← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 90

Sashe 33

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun billo daga wani jeji a yankin Adamawa muka dira a Gongola, muka dawo Dukku ta Gombe, muka sake tashi muka koma zama a Alkaleri ta Bauchi. A kan hanyar mu ta isowa Medile daga Yako, mahaifinmu wanda shine shugaban ayarinmu ya mutu, sai kanin sa Baffa Lalajo shi ke kula da mu kuma shi aka nadawa rawanin mahaifin mu.

Bayan rasuwar sa ne muka lula cikin nahiyar Kano, a wani jeji bayan garin Shanono muka kafa bukkoki, muka saki dabbobinmu muka yi zaman mu anan cikin kwanciyar hankali. A can duk aka haife mu ni da kanwata Hajjo, da Baffa ya mutu ya bar Innar mu da tsohon cikin ta, kushewar ‘yan uwa da kakannin mu har yanzu suna can.

Malam Ibrahim sarkin noma shine Sarkin Noman kauyen Shanono, mutum ne mai arzikin gaske, a garin Shanono bakidaya, babu wanda ya kai shi nome amfanin gona mai yawa, ya mallaki tafka-tafkan gonaki sama da goma ya kuma fi duk manoman garin samun amfanin gona mai albarka. Dabbobi garke-garke da gidajen gona da wannan mutum ya mallaka har ba zasu lissafu ba, a takaice abinda za’a ce shine duk fadin garin babu wanda ya kai shi arziki.

Abin tausayi da wannan bawan Allah shine bai taba haihuwa ba, har shekarun girma suka riske shi. Shekarun su ashirin cif da matar shi ta ladan noma Shatu amma ko batan wata bata taba yi ba.

Daga baya ne ya shiga neman auren karamar yarinya budurwa, tare da Addu’ar Allah ya sa karshen wahalar sa ta zo na samun Magaji daga gareta, wanda ya ke kwana rokon Allah ya bashi kamin ya dauki ran sa.

Shekaruna goma sha hudu Baffa na ya ce ya ba sarkin noman Shanono aure na. Na yi kuka nayi bakin cikin kiyayyar auren tsoho sa’an Baffa na kaman in mutu, amma sai Baffa ya daga ni ya jefa a katuwar tukunya, ya zane da tsabga, sai da ya yi mun tabban da har abada ba zasu goge a gadon bayana ba kana ya kyale ni, ya kuma ce idan na sake tada hankalina kan auren sarkin noma sai ya kore ni daga rugar mu, mahaifiyata da Yafendo na babu yadda suka iya, haka suka wanke ni suka ba sarkin noma. Sarkin Noma ya dauki son duniya ya dora a kaina, wannan ne ya sayo mun bakin jini a wajen kishiya ta, Shatu, kullum cikin yadar mun da magana ta ke kan yarinya ta dani na auri tsoho sabida tsabar kwadayin abin duniya, na juye kan tsoho kinibabbiya, har sai da ta kai ko tsakar gidan bana iya fitowa in har ba Sarkin Noma na gidan ba, bana umh bana umh-umh kullum sai sakar auduga.

Ba sai na fadi ba ku ma shaida ne a kan irin kyawun da Allah yai min, kyawun da akan ce duka rugar mu babu kama na. Da na lura Shatu ba kishiyar kirki bace sai na shiga yiwa kaina addu’o’in tsari daga sharrin ta, tare da yin taka-tsan-tsan cikin duk wasu al’amurana da ita.

A zamana na shekara guda kacal da Sarkin Noma na fahimci shi mutumin kirki ne, mai alheri mai saukin kai da taimakon talakawa, duk garin kowa na kaunar shi da girmamashi suna kuma taya shi Addu’ar Allah ya cika mishi dadadden burin rayuwar shi kamin mutuwar sa. A hankali-a hankali sai na ji nima ina kaunar shi sabida kyawawan halayen sa.

Shatu kan ce ta san na zo ne in haihu da Sarkin Noma, in kashe shi in kwashe dukiyar sa in gudu, to kuwa na haihun ta gani, domin ita tana cikin sahun matan nan da ake kira (juya).

Yafendo na da dangina da ke ruga kan ziyarce ni lokaci-lokaci. Shekara ta daya a gidan Sarkin Noma sai ga ciki ya billo, amma da ya ke ni doguwa ce babu wanda ya farga har sai da ya shiga wata bakwai, ni kuma dama ba baki ne da ni ba balle in fadiwa wani. Ko shi kansa Sarkin Noma bai kawo a ransa wai ciki ne da ni ba duk da kibar da na yi, to abu ne da duk an fidda rai.

Rannan Aliero (Yafendon mu) ta zo duba ni kamar yadda ta saba, na tashi don in debo mata ruwa a randa sai cewa tayi

“yaki Dije, ikon Allah, ashe juna biyu gareki baki fadi mun ba? Ke dai Aradun Allah zurfin cikin ki wataran sai ya kahe ki� nace “juna biyu? Yafendo me ar juna biyu?� tayi tsaki ta fito soro ta tadda Sarkin Noma, tace zasu dauke ni rainon ciki, ba kuma zan dawo ba sai na haihu. Farin ciki a wajen Sarkin Noma kema kin san fada ma bata baki ne. Ya daga hannu yayi godiya ga Allah ya shiga rabar da dabbobin shi da kadarorin shi masu yawa sadakah, ya kuma kara kyautatawa Malaman da ke taya shi rokon Allah kan su kara dagewa da Addu’ar Allah ya sauki Dije lafiya.

How much do you like this story?
5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two

*@Takori*

Page7ï¸âƒ£

A rugar mu na haife sankaceciyar diyata mai kama da ni a komi. Tun daga yatsun kafa, nannadaddiyar sumar kai har zuwa baki na jaririyar nan bata bar komi ba illa digon tawwadar Allah da ke gefen hancin ta na dama wanda ni bani da shi.

Ranar suna Sarkin Noma sa da rago ya kayar ya rada wa yarinya suna Fatimah. Ban koma gidan Sarkin Noma ba sai da diyata tayi watanni uku kaman yadda ya ke a al’adar mu. Iyaye na sun yi mun gara mai yawa da burgewa. Ranar da daddare Sarkin Noma ya dauki Fatima ya tsaga mata uku-uku a tsakiyar kirjin ta na family din shi. A ranar mun yi kwanan farin ciki da Fatima a tsakiyar mu, amma sai me? Wayewar garin Litinin muka shafa babu jaririyar mu babu dalilin ta.

Sarkin Noma ya yayi salati ya buge ni yace “ke Dije, ina kika aje Fadima?� Na mike nima ina mutstsike ido nace “ina ko na aje ta banda nan tsakiyar mu?� Ko kamin in kai karshen magana ta na soma kuka, aka caje gida kaf ciki da bai babu Fadima babu alamar ta. Shatu tasa hannu aka ta rafsa ihu tace

“yanzu ‘yar daya jal, da muka samu aljannu sun dauke?� Jin abinda tace a take na fita hayyaci na ko jin su ba na yi na zame kasa a sume.

Shi kuwa Sarkin Noma tuni hankalin sa ya gushe dama kuma ga rudu irin na tsufa, cewa ya ke “ina! Ina za’a ace aljannu sun dauke mun ‘yar guda daya da ban samu ba sai a tsufa na?�

Yayi titi a guje mutane suna rike sa yana fizgewa yana kara nausar titin. A can gefe kuma mota ce akori-kura ta taho cike da tumaki da gudun gaske, irin motocin nan na kauye da basa jan birki sai sun je tasha. Abin ne ya zo da karar kwana in ba don haka ba ‘yar turewar da motar ta yiwa Mal. Ibrahim Sarkin Noma, bai isa a ce ya mutu ba, amma ko shurawa bai kuma yi a wurin ba.

Da na komo hayyacina iyayena suka zo suka dauke ni na yi takaba kaman yadda Addini ya tsara. Baffa na babban malami ne, masani kwarai a cikin ilmin Alkur’ani. Ya dage da binciken Allah ya nuna masa musabbabin batan diya ta cikin Istikhara, cikin kudurar Allah kullum kishiyata Shatu yake gani. Rannan mafarki yayi wai ta haka rami tana neman bizne Fadima sai wani bawan Allah ya fizgeta yayi sama da ita, wanan kadai ya isar mishi gane cewa Shatu ce musabbabin batan diyata.

To bafillace bai iya fushi ba, balle Baffan mu tun can zuciyar shi bata da linzami. Yasa samarin rugar mu suka haka mai wani wawakeken rami a jeji, manyan ‘ya’yan shi Leko da Kallamu yasa suyi fakon Shatu in ta dawo daga rafi su rufe mata ido da baki da bakin kyalle su dauko mai ita.

Hakan kuwa aka yi. Kamar kullum Shatu ta dawo daga rafi da tulunta a ka, tana tafe tana ‘yan wake-waken ta hankalin ta kwance, duniya tayi mata dadi domin ita ta mallake komi na Sarkin Noma ko allura bata bari an bani ba, don a cewar ta yayi wasiyya tun yana raye cewa komi nashi ita ya mallakamawa, sabida tare suka tara abin su, sai ji tayi an kayar da ita an yi sama da ita, iyakar rudewa kam ta rude sai salati ta ke tana kiran iyayenta da kakanninta, bata zata ba bata tsammana ba ta ji ta kif, cikin rami, bayan ta da kasusuwan ta babu wanda bai amsa ba, tuni ta dauka mutuwa ta yi aka kawota kabarin ta.

A lokacin duhun dare ya mamaye sararin samaniya, sai Leko da Kallamu suka gudu suka buya. Baffa na ya fito daga maboyar sa, nannade cikin farin rawani, ga farar auduga duk ya bi fuskar shi da ita, hannun shi na dama rike da kafceciyar addar saran bishiya, ya tsaya a bakin ramin yace “baiwar Allah, yau taki ta kare idan baki gaya mun inda ‘yar kishiyar ki take ba� Shatu tasa kuka ta ce,

“wallahi ba cewa nayi su kashe ta ba, cewa na yi su kai ta dokar daji su yar, amma ba dajin nan kusa ba, cewa na yi ma su kaita wajen shiyyar nan kwata-kwata inda hankalin wani dan adam bazai taba kaiwa ba, sai in gaje gonaki da shanun Sarkin Noma ni kadai� Baffa yace “su waye suka taya ki wannan danyen aiki?� Tace “’yan sholisho ne na kira a tasha, yanzu ko zan sake rayuwa ba zan ce ga kamannin su ba balle inda suke�. Sai Baffa na ya mika mata hannu ta kama ya fito da ita yace “ki je ki ke da Allah, mun barki da fitowar rana da faduwar ta, idan Allah ya yarda sai kin ga sakayyar Allah ta sauka a kanki tun daga nan gidan duniya�. Ashe Baffa ya fadi da bakin mala’iku,

Shatu na tafiya tana waiwaye ko gaban ta bata gani sabida tsoro da razana, ta afka wata korama da ke gudanar da ruwa, ruwa ya tafi da ita ba’a kara jin duriyar ta ba har yau din nan.
Chapter 33 · 0% Book details