← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 90

Sashe 79

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin tagwayen data haifa duk maza suna da shekaru biyu da haihuwa sai Zarah da ke da shekaru hudu, wadda daga yaye dai ta za ma yar su kwata kwata, don daga Daddy har Aunty Saratu babu wanda ya kara magana a kan zaman yarinyar tare dasu.

Tsarin rayawar gidan dole ya baka shaawa, babu hayaniya sam-sam, rayuwa ce kawai suke kamar a turai. Lokaci-lokaci suna zuwa Shanono duk da cewa dangin sun kare. Matan Hakimi tun bayan rasuwar sa duk sun kama gabansu, manyan yayansa maza kuwa duk Bashir ya dauki nauyin karatun su a manyan jamio’in mu, matan duk shi ya aurar da su tare da basu jari mai tsoka domin dogaro da kai. Haka duk matsalolinsu yana kokari a kai domin tabbatar da cikin su babu mai kukan rashi.

Ba tare da yin shawara da kowa ba Hajiyar su Faisal ta shiga yi masu cuku cuka ita da Faisal, Najib da Hidayah domin tafiya Al-kahira, saida ta kammala tsaf aka sanya masu date din tashi kana ta samu Daddy ranar girkin ta a wani dare, ta sadda kai cikin matsananciyar kunya ta ce,

“Babansu Khaleel, ina neman izninku zuwa wajen Intisar, ina matukar kwadayin afuwarta da yafiyar ta gare ni, har yau ji nake ban sauke wani nannauyan dutse daga kaina ba. Idan ka amince zan nemi rakiyar su Najib ko albarkacinsu ta dube ni ta yafe mani.�

Tasa habar zaninta ta share idonta ta fyace majina ta ce,

“Idan yarinyar nan bata yafe mun ba, bana jin Alameen ma zai taba yafe mini. Haka ubangiji na ma ba zai yafe mun ba, iznin ka kawai nake nema domin nagama komi, jibi ne zamu tashi.�

Ya daga ido ya dube ta kawai ya ce, “Me yasa bakya shawara kafin gabatar da alamuran ki? Sai in ce kin yi asarar kudin ki domin kuwa jibin ne zata dawo hutun karshen shekara.�

Ji ta yi kamar anyi mata bushara da Aljannah. Ta ce,

“Ba komi ai, Allah ya kawo su lafiya.�

A Egypt
Saratu da yar uwar ta Hunainah, cikin wani boutikue dake cikin jerin kantunan Shaam-El-Sheikh da ke cikin birnin Al-Kahirah, dukkansu suna sanye da riga da skirt iri daya samfurin Dolce&Gabbana, sun kuma daura after dress bisa dressing din nasu kala daban-daban, na Intisar grey ne wato ruwan toka-toka yayin da ta Hunainah ta kasance baka sidik. Hunainar rike da kwando da suka cika taf da kayan shafa, (shopping) suke domin dawowa gida hutu a washegarin gobe in Allah ya kai mu.

Ga dukkan alamu ita Hunainan cike take da farin-cikin dawowa hutun ko ba komi ta dade rabon ta da gida fiye da yadda ta saba yayin da a daya bangaren Intissar gata nan ne dai kawai. Kwata-kwata ta rasa me yasa bata farin ciki da wannan hutun duk da cewa kuwa rabon ta da gida shekaru biyu kenan cif.

Hakanan dai take ji a ranta wani bakon alamari na shirin faruwa da ita a wannan tafiyar kamar yadda yake a aladarta, komi zai faru da ita mai dadi ne ko akasi takan ji bacin rai ne wanda ke kasancewa zane baro-baro a kyakkyawar fuskarta, duk rabin hirar da Hunainan ke mata kan tsohon cikin da Hidayah ke tare da shi, da bidirin da zaa sha wajen haife shi kasancewar Hidayar mai rakin tsiya ko kadan hankalin ta baya tare da ita.

Gane hakan da Hunainan tayi sai itama ta ja bakinta ta tsuke, har suka koma makaranta basu kara ce da juna komi ba.

Karfe tare na safe jirgin Egypt-Air ya dire su a birnin Kano. Kai da ganin su kaga yayan hutu na garari kuma yammata na kasaita, wadanda gabansu da bayansu, gata da hutu kadai ke magana. Zai yi wuya ka yarda haifaffun kasar Nigeria ne, sun fi kama da santala-santalan matan Mouritania ko kuma irin half-cast din nan da suka tashi a kasar sanyi. Akwai wata nutsuwa ta musamman da zuzzurfan ilmi ya kara ma fuskokin su. To haka makallalen saurayin da Hunainah ta yi tun a cikin jirgi ke biye dasu har zuwa reception inda duk suka a je kafa nan yake mayar da tasa.

Ya kare ganin basu da niyyar kulawa ya sha gabansu, kyakkyawar fuskarshi dauke da kayataccen murmushi ya dubi Intisar ya ce Assalamu Alaikum Yayata, zuciya ce ta ga wani koren fure tana so shine take ta faman bibiyar sa, kada iska ta dauke shi ko kuma ya bace mata tana ji tana gani.

Suna na Hashimu Ingawa, ki taimaka kar ki bari furen nen ya bace mani, don Allah? Yana magana ne cikin accent na Katsina, ya rausayar da kai gefan da Hunainah ta ke, ta cika ta yi fan har tana neman fashewa. Idan da abinda ta tsana a duniya to wani namiji ya ce yana sonta, duk dangantakar dake tsakaninsu daga ranar zata wargazata da rashin mutuncin da ko inuwar ta ya gain sai ya sauya hanya.

Ta tura akwatin ta fuuuu! Tayi gaba kaman guguwa. Intisar ta yi murmishi, haka kawai ta ji gayen ya burge ta, tana son mutum mai fallasa asirin zuciyar sa da fidda zahirin kaunarsa gaban kowa ba tare da shayi ko haufin komi ba tamkar Alameen din ta.

Ta dube shi tsaf yake baya da makusa, da ganin shi ka ga wanda ilmi da naira suka ratsa sai dai baki ne, amma bakin sa mai kyau ne tunda kuwa ya hadu da hutu da gogewa. Sanye yake cikin makubar suit da ratsin fari sol ya daura jibgegiyar rigar sanyi fara sol wadda tsawon ta yake har guiwar sa, ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihun rigar amma hakan bai boye hasken agogon diamond da ke walkiya cikin lafiyayyar fatar hannun shi ba.

Ta ce mun gode Hashim, amma in gaya maka gaskiya wannan furen da kyar zaka same shi ya fiddo ido abin tausayi duk sai ya bata dariya, da gani maabocin raha ne shima kaman Alameen ya ce is she married (maana tana da aure?) ta girgiza kai tana murmushi tace uhm-uhm, tukunna dai, karewa ma dai wannan furen naka tsoron maza yake, da kyar zata tsaya ta saurare ka.

Yayi wata ajiyar zuciya mai karfi duk sai ya kara burgeta, da gani ba kankanin so ya kamu da shi a lokaci daya ba. Ya ce ni dai Yayata, pls help me, ni na san yadda zan yi, kuma zaki yi mamaki Allah, bata samu Mr Right dinta bane yet, amma ni tunda na ganta a Cairo nasan we are meant for each other kuma naga matar aure, shin zaki iya ba Bakatsine auren yar uwar ki?

Ta yi murmushi mai sauti har kyawawan hakoranta suka bayyana tace why not? Katsinawa sun dade suna burge ni. Don an ce akwai su da rikon aure da muhimmanci fiye da Kadawa da Kanawa. In har ya cancanci in bashi kuma tana son sa everything is possible wato komi mai yuwuwa ne.

Ta fiddo katin Babansu mai dauke da adires na gida ta kuma fiddo biro cikin jikar ta ta rubuta mai nambar Hunainah a bayan katin, yayi mata godiya sosai, ya ce har abada ba zan mance da wannan taimakon da kika yi mun ba Yayar mu, na gode. Da haka suka rabu, ta doshi Hanainah da ke ta faman cikka, kiris ta ke jira ta fashe.

Bata bi ta kanta ba ta fiddo waya ta cire layin ta na Cairo ta sanya MTN tayi lodin recharge da ta saya a gefe tana kiran Babansu, cikin minti goma sha biyar sai ga mota ya turo masu da direba, ya kwasheu zuwa Lamido Crescent.

A cikin motar Hunainah ta kara cika ganin Mamar da Baban ba wanda yazo taryon su ga bakin-cikin da Saratu ta kunsa mata kuma ta ki bata hakuri sai hawaye sharrr! Intisar tayi kokarin maida dariyar ta don kar ta fito ta rufe ta da duka.

Sai da suka shiga gidan ta sunkuya ta kwashi dariyar ta mai isarta tana bawa Maman labarin yadda aka yi da sabon saurayin Hunainah, ita ko tunda ta watsar da trolly din ta tayi sama bata kara saukowa ba, saida matsiyaciyar yunwa ta hullo ta.

Sun hadu a dining karfe hudu na yamma suna cin abinci tare da Baban su, yan biyu a cinyar Intisar hagu da dama tana sanya masu friso cream a baki da dan kankanin cokali yayinda Zarah ke zaune bisa tata kujerar kusa da ta Babanta Bashir tana cin vicorian sandwitch suna bashi labarin makaranta da yanayin karatun su, ya ce nikam ban so kika dauki surgery ba, naso ne ki dauki gynaecology domin muna da karancin likitocin mata kuma mata yan uwan su a nan Arewa tace lah Daddy, ai Hidayah ce tace zata dauka bayan ta haihu, sai na ga da mu taru duk a abu guda, ai gara a rarraba kafa ya ce wannan shirmammiyar ce zata koma wani karatu, ba ki ji ba tun yaushe take wakar zata koman kin kara jin sun tayar da zancen, ki daina sata a layin karatu bar ta dai da mijin da giringidishin ta, amma ba wani karatu da zata koma balle idan ta soma zubo yaya. Gaba daya aka sa dariya.

Yace Daddynki yace ki yi zaman ki sai ya neme ki, kuma kiyi shirin tarbar wasu muhimman baki gobe da zasu zo specially don ke ta yi murmushi ta ce,

Daddy kenan, shi gani yake har yau bana son zama da mama ne bai san alkunya nakewa Aunty na ba ta fada tana kallon mamar cikin ido cikin sigar tsokana.

Da ganin fuskar maman ka san ta ji dadin maganar ta amma sai ta daure fuska ta ce ke bana son rashin mutunci, Hajiya Saratun kike yiwa alkunya?

Don ta kara bata kunya sai ta shagwargwabe fuska ta ce to

“Mama ai so-so ne, amma son kai ya fi ko? Ni ma ina son jin dumin mamana da ta haife ni, don Anti Hajjo tace mun tunda aka sace miki ni baki kara dariya ba, sai ranar da kika gan ni ko Daddy?�

Yayi dariya ya ce, “Kwarai Intisar, in na ce zan baki labarin irin suman da ta…� Hajiya Hadiza ta mike tana harhada tangarayen da suka ci abincin a kufule ta ce,
Chapter 79 · 0% Book details