← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 90

Sashe 66

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce, “To Daddy itama bata kula ni sai ‘ya’yanta (Su Hidayah) to ni ma ba sai in zauna inda na fi wayau ba?� Ya girgiza kai cikin murmushi “a’ah, ba zaki zauna inda kika fi wayau kadai ba. Uwa-uwa ce, matsayinta ya wuce duk yadda kike tsammani, ko ita bata kula ki tilas kuma wajibi ne ke ki kulata, ki dinga nuna mata kauna.

Above all, Hadizah bafillatana ce usul fillanci take maki, wannan kunyan na dan fari na nan tattare da ita ga kuma rashin shakuwarku, wanda wannan sai a hankali. Ke zaki taimaka ku shaku. Idan bakya kusantarta yanzun ba zaku taba sabawa da juna ba tunda yake ke mace ce, gidan aurenki zaki cikin dan lokaci, ki daure kiyi hutun karshen wannan shekarar tare da su. Don ba mamaki kamin ku dawo an daura auren ku duka.�

Ta cira kai a hanzarce tana yi mai duban mamaki kana tayi saurin sadda kai, cikin siyasa irin tasu ta manya ya ce,

“Wai yayane? Ke da mutumin me kuke ciki ne, na ganshi yana ta mana zarya kamar marayan da ya rasa uwa, me kuka yanke ne? Su Najib fa ku suke jira don tuni sun gabatar da bukatarsu suna son asa masu rana da wuri.�

Yayi shiru yana nazarin irin karbar da tayi wa zancensa.

Tayi lamo da wuyanta a masangalin kujera abin tausayi. Idonta ya kawo ruwa raw-raw cike da nadamar hukuncin da ta yanke akan Al’ameen, wanda tasan abinda bazai taba yiwuwa bane. Tayi kokarin maida hawayen don bata son Daddy ya gani.

To amma shi Daddyn duk tsawon lokacin idanunshi na kanta, tsoron shi Allah, tsoranshi kada Intisar tace bata son Aminu. Da ina zai sa kansa da rigimar Al’ameen yadda jiya ya sashi gaba da magiyar a daura musu aure koda tace bata son shi!

Abinda shi kuma ba zai taba Iyawa ba wato danne mata hakki don farin cikin nashi? To amma shi kansa yakan so kasancewar al’amarin ba don komi ba sai don cigaban zumuncin bangarorin guda biyu, hakannan zuri’arshi kadai ya taba yiwa sha’awar auren kamilallar mace irin Intisar! Balle gudan jinin sa Ameenu?

Kwata-kwata tarbiyar Ihsan bai mishi ba, tun haduwar su na farko. Hakannan banda mutuncin Dr. Argungu da yake gani da tun zagin da Ann Hathaway taje ta yi mishi har ‘office� kan wai Al’ameen ya ci mutuncin Addininta don kawai ta bashi shawara kan zaman shi da Ihsan gaba daya suka sire mishi.

Haka shigowa da Ihsan ke yi rungume da Al’ameen har cikin dakinsa abin na damun sa kwarai, don dai ba yadda zai yi ne. Cikin murya mai sanyi ya ce,

“Saratu, ki gaya min saboda Allah ba kya son Al’ameen ko?�

Ta shiga girgiza kai da sauri alamun ba haka bane, hawaye suka soma biyo kumatun ta. Tsohon Brigedier Bello Makarfi, ya mike zaune daga kishingiden da yayi, ya daura hanunshi na dama a kanta, ya ce,

“Wannan hawayen da kike kwarararwa a kullum yana damuna, sai in ga ni ban kai ga taka rawar uba har yau a gareki ba. Bayan ukubar da na sanya ki cikin gidana, still na kasa share miki hawaye a shekarun farin � cikin ki, na kasa tsayawa in gina maki rayuwa ta kwarai tamkar yadda na gina ta ‘ya’yana, na zalunce ki, na bautar dake, ban baki kwakkwaran ilimi ba har yau, ban idasa da zaba maki miji na gari a girman ki ba.

Idan bakya son Al’ameen kada ki ji nauyi na, ki kawo ko waye ni kuma mai share hawayen ki ne, in har ya cancanci ya amsheki daga hannuna, zan bashi.

Ki bar la’akari da kasancewar Aminu da a gareni, ni duk daya kuke, sai ma in ce kin fi shi. Domin ke ‘ya ce da ban taba ganin mai biyayyar ta da son iyayenta tamkar ke ba. Na rantse, a cikin ’ya’yan da na haifa bakidaya babu wanda ya ji kai na ya ke kuma kaunata tamkar ki.

Don haka don baki son Aminu baya nufin bakya son Daddyn Aminu, Illa shi Aminu ne ba kya so saboda wani aibinsa ko wani kuskure daya aikata miki kika kasa yafewa!

Ni dai hakannan nake son ki da Al’ameen, ba don komi ba sai don masifaffen son dana lura yana yi miki mai gigigatarwa, mai neman fitar da shi daga hayyacinsa, mai neman raba shi da rayuwarsa.

Duk kuma bakomi ba ne face sakayyar Allah garemu a kan ki. Ina son inda za’a so ki ne, har illa masha Allahu, ba inda za’ayi miki son wanin ki ba. Abin nufi, masu aurenki domin wani naki, kyawu ko dukiyarki.

To sai naga Al’ameen ne irin mijin da ya dace da ke, irin mijin da na dade ina yi miki burin samu, zai kuma rike mana ke da dukkan kauna irin wadda muke so ki samu a gidan aurenki.

Na kuma dade ina sha’awar yiwuwar hakan a raina tun kamin shi ya furta, tun a sanda yake cin zalinki naga abubuwa dayawa cikin kwayan idanun sa, na kuma san ko ba dade ko ba jima Allah na nufin wani babban al’amari a tsakanin ku. Amma in kina ganin na so kaina ne Saratu fada mini?�

A gaggauce ta rarrafa gareshi ta gurfana a gabansa, ta girgiza kai da karfi ta ce,

“A’ah! Har abada Daddy nasan babu mai kaunata a duniya tamkar kai, har kuma iyayen da suka haife ni. Ba kuma zaka taba yin wani abu da sunan son kai a gareni ba. Kuma ni baka taba bata min ba, dai-dai da rana daya balle ka sa ni cikin ukuba.

Bana kuka domin kiyayyar Al’amin, kuka nake don so da kaunarsa, da suka yiwa zuciyata katutu. Allah Daddy, ban taba fada ba, amma Aminu na taba ji har ruhi da bargon jikina, nake kuma azabtuwa a zuci da gangar jiki domin kaunar sa!

Kuka nake domin nadamar tsatstsauran hukuncin da na yanke a gareshi wanda na zauna nayi tunani akai na tabbatar ba zai taba yiwuwa ba, domin kiyayyarta gareni ba karama bace, da kiyayyata aka halicceta baza ta taba yin abinda na kudurta ba.

Kuka nake domin sanin cewa na jefa Al’ameen dina cikin halin kaka-ni-kayi, halin da bazan iya fitar da shi ba, halinda zai iya janyo muguwar gaba tsakanin sa da wadda ta haifesa, ta shayar da shi mamanta, ta raine shi har ya girma ya kai munzalin da har na gani na ke bege, take kuma son sa fiye da kowa a duniya.

Dama tace ni din mayya ce, yanzu zata kara tabbatar da zarginta cewa na mayancewa ‘ya’yanta, bayan ni kullum kokarina shine in nisance su, in yakice su daga cikin rayuwata amma na kasa!

Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara, ba don kaunar jini ba sai don cewa su wani bangare ne daga jikin Daddy Makarfi. Jinin da yafi karfin wulakanci da tozarci a gareni. Ina tsoron hukuncin da zata yanke masa, wanda ko menene ni ce zan zamo sanadi.�

Daddy ya yi murmushi, yace “Gaya mun hukuncin da ki ka yankewa Al’ameen din ki?� Cikin hawayen dai tace

“Cewa nayi yaje yazo da Hajiyar sa, ta nemi gafara ta kan kiyayyar da ta wanzar da rayuwarta nuna mini, ta kuma furta amincewa da auren mu da bakinta, sannan ne zan maido soyayya ta, in rungume shi matsayin miji na uban ‘ya’yan da nake burin samu daga tsatson Daddy Makarfi.� Ta cigaba da kuka sosai, ta ce,

“Daddy daga baya nasan ban kyauta ba, nayi nadama, hukuncin yayi masa tsauri, don bazata taba amincewa ba, shi kuma ba zai dawo gareni ba sai da amincewar ta, tunda hakan muka yi alkawari. Ni kuma ba don komi nayi hakan ba sai don kwatarwa kaina da ‘ya’yan da zan haifa a gaba ‘yanci daga gareta.

Ina guje masu halin da zasu iya fadawa a gaba daga ukubar ta. Ni kadai nasan ita ko wacece? Ku bar ganin wai don iyayena sun bayyana zata daina ki na, a’ah, kiyayyar ta gareni a cikin jinin jikinta take, bazata taba dainawa ba. Koda kuwa a ce ni ce mafi rinjayen iyaye a duniya.

To amma ai shi Al’ameen na zalunceshi, na hukuntashi da laifin da ba na shi ba ko Daddy?� Tayi shiru tana maida lumfashi cikin zargin kanta.

Ga Mamakin ta sai yayi murmushi, ya dora hannu bisa kafadarta, ya ce,

“A’ah, ba ki zalinceshi ba, kin yi dai-dai. Ban taba ganin yarinya mai tunani, hazaka da hangen nesa irin ki ba Intisar! Ina ma a ce sauran yara mata zasu yi koyi da dabi’un ki da an daina wulakanta su a gidan aure.

Soyayyar dake zuciyar ki bata rufe maki ido ga hango gaba ba, da abinda gobe zata iya haifarwa ba. Sadaukarwar ki da sanin ciwon kan ki bazasu tashi a banza ba!!!

Abu ne da bazan iya gaya miki ba, Illa ni ma Haj. Nafi ta cuce ni ba kadan ba, wanda hakki ya koma mata. Ban saketa ba, amma ga gidan, ga ‘ya’yan nata kiri-kiri ta kasa zama a cikinsa, to tun a duniya kenan wata shari’ar sai a Lahira!

Komi za kiyi Saratu ki sa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki. Kar ki ji tsoron mutum domin shi ba komi bane face abin halitta daga yunbu, mai yin komi daga kudirah da Iradar Ubangiji kuma bisa nufi da yardar sa.

Magana ta karshe shine ina bayanki akan kudurinki na cewa sai Aminu ya kawo mahaifiyar shi nan a gabana ta nemi a fuwarki, bisa dimbin azabobin data gana miki, wanda ko Allah baya yafe hakkin wani kan wani. In kuma har baki yafe mata ba ai Allah ma bazai yafe mata ba.

Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince ki zamo mata a gareshi wannan tunani ne mai kyau. Ni kuma alkawari daya nake so ki min shine, daga yau bazaki sake zubda hawayennan haka kawai bada kwakkwaran dalili ba muddin ina raye�

Ta sa hannuwanta duka biyu tana sharewa tace

“Na daina Daddy, kuma in har hakan ta faru ni kuma na amince da auren Al’ameen koda a gobe ne, kuyi duk abinda kuke ganin ya dace.� Ya ce,
Chapter 66 · 0% Book details