← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 90

Sashe 5

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari autan su Khalil ne ya yi ta yi wa ‘yan uwan buge-bugen waya yana sanar da su dawowar ya Ameenun da matar shi Ihsan, hatta Faisal da ke Birmingham yana karatu a lokacin ya ji dawowar Ya Aminu. Yasir ya ce suna gaishe shi, amma suna masu tsananin fushi da shi su duka har sai sun ganshi a garuruwan da suke shi da Ihsan tukunna su huce. Al’ameen ya amsa zai je wa kowannensu shi da ba bakon zafi ba har ya isa ya ja masu rai?

Ga dan zafi Najib kuwa ko sannu bai samu ba, don har yanzu yana kullace da Aminun, wannan ta wuce.

Karfe bakwai na safiyar Litinin ya zuba koriyar shadda Edcellencior da aka yi wa dinkin Mohamed Abacha, kan shi ba hula, don bai da ita. Wannan shaddar ma ta jikin shi Furkan ya ba shi, don ba zai so Baffan su ya soma ganin sa cikin suit ba. Kasancewar ya dade rabonsa da irin wannan dressing sai ya fito a wata kala daban.

Hakika kalar Maman shi ‘yar uslin garin Maiduguri, cikin kabilar nan Shuwa ne ya debo kamanni da zallar kyau, ta wani bangaren kuma sai ya fito a tsantsar Bahaushen sa sak mahaifin shi Bello Makarfi. Ya shirya ma fita karfe bakwai da rabi ne don yana da sabgogi da yawa da yake son gabatarwa a ranar in Allah ya ara mai rai da lafiya.

Bayan zuwa wajen Baffansa da Aunty Saratu da ke garin Makarfi yana son neman filayen da zai yi ginunnuka ga takardun hijira da zai aika Miami ta komfuta da neman izininnikan medical branches da yake son assasawa anan kasar mu Nijeriya wanda zai kasance reshe daga meritime da ke karkashin kulawar Dr. Rehab da zai nema daga ‘Federal Ministry of Health�, wato hukumar lafiya ta kasa. Yana son assasa asibitoci anan Abuja, Kaduna da kuma kauyen su

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one

*@Takori*

Page3ï¸âƒ£

Makarfi

Hakan nan yana son ya je ya gaida surukan shi a Garki, ya yi masu wata kyauta mai daraja ba don komai ba sai don neman albarka, duk da hararar gefen idon da ya ga ana yi masa duk da cewa he did not care, wai sai ya shiga yi wa kansa dariya, da ya ce zai kai wa iyayen Ihsan abu don neman albarka. To albarkar Kiristin zai nema?

Ya yi saurin cewa a’a na uban da yake Musulmi, kuma mutumin kirki a bakin kowa.

Akwai kuma muhimman kayayyakin su da suka taho da su musamman motocin su zai je port da airport ya fitar da su. Ya san idan ya fita yau sai Allah, don haka akwai bukatar ya yi kyakkyawan break-fast da abinci mai nauyi don shi ba ya jure yunwa sam.

Kafarsa ko takalmi babu yana tafe yana magana da Ihsan din shi tana gaya masa yadda ta yi missing din shi ne a daren jiya, tana kuma tambayarsa ko how much did he missed her? Sai ya kada harshe ya ce, “Wai ke Ihsan kin yi murna da ganin Ann, da ki ka dame ni da mu zo ki gani? Ni ko sai na ga you are not happy as I am, don ni jiya har sha biyun dare ina tare da Hajiyana, muna hirar da for so long ba mu samu mun yi ba. Ina na tuna da wata soyayyar ki can?�

Ta ce, “Ya yi kyau, ai ni dama kullum mantawa nake ni ke son Al’ameen, ni na damu da shi, ni kadai ke kaunar shi, amma duk kokarina bana burge shi, so ka yi hakuri.�

Da haka ta katse layin, ko ba ta fada ba ya san ranta ya baci, shi ko sai ya yi murmushi ya ce, “Allah Sarki, nima ina son ki, damu ne ba na so, ko karyawa ban yi ba.� Sai ya bai wa kansa dariya a karo na biyu, lallai kam duk girman mutum a gaban iyayensa ashe yaro yake komawa, ko kuma don ya dade baya tare da su ne? Oho. Yadda kyawawan fararen kafafunsa ke mannewa bisa marbles ma kadai abin sha’awa ne, to haka his gait, his geniusness and his coolness ke da daukar hankali.

Wata yarinya ce fara, irin farin nan da ke da jaja-jaja wanda Bahaushen tsantsa baya mallakarsa, doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Seirraleone. Fuskar ta oval shape, mai wadace da kayataccen dogon karan hanci, tamkar ansa ruler, an ja shi an daidaita shi a tsakanin idanun ta. Idanuwan ta kadai sun isa su sa mutum ya so ta ko da ya ki Allah (Almond-Eyes). Girar idonta gazar-gazar kuma kakkaura siririya, bakinta dan surut jazur da shi mai matukar daukar hankali, yatsun ta na kafa da hannu zara-zara masu matukar taushi da kyan tsari, tamkar ba na ‘yar aiki ba.

Sumar kanta yalwatacciya ta Fulanin usli nannade take kamar gammo duk ta wani irin mummurde alamun rabon da a taje ta har an manta, sanye take cikin wata zulumbuwar riga ja mara ado wadda a kullum suke cikin dattin kitchen, duk inda kyakkyawar mace mai fasali take to wannan yarinya ta isa har ta wuce. A ransa ya ce, ‘Kai Allah ya yi halitta tamkar Hurul’eeni???�

Ya yi sallama har sau uku, amma yarinyar a zuci ta amsa ko dagowa ba ta yi ba balle ta ga waye mai sallamar, illa zuciyar ta cike da jin dadin yau an yi mata sallama sabanin da da duka ko zagi ke mata sallama.

Hakan nan wannan wata murya ce da ake kira ‘husky� da ba duk maza Allah ya mallakawa ba sai ko wadanda suka amsa sunansu ba ‘muna-maza� ba. Murya ce mai shigen ta Ya Faisal, sai dai wannan akwai alamun sense of humour wato raha tamkar ta Daddy, ba ta raba daya biyun Yasir ko Nasir ne oho, ita yanzu ko a lahira ta ga ‘ya’yan Hajiya ba ta fatan Allah ya ba ta ikon kula su.

To Al’ameen sai ya dauka ko ba ta ji ne kwata-kwata, ya kai hannu ya kwankwasa lockers din kichin din da karfi, ta dago a dan razane. Ta so ganin mamallakin wannan murya mai sanyawa mace kasala ba tare da ta ga mamallakinta ba, ta so ganin mamallakin wannan ni’imtaccen kamshi da ba ta taba ji ba a rayuwarta, sai suka yi ido biyu da mutumin da ba ta sani ba ba ta taba gani ba.

Babu abinda ya firgita ta kamar kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen wanda hakan ya janyo mata gigicewa tare da mance abinda take yi, wani matsanancin tsoronsa ne ya kama ta, tsammani take Hajiya ce ta turo shi ya sa mata shocking din da ta ce za ta sanya mata in ba ta kammalawa bakonta karin kumallo da wuri ba a safiyar yau.

Tuni ta karasa rudewa ta rikirkice ta soma matso kwallah ta ci gaba da firar jibgin dankalin turawan da ke gabanta fiye da bokiti guda tana ferewa da dukkan karfinta da iyakacin saurin da za ta iya sai shap! Ta zaftare tsokar dan yatsan ta jini ya soma fita a guje, amma ba ta kula ba sam, aikin ta ta dage da yi. Aminu ya kama kai, ya karaso gabanta ya rusuna ya kama hannun ta mai rike da wukar ya ce, ‘Ke ba kya ganin kin yanke ne?�

Maimakon ta bari, sai ma ta kara daukar dankalin da ya subuce a lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannunta daga hannunsa ya ce, “Ki yi hakuri in tsayar miki da jinin?�

Ta dago a hankali ta dube shi, to shi ma din kallon ta yake, suka yi wa juna kuri da ido; wani chemistry ya shiga aiki cikin ‘yan mintocin da ba su gaza uku ba, ita ta fara kawar da kai, ya mike ya fita da sauri yayin da ita kuma ta yi jigum ta na duban yatsanta da ke ta bulbular da jini ta ce a ranta wannan wane irin mutum ne he is so caring.

Ya dawo rike da dan karamin First-aid bod cikin nutsuwa ya wanke mata yatsan da ruwan hydrogen tas babu ko kwayar jini, ya shafa iodine don azabar shi sai tasa kuka, yasa plasta karama ya nade yatsan, ya tsani ya ga mace tana kuka. Ya sarke yatsun su cikin na juna ya ce cikin tattausar muryar shi.

‘Ki yi hakuri, duk ni na jawo miki, don haka tafi daki, ni zan karasa miki.�

Ta share hawayen ta da gefen rigar ta iodine na mata radadi da zugi, amma tausassan yatsun Al’ameen sun tsare komai. Da ya ga ta yi shiru da kukan da take sai ya zare hannunsa ya shiga aikin dankalin nan tukuru cikin dan lokaci ya gama ya zuba a katoton fraying fan da ke tafasar da mai ya soye shi tas, haka ya shiga hada kowanne kwai da dan uwansa ji ka ke kas! Sai ya juye cikin babbar silver nan da nan ya soye shi fes. Tuni ta kammala ragowar kananan aiyukan kamar su zuba ruwan zafi a filas da jera komai bisa faranti.

Ya dauki plate mai tsabta, ya debi abinda zai yi masa ya dau cokali fork ya aza bisa ya juya ya fita, har ya kai bakin kofa sai ya dawo ya dube ta ya ce“Ke daga yau in kin gan ni kar ki sake firgita, don bana satar yara, hakan nan al’adana ne shiga kicin, don haka in ki ka sake yankewa ba ruwana.�

Bai fita ba sai da ya bi Hajiya sassan ta suka gaisa, Daddyn bai fito ba don haka ya zauna zaman jiransa a falon gidan har ya gama. Shi ya sauke Daddyn a ofis yau kana ya wuce ya kama harkokin gabansa zuciyarsa cike fal da tausayin ‘yar aikin Hajiya, ya yi mamakin yadda kyakkyawar yarinya kamar ta da daga gani ta fito ne daga gidan hutu ke aikin wahala irin wannan.

Idanuwanta kadai sun ishi kowanne irin namiji yanga da ita a matsayin mata. Ya alkawartawa ransa matsar ta ya ji dalilinta na wannan aikin wahalar duk da ya lura yarinyar ba ta son magana da kowa to shi dole ta yi masa.
Chapter 5 · 0% Book details