rikon wulakancin ba don ba uwar ta balle ‘yar sa ta cikinsa.

Ta ciccibeta tasa a baho ta jika tsumma cikin ruwa tana matsa mata jiki, inda duk ta sa tsumman sai tayi kara kaman ranta zai fita.

Ita Dela a ganin ta taimako ne take yi bata san azaba take kara mata ba, tunda kuwa tafasasshen ruwa ne take danna mata cikin tsokar ta da ta bubbude, a ranta ko tausayi ne fal, tana mai yaba kowacce kankanuwar halitta ta Intissar tare da koro tasbihi ga Allah Al’khaliku daya kaga halittar yarinyar.

Ko fatar jikinta mutum ya gani yasan akwai hikimar Allah a ciki, irinsu ne ake kira matan manya; ga tsayi ga zati. Yadda Hajiya ta ruda mata jiki da kebur duk jinni ya taru ya kwanta yarab, abinki da farar fata jazur kar kiso kiga yadda ta koma kamar jini zai feso ta yi wani irin jazur, hatta idanuwanta da kyar take iya bude su sabida yadda suka kumbure sukayi luhu-luhu amma ba su fasa fidda hawaye ba.

Tunda ta ke, wani abu makamancin wannan bai taba sauka jikinta da sunan duka ba, lebbanta keta motsin da ke nuna ‘kafa ta�, Dela ta fahimci targade ne ta samu a kafarta ta dama, tana gyara mata tana kara amma muryar bata fita sam, bata san sanda itama ta soma hawaye ba ta ce “‘yar nan, shin ina mahaifiyarki ta tafi ta barki da wannan azzalumar mace?� Wannan kenan.

Sati biyu bayan wannan tana tsaye tana kankarar abincin kasan tukunya kamar yadda Hajiya ta tsara mata. Duk dokokin data kafa mata tana kokarin ganin bata tsallake ko daya ba musamman hurda da su khaleel.

Saratu tana da ‘zuciya�, babu abinda ta dauka da zafi kamar cewa da Hajiya ta yi meyasa ta ke son ‘yayan ta, bayan ita ta tsaneta?

Don haka har kullum take kaskantar da kanta ga su Khaleel da nuna cewa ita ba kowa bace face ‘yar aikin mahaifiyarsu. Ko gaisuwa bata sake bari ta hadasu ba duk da su suna iya kokarin su wajen nuna mata kauna da jawo ta a jiki, hakannan karbar mata aiki amma duk bata kulawa.

Furkan ne ya shigo kichin din rungume da ledoji shake da mayuka, sabulai, kayan gyaran gashinta zuwa su biskit din ‘digestive� da take yawan ci, ya rausayar da kai yadda dai zata ji tausayin sa ta amsa ya ce,

“Inteesar, ki yiwa Allah ba don ni ba, ki amshi wannan, kudi na ne halali na, Allah kin ji na rantse.�

Ta yi tsaki ta aje tukunyar ta dauki abincin ta data kankaro a murfin kwano tayi gaba tana cewa.

“Idan dayan ku ya sake shiga harkata to Hajiyar ku ce zata raba mu.�

Amma can a karkashin zuciyar ta wani gefene ke ta amon tambayarta “Saratu har Faisal?�

Wasu mulmulallun hawaye suka mirgino mata a guje. Tsayawa neman tabbacin wannan amsar kan iya haifar mata da psychological depression.

Aikin karfi da wahala, rashin kula da rashin gyara, kar ki so kiga yadda ya taru ya maida Saratu Bello, dalibar kimiyya a Riyadh, wadda ada baka banbance ta da mutanen Abu-dhabee ko Kuwait, a yanzu Saratu bata da maraba da ‘yan aiki Fulani ko irin Bararojin nan da ke aiki gidan masu kudi.

Gashin kanta dankare wuri guda rabon da ya ga ruwa ko (kumb) har ya manta balle uwa-uba man gyara. Farinta ya dushe kamar yadda zuciyarta a kullum ta ke a cunkushe da bakin-cikin da ba za ta taba rabo da shi ba.

Bata nadamar kasancewa diya ga Bello Makarfi, kuma har abada ba za ta yi ba. Bata bakin-cikin irin abinda ya yi mata matsayinsa na Ubanta mahaifi, kamar bakin-cikin rashi da rabuwa da mahaifiyarta. Tana taya Mamarta kishin rabuwa da soyayyar Daddy Makarfi, don ta san har abada ba zata sami makwafinta ba.

Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyar nan tata sai dai komi tana danganashi daga Allah ne, ta kuma san ko ba dade, ko bajima in Allah yayi zasu sake ganin juna to za su sake a cikin kudurori da yardarsa ta amince bai manta da su ba.

Bata bakin-cikin bautar da take yi a gidansu, don zata iya yin komi domin Daddy Makarfi. A yanzun ma ta kan sa a ranta ne cewa Daddy ne ke cewa “yi min kaza Saratu� ranshi na mai dadi yana sa mata albarkar nan da baya gajiya da yayyafa mata, to akan me zata yi bakin-ciki?

A da, Daddy ya nuna mata matukar kauna da bai nunawa daya cikin ‘yan� uwanta ba, ya daukaka darajja da martabarta bisan ‘ya’yansa bakidaya, a yanzu kuma ya tsaneta; kenan yanzu (it’s her turn) yanzu ne ya dace ta nuna mai tata kaunar ta hanyar yiwa matar daya ke so biyayyah? Yanzu ne zata cika wannan alkawarin da ta yiwa Daddy na kasancewa a cikin umarninsa muddin rai? Yanzu ne ya dace ta yi masa biyayyar da cikin ‘yayansa babu wanda ya taba yi masa ta hanyar daya zabar mata, watau aikatau din gidansa?

Ta tabbata Ameenun da ya ke alfahari da biyayyarsa, ba zai taba yi mai wannan ba, bai kuma taba ba, kenan yanzu ne ya dace tacigaba da yi mai biyayyar da tayi alkawarin yi mai wadda Ameenu bai taba yi mai ba?

A ganinta ta ragewa Daddyn ta nauyin dubbunnan da yake biyan masu aiki sama da goma dake cikin gidanne, a yanzu ta zama makwafin su, to a kan me zata yi bakin-ciki?

A lokacin ta fidda jin dadin rayuwa kwatan-kwata daga tsarin rayuwarta, ta amince da zabin Daddy ne dauwama a matsayinta na Jikar Jummai ‘yar aikin Hajiya. Ta amince haka Allah ya tsara mata tata rayuwar. Wata kwalliya ta kece raini da ‘ya’yan masu kudi ke yi ita dama tun fil azal ba ra’ayinta bane, tafi tafiyarda tsarin rayuwarta bisa tsari na larabawan data yi rayuwa a cikin su, balle yanzu da take ‘Yar Aikin Gidan Su?

Tunda dai zatayi wanka ta wanke baki shikenan. Bata Addu’ar Allah ya fitar da ita daga halin da take ciki illah Addu’ar Allah ya dai-daita tsakanin Daddy da Anti Saratu.

To in baku mance ba a littafi na daya, cikin halin da bakon Miami, wato Al’ameen Bello ya diro gida Nigeria kenan ba zato ba tsammani, tare da matarsa Ihsan, dawowar da ta kunshi canjin sabbin al’amura da dama cikin rayuwarsu baki daya. Sauran abubuwan da suka biyo bayan dawowar duk kun ji su kaman dawowar Faisal da Mamarta. To amma ya akayi Maman ta dawo? To bari mu bisu mu gani.

How much do you like this story?
5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three

*@Takori*

Page4ï¸âƒ£

Lagos/ Talata

25 Ga Watan Shawwal
Dr. Hajjo Hassan Biu, kodayake da yawan dalibanta a LASU sun fi kiranta da Dr. Biu, sunan Biu ta sameshi ne daga mijinta Hassan wanda yake mutumin garin Biu ta jihar Borno. Ta baro ofis da karfe hudu dai-dai na yamma a matukar gajiye cikin motar ta Legend (One Door), sauri take data kai gida ta yi ‘freshen-up� wannan gajiya da ta kwaso ga Maigidanta da yaranta tasan suna nan suna tsimayen ta ne ita kadai, dai-dai (junction) din da zata dauki titin Victoria Island danja ta tsaidasu, ta yi tsakin takaicin bata mata lokacin da za‘ayi a ranta ko tana tsinewa wannan traffic-congestion na garin Lagos, tsayin minti ashirin ba’a basu hannu ba, ta sake tsuga tsaki ta bugi sityari tace “damn it� kana ta sake duba agogon hannunta dana motar baki daya, yanuna karfe hudu dai dai na yamma dai-dai kokacin da wani Bayerabe ya zuro mata tulin jaridun mako ta tagar motar ta.

Ta harareshi cikin takaici amma me? TELL Magazine ta wannan ranar dauke take da wani ‘headline� da ya sa jikinta tsuma, da hamzari ta dauka ta bashi kudinsa, tabi rubutun a gurguje da mamaki “INNOCENT-MAKARFI, RELEASED!� Ma’ana “an sake shi a matsayin mara laifi� a shafi na gaba kuma “Makarfi celebrated his sixtieth birthday, at Nicon Noga, on 2/2…� watau Makarfi yayi bikin cikar sa shekaru sittin a hotel din Nicon-Noga dake Birnin Tarayya ranar biyu ga watan biyu, sai kanun labaran yadda kowanne ya kasance.
Chapter 50 · 0% Book details