← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 90

Sashe 20

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daren Hajiya Saratu kwana ta yi rikon Allah ya raya mata bebin ta, ya kare ta sharrin dukkan abin ki, ya rufe bakin Hajiya Nafi kada ta fadawa ‘ya’yanta bebin ‘yar tsintuwa ce.

Da sati ya zagayo raguna har biyu Brigadier ya kayar a kofar gidan si ya radawa yarinya suna Saratu, don kawai ya nuna mata godiyar shi kan karamcin da ta yimasa da kuma matsayinta a zuciyar shi ya zarce na kowa. Domin shi kan son bebin nan yake bilhakki, son da yake jin baya yi wa wani cikin ‘ya’yan shi bayan Al-Ameen.

Unguwar Gwamna Road irin unguwar nan ce ta masu fadi ajin garin Kaduna da babu ruwan kowa da rayuwar kowa, balle har tsegumi ya bullo, don haka Brigadier ya yi wa yaran shi kawai Walima wadda ya hada da birthday din Khalil na 3 years.

Da alama jinin Faisal da babyn Saratu zai fi haduwa, don kacokan Faisal ya tare a sashin Antin yana taya ta rainion babyn da yake kira Intisar. Shi dai haka nan yake son sunan, tuni duk yaran suka kama Intisar, Intisar. Antin kadai ke kiran ta da Saratun ta sak.

Tun Hajiyar su na duka da zagi kan ya fita hanyar su har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido ta yi watsi da al’amarin su kamar ba ta san Allah ya yi ruwan tsirar su cikin gidan ba ma, ta rungumi kasuwancin ta kadai. Kuma dama yanayin sashin su sai mutum ya yi wata guda bai ga dan uwan sa ba in har ba shi ne ya neme shi ba (tamkar tafiya ce ta layi guda).

Babbansu Al’ameen dama tun da fari bai kaunar Anti Amarya, a dalilin yana ganin a kan me Daddyn baya shawara da mahaifiyar shi akan komai na gidan dama rayuwar shi gaba daya sai ita da ta zo daga baya?

Don haka ko da ya dawo ya tadda haihuwar Anti amarya bakin ciki bai sai an fada ba. Aminu kawai masifar jin kai da takama sabanin su Faisal da suke friendly ga kowa, ga miskilanci kamar tsohon kuturu, sai dai fa natural brain wannan shi ne nick name din shi a makaranta, Aminu yaro ne mai kwakwalwa a karatun lissafi tun yana karami.

Sun dauki Intisar sun kai Makarfi sun warwarewa Baffan su da ya rage masu a duniya da Goggo Jummai mahaifiyar Anti Saratu komai. Abin da suka ce shi ne Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta kuma mai amfani ga al’umma.

Baffa ne dai ya ce mai ya sa bai tuntubi hukuma ba tun da fari? Ya manta Bellon kansa hukuma ne tunda kuwa babban kusa ne a soja, sai ya ce kawai shi dai hakan nan Allah ya daura mai kaunar Saratu har bai jin dadai duniya zai taba rabuwa da ita.

Malam ya ce,

“hakika Ubangiji Yana jin kan bayin sa masu jin kai. Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta, ta kuma zamo ‘ya abin alfahari a gare su�, yadda kuma abin yake sirri a tsakanin su haka suma za su rike.

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one

*@Takori*

Page1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£

Cikin ‘ya’yan Hajiya Nafi kaf, Aminu ne ya debo halin ta na keta da kekasashshiyar zuciya. Da ta lura shi ne kadai mai taya ta kishin su Saratu, mai kuma son duk abin da take so, duk yaranta sun tare a gindin Anti Saratu sai ta shiga zuga shi ya ki Saratu karama, ya kuma dinga gana mata azaba a boye. Dama kuma duk cikin yaran gidan kaf ba maras kirki irin Aminu, amma Daddyn bai ganewa, wannan ya samo asali ne da kasancewar Aminu lumbu-lumbu wutar kaikai, sunkuru macijin sari ka noke, a fuska Musa a zuci Fir’auna, don a fuska mutumin kirki ne.

Daddy na son Aminu ne saboda hazakar sa wanda kullum cikin dauko kyaututtuka yake a makaranta, bai taba yin na biyu ba a gaba dayan shekarun sa na sakandire. Hakan nan Aminu na da shiga ran iyaye da sauran jama’ar duniya ma baki daya. Shi kan sa ya san shi kyakkyawa ne, wannan na sa shi kara homa cikin tsararrakin shi duk da haka yana masifar gudun bacin ran Daddynsu.

Shekarun Intisar uku cif, amma hikima da basirarta sun fi karfin shekarun ta, ko kadan ba ta da wayo sai dauke abinda duk aka koyar da ita nan take, don haka Aunty Saratu ta tuntubi Daddy da shawarar ya dace a sanya ta ajin rainon yara.

A lokacin an yi posting din Daddyn jihar Lagos dukkan su sun tare a sabon gidan su da ke Victoria Island, wani azababben gini da Daddyn ya yi shekaru yana zubawa kamar ba ba za a mutu ba. Faisal ne ya kawo shawarar a kai baby Intisar Links International School, makarantar rainon yara da wata Baturiya mutuniyar Russia ta zo ta bude a Lagos. Satin baby kwata-kwata hudu a Links shugabar makarantar ta zo ta samu Daddy a ofis, bayan sun gaisa ta ce ita shugabar makarantar da yarinyar shi Saratu ke karatu ne, ya ce, ‘O.k, Links ko?�

Amma can a karkashin zuciyar shi cike yake da tunanin ko laifin me? Saratu ‘yar shekaru uku da doriya kacal a duniya ta yi? Matar ta ce,

“Wato abin da ya kawo ni shi ne in shawarce ka, gaskiya basira irin ta yarinyar ku ya wuce nursery, don haka na kawo ma shawarar in da hali kawai a kai ta (primary 2) a Turkish da aka bude kwanan nan, sai dai makarantar akwai tsada, amma I’m sure, Saratu za ta sami sound background (tushe na kyakkyawan ilimi) a gaba.�

A nan ne Daddyn ya ja numfashi ya kuma saki murmushin jin dadi,

“Ku kai Saratu duk makarantar da ku ke ganin ta dace da ita. Kada ku dama da kudi, daga naira daya har million zan biya, ni dai burina kasar mu ta amfana da ilimin ‘ya’yana.�

Baby Intisar na aji uku a Turkish, amma fasaharta da kwazon ta kan ba malamanta tsoro. Ba ta da magana ko kadan sai tsabar karatu a cikin kanta tamkar wadda ake wankewa kwakwalwa da ruwan zam-zam. Kyawun ta kadai ya isa yasa mutum ya so ko da ya ki Allah. Sai kuma aka yi sa’a ya hadu da ‘yar gayun uwa; Aunty Saratu kullum cikin wanki da gyaran sumar Intisar take da mayuka masu kyau da tsada, don haka ne kullum za ka ga kan yarinyar yana wani sheki da kamshi, baki sidik kuma a kanannade (curl). Fara ce sol, siraran labban ta jazur da su, hancin ta matsakaici tamkar ansa ruler an ja shi an daidai ta shi a tsakanin idanunta.

Wasu irin lumsassun idanu kullum kamar tana jin barci, fasalin su na ‘ya’yan itacen Almond (Almond eyes). Akwai tawwadar Allah a gefen hancinta na dama. Shape din fuskar ta oval (Tamkar zanen kwai), akwai gazar-gazar gashin gira, yalwatacciyar suma ta Fulanin usli, ga kyawawan yatsun kafa da hannu Tubarkallah.

A kullum shakuwa mai tsanani na kra shiga tsakanin ta da yaran gidan musamman Faisal da Khalil da yake kusan tsaran ta.

Rannan Antin na ofis aka sanar da ita tana da baki kafin ta yi masu izinin shigowa kasancewar ta nemi (transfer) zuwa nan Lagos, suka gaisa, sai suka ce su Malaman su Saratu ne, sun zo ne kurum su ga Mamar ta, su gaya mata Allah yai mata baiwa da ya bata ‘ya kamar Saratu.

Aunty Saratu sai ta yi dariya, wannan complain (korafi) na jama’a ba yau ta fara jin sa ba, tun ranar da ta soma fita da Saratu mutane suka gan ta. Ta tambayi sunan su, dayan ya ce suna shi Mr. Victor shi ke koyar da Saratu lissafi. Dayar Mrs. Risikat malamar Turancin su Saratu ce. Tohaka ko kanti suka shiga sai an ba baby sweets zuwa biscuits an ce da Anti Saratu ana son ‘yar ta.

Rannan Faisal ya ce, “Anti amarya ba za ki wa baby layar baki irin wanda Hajiyar mu ke mana ba in zamu shiga mutane?�

Maganar Faisal ta ba ta tsoro. Don haka a washegari Makarfi suka yi sallar Azahar ta kwashe abinda Faisal ya ce ta gayawa Baffa. Baffan ya ce, Faisal ya yi tunani, kuma tsari tun yanzu zai soma yi wa Saratu.

A wannan shekarar ne Aminu ya kammala karatun shi na sakandire a FGC Abuja, with flying colours (da sakamako mai ban mamaki). Aminu ya sha albarka a wurin Daddy, gata kuma ya karu sai abin da ya ga dama yake yi a gidan.

A falon Hajiya ake hirar wai budurwar Ya Aminun, Bose ‘yar yarbawa Aminun ya kai mata katunan happy-Xmas masu kyau. Yasir ke baiwa Hajiyar labari, ta fusata ta ce, “Kai ina ka san Bosen?�

Ya sosa keya yana dariya ya ce,

“Ki rufa min asiri Hajiya, Allah in Daddy ya ji harbe ni zai yi, kin san Allah kanwar abokina David ne, in suka zo masa visiting sai ta yi ta kawon kaya wai tana sona, ‘yar wannan General Benga Delsun abokin Daddy da suka shirya coup (juyi mulki), a shekarar baya suka fasa?�

Hajiya ta kwabe baki ta ce,

“Kai nan har ka isa yin budurwa dan nan, oh, duniya ina za ki da mu?�

Ya yi murmushin da ke lotsa gefen bakin shi na hagu (beauty point), ya kuma lotsa tsakiyar habar shi (cleave).

“Kai Hajiya, ita har ta isa in yi budurwa da ita? Ba ki gan ta ba fa baka mummuna, ga warin Yarbawa, romantic eyes din ta kawai nake so.�

Hajiya ta yi salati yayin da gaba daya yaran suka kwashe da dariya, ta ce,

“Miko min wayar can Faruk ka gani, in zane dan banzan nan.�

Ya mike yana murmushi ya ce, ‘Fada kawai ki ke Hajiya ta, amma na san ba za ki iya ba, ni din Al’ameen dan Hajiyarsa?�

Faisal ne ya shigo rike da hannun kanwarsa Intisar da ta ci ado har ta gaji, sanye take da ruwan bular riga da siket din jeans, gashin kanta an yi kananun kalba an makalkale su da kyawawan ribbons kala-kala. Faisal ya ce,

“Ya Aminu ka je in ji Daddy yana falon Anti Amarya.�
Chapter 20 · 0% Book details