← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 90

Sashe 52

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kauyen Makarfi, Cikin Garin Kaduna
Aunty Saratu tun bayan rabuwar su da Daddy tana gidansu a Makarfi, kullum kuma idanunta basa rabuwa da tsiyayar da hawaye duk kuwa da kulawar da lyayenta ke gwada mata. Baffansu cewa yayi Allah yasa hakan shi yafi alkhairi agaresu duka ya kuma kawo mata mijin aure kurkusa, (ya ma manta ciki ne da ita).

Hakan kuma bai bata tsakanin shi da dan dan-uwanshi ba daga matsayin da ya rikeshi watau Da. Duk da cewa shi Makarfin ya watsar dasu gabadaya don ma kar suce ya maida Saratu, don shi yanzu ko mai irin sunanta baya son ji, kafafunshi kuwa rabon da su taka garin Makarfi shekara guda da doriya kenan.

Shi ko Baffan musamman yake nikar gari ya je har offishinsa yace yazo ne su gaisa kurum ya ga lafiyar shi tunda shi ya watsar dashi akan abinda bai shafeshi ba.

A irin wadannan lokutan Daddy kan ji kunya matuka. Tun yana dari-dari da Baffan har ya dawo ya saki jiki dashi suka koma kamar da, don ya lura Baffan mai kaunar shi ne don Allah ba wai don wata tsiyar hannunshi ba. Don kuwa ko kwandala baya tambayarshi in har bashi ya dauka don kashin kansa ya bashi ba bare har yace ya maida Saratu dakinta.

Daga baya kuma ya wanke kafa ya soma zuwa Makarfin don kansa, amma baya shiga cikin gidan, iyakacin sa falon soro da ya ginawa Baffan don bakin kunya. Hakannan tun bayan fitowarshi yasa an rushe gaban gidan anyi mai zubin zamani an kuma wadatashi da komi na jin dadin rayuwa.

Tun rabuwar shi da Anti ko naira biyar bai taba dauka ya aika mata ba a matsayinta na me dauke da cikinsa. Wannan bai dami Hajiya Saratu ba, don ita kanta mai kudin kanta ce a halin yanzu, a sabili da aikin da ta fara bayan fitowar Daddyn a sanda kuma duniya ta dawo masu sabuwa, sai kawai ta shiga tari, ga wanda Daddyn ke basu ita da Hajiya naira dubu dari-dari duk wata, don haka yanzu ‘account� din ta cike yake da (millions) gashi kuma ba abinda tsoffinta basa yi mata.

Koda wasa Baffa Sani bai taba daukar carbi da niyyar wai Allah ya gyara auren Saratu da Daddy ba, sai dai Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta.

To amma Goggo Jummaifa? Kusan kullum sai sun kai ruwa rana da Baffan kan don me ba zai mike ya nema masu makarin asiri ba bayan yana da tabbacin wannan duk aikin tsafin su Hajiya Nafi ne?

To in tsafi suke ita Addu’a ta ke, kuma ko gonakin gadonta zasu kare sai Saratu ta koma dakinta.

A irin wadannan lokutan sai Baffa yace “kema tsafin zaki tafi nena kenan? To ki dinga yi dai kina tunawa duk matar da taje wajen boka ya bayyana mata wani sirri da Allah ya boye ko ya biya mata wata bukata da take ganin Allah ya gaza ko jinkirta biya mata, sai anyi kwana arbain ba’a karbi sallar ta ba, hakannan tayi shirka�.

Goggo Jummai bata tsinkawa don tasan bata nufin kowa da mugun nufi face nemowa diyarta farin-ciki wanda yake a wuyan su iyaye, hakannan ta san boka ta san Malam.

Shi kansa abinda yasa yaki tsoma baki don yana ganin da Saratu da Bello duk daya ne a wajen shi ba wani banbanci, kuma da suyi zaman aure tare da kar su yi, duk sunansu ‘ya’yan sa.

Idan ya yi Addu’ar Saratu ta koma gidan Birgedier yana bukatar abin hannunshi da ya rage basu kenan, wanda shi ba don haka yake kaunarshi ba.

Ya rungumeshi a sanda yake maraya; ba Uwa ba Uba balle dangi, ya zame masa komai nasa a lokacin shi bai taba haihuwa ba, ya wahala ainun wajen daukar nauyin karatunsa. Ya shiga kwanan kurkuku yafi a kirga akan bashi, don Bello ya zama soja, ya sha zagi gun mutanen kauyensu kan ya daurewa dan Wansa gindin zama dan fashi da makami, a lokacin kai bai waye da ilmin zamani ba, to akan me a lokacin bai ki shi ba sai yanzu don ya saki kanwarsa kan ta ci mai mutunci?

Wane irin tallafi da girmamawa ne bai yi masa ba da ya soma daukar albashinsa na farko a soja, tun kafin a haifi wata aba Saratu? Ba zai ki Bello ba cikin kowanne hali, dukkansu kuma bai ga laifin kowanne ba.

Ya san halin Saratu sarai, raina na gaba da ita balle mijin ta ba halinta bane sam tabbas akwai dalilnta na yin hakan, duk kuma dan-adam yana tare da ajizanci, sannan shi aure rai ne da shi, duk ranar da Allah ya kawo karshen sa zai mutu, ana so ko ba’a so.

Hakannan hakuri da wahalar da suka sha ita da diyarta lokacin da yake kulle, sun cancanci mafificiyar kauna daga gareshi ba wulakanci ba. Dole watsar dasu din da yayi yayi mata zafi. Ya san in aka kawota bango kamar mara tunani take.

Ita ko Goggon tunanin ta sabanin na Baffan ne, cewa take so-so-ne, amma son kai yafi. Da yardan Allah sai Daddy yayi nadamar wulakancin da yayi wa diyarta lokacinne ita kuma zata nuna mishi Nairarshi bata da amfani agaresu.

Ta fannin ita Saratun kullum tunaninta na bisa halin da ta baro Intisar a ciki ne. Ta tabbata Allah ne kadai zai ceceta a hannun Hajiya. A duk sanda tayi rin wannan tunanin ta soma kuka kenan har Allah ya gajishsheta.

Sau da dama ta kan yi tunanin kawai taje ta dauko ta shine mafi a’ala amma tunanin barazanar Makarfin da gudun abinda hakan zai haifar, na tonon abin tausayin da ke rufe daga Daddy ko Hajiya game da Intisar din shine ke tsorata ta.

A watan Najib yaje Makarfi, sun jima suna hira da Antin iyakar kokarinsa yayi wurin boye mata zahirin halinda ‘yar ta ke ciki, yace ne kawai tana nan lafiya koda yake shi ba zaman gidan yake ba yana Enugu.

Wannan ya dan kwantar mata da hankali don lafiyar ta tafi ji ba damuwarta ba. Ta tabbata dole ne zata kasance cikin damuwa kamar koma fiye da ita. Amman komi mai wucewa ne da yardan Allah.

Bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin Intissar don haka ta dage da Addu’ar Allah ya kawo masu mafita cikin al’amuransu.

A watanninta na biyar da zaman Makarfi, ta haifi sankaceciyar diyarta a safiyar wata litinin. Yarinyar bata debo kamannin kowa ba sai na Faisal. Kamar su daya da faisal a komi. An aikawa Daddy a ranar ba yabo ba fallasa yayi hidima dai-dai gwargwado don Baffa kadai amma ba wai don ya damu ba. Da aka tambayeshi sunan jaririya sai yace su sanya duk wanda yayi masu mana?

A nan ne ran Baffa ya baci yace a sawa yarinya suna Fatima � Zahra. Su yasir duk sun baro Enugu sunzo sunga kanwarsu dukkansu sai kururuta tsabar kamanninta da Faisal ne babu kuma wanda ya leka Abuja a cikinsu har suka koma.

Anti Saratu kanji haushin Goggonta kan yadda taki hutar da kanta ta zauna wuri daya ta dangana da kaddarar rabuwarta da Daddy. Ita a yanzu ma chairman na Makarfi ke son aurenta tun bayan aifuwarta.

A ranar wata alhamis Goggo da aminiyarta Inna Jami suka dawo yawonsu goshin mangariba kafafun su futu-futu da kura duk sai suka bata dariya. Jami tace

“Au, dariya ma kike mana Saratu don muna nema maki ‘yancinki da aka bi aka bibbinne?

Ni bani ruwa inyi alwallah inyi Sallah ki ji labari. Ai dama aka ce mai nema yana tare da samu, in Allah ya yarda nanda sabon wata mai kamawa kina dakin mijinki, kaikayi kuma koma kan mashekiya zamuyi�.

Saratu tayi tsaki, ta mike ta ciccika masu butoci da ruwa a randa a lokacin zarah keta tsala ihu amma ko waiwayon inda take batayi ba. Jami ta dauketa tana cillawa tana cafewa ta ce

“yi shiru ‘yar ikon Allah, daga wannan watan kin bar zafin kauye In sha-Allahu don nasan shi ke damunki sai Habuja, ke da kauyen Makarfi sai ko gaisuwar Sallah�.

Goggo Jummai tayi dariya ta ce� ai gobe har ita zamu tafin ko? “Jami tace “kwarai kuwa, don gara a soma yi mata rigakafi itama, baki ji Malam na Kafanchar yace itama an maida ta kamar mijiya a idon Mahaifin ba?

Tunda aka haifeta kin ji yace a bashi ita ya gani? Ai gobe Saratu da kin ki da kin so kafar mu kafarki bukkar Mallam Sidi Fari�.

Ita kam jinsu kawai take a ranta ko cewa take ko Sidi Baki ne ba inda zata. Haka kawai don B-Bello shine autan maza?

Itama bakikkirin din take ganinshi babu kuma koda birbishin son sake zama dashi ko kankani a kalbinta, zumunci ma don ya zama dole ne.

Har sun kwanta da doddare Goggo ta kasa hakuri ta kirayi sunanta a hankali tace “Saratu, duk fa hakilon nan da muke yi don ke muke yinsa da farin-cikin ki ba don wani abu daban ba.

Amma na lura ke haushin mu ma kike ji bakya godewa. Dazu ina ji Jami na ce miki gobe ki shirya mu tafi Kafanchan kin yi shiru baki amsa ba har da bin ta da tsaki. Shin ko yanzu ba kya son mijin ki ne?�

Aunty Saratu ta gyara kwanciyar Bebinta dake barci tana fidda numfashi sannu a hankali cikin koshin lafiya. Tabbas tambayar Goggo itace amsarta. Ko a lahira bata fatan su hadu da Birgedier yanzu (kaji sharrin kishiya).

Ta muskuta cikin tsananin bacin ran tono ma mutun abin bakin-cikin da ya manta dashi tace “Goggo ni fa tunda na bar gidan ban kara tuna wani Bello da sunan so ba, sai ko Yaya na Uban ‘ya ta. Yadda kika san bakin kumurci haka nake ganin sa ko muryarsa bana son ji wallahi.

Wannan ‘yar ma kan dole nake shayar da ita, amma duk sanda na tuna wai kanwar su Aminu ce kamar in shake shegiya wallahi�.

Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji tace “Ba zan musa miki ba Saratu don tabbas kema tsafin ya ci ki, amma a kalla gobe ki bimu addu’o’I ne Malam Sidi zai baki na neman zabin Allah ba wai wani abu ba�.
Chapter 52 · 0% Book details