← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 90

Sashe 82

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kyale su honey, shekara mai zuwa duk haka zasu koma suma, gara ke tare zamu yi nakudar mu mu biyu mu haife kayan mu.�

Hunainah ta ce, “Tab! Allah ya nuna mun wannan rana, wallahi bayan taga zai koma ya na leken ki, ki na wayyo Allah Najib, ba ka ce tare zamu yi nakudar ba, ya zaka tafi ka barni ni daya? Tana yi tana gwada irin rike kwankwason da Hidayar zata yi gaba daya suka sa dariya har ita.�

Najib ya ce, “A bar zancen wasa, ke Intisar bakuwa kika yi tana falo, Maman Hunainah ta ce ku je dukkan ku. Kin ga dan ki ko? Ta sukuyar da kai a hankali ta ce, “Eh, Alameen ya girma fiye da yadda na zace shi, kamannun shi da Baban shi har sun yi yawa.�

Ya yi murmushi ya ce, “Kowa haka ya ke cewa.�

Duk sai suka yi shiru dukkansu, babu shakka kowa Alameen din ya tuna. Najib ya bagarar ya dubi Hidayah yace zani cikin gari honey, take kia of yourself, pls, me kike son in taho miki da shi? Ta yamutsa fuska tace kafafunnan sun matsa mun Najib, ko asibitin zamu koma? Ya ce yana karasowa inda take kwance a gafen Hunainah,

“Aah bari in gani, I can deal with them, messaging din su zan cigaba da yi zasu sace yanzun nan.�

Gaba daya ya manta da su Intisar da ke wajen, ya debi kafafun ya aza a cinyar shi yana matsawa sannu a hankali. Cikin matsananciyar kunya suka zame daya bayan daya suka bar masu dakin zuciyar su cike fal da shaawar su, barin Hunainah da a take ta rinka kissima wai inama ita ce da Hashim din ta, ita kuwa Intisar tunanin ta shine Allah ya bata mai son ta kamar yadda Najib ke son Hidayah, har baya iya jurewa a gaban kowa nunawa yake bashi da abu mafi muhimmanci kamarta.

Ta shiga falon da sallama, amma sai tayi turus, a bakin kofar bata karasa ba. Zuciyar ta na harbawa, kafafuwanta suka sage, jikin ta yayi sanyi; Hajiya Nafi ce, a zaune a falon mahaifiyar ta sai Khaleel da ke shan lemun Ribena. Ta juya da niyyar komawa cikin gigicewa amma muryar da ta ji daga can kofar shigowa ta katse gudun jinni a cikin jikin ta, ta warware tunanin ta kaf ta kasa koda motsa kafar ta balle ta idasa yunkurinta na komawa inda ta fito, muryar Faisal.

Ya ce Intisar! Bata amsa ba, amma ta dakata kuma bata juyo ba, shima bai shigo cikin falon ba, daga can bakin kofa yake maganar kamar baya so, da gani don ta zame masa dole ne amma da ba zai yi ba.

Ba kuma tare da ya kalli sashen da take ba ya ce (cikin murya ta girma da bada umarni).

A matsayin Yayan ki, baa matsayin dan ta ba, ina ganin ya dace ki saurareta. Ba lallai ne ki yarda da abinda zata ce da ke ba, amma a kalla tunda gaba take da ke, ta kuma taso gari-ya-gari domin ki, ta kashe muhimmin lokacin ta tazo gareki, duk da kike kasa da ita, ta zo neman wata alfarma a gareki.

Ashe kenan ta san cewa ke wata aba ce mai daraja da zata nemi wani abu daga gareki. Bai dace ki wulakantata ba tunda Manzon Allah (SAW) ya ce bakon ka annabin ka ne. Kuma ko a lahira wani kan ci albarkacin wani.

Da haka ya juya yayi ficewar sa. Ya bar mata permanent (tabbataccen) kamshinsa na (5,000 Doller perfume) da har a mafarkin ta jinsa take yi. Hawayen suka idasa zubowa bisa kundukukinta.

Cikin dauriya da jarumtaka ta juya ta isa gabanta, ta zube guiwoyinta a kasa hawaye na zuba a idon ta tace Hajiya ina wuni?

Ita kanta Hajiyar kuka take yi, haka bata ji dadin kalaman da Faisal yayi amfani da su wajen yi mata magana ba, tamkar ya goranta mata kaunar da suke mata ne, su da suke nema. Ta kai hannu ta dafa kan yarinyar tana share mata hawaye da hannunta, ta kuma sauko daga kujerar da take zaune ta zube gwiwoyinta a gaban Intisar din kamar yadda ta yi, ta ce,

“Ki yafe min don Allah Saratu, ki yafe ni Saratu, bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen nuna miki dimbin nadamata kan abinda na yi miki. Abinda zan iya cewa kawai shine kiyi hakuri ki yafe min hakika nayi nadama, na yi nadama mara amfani a kan ki Intisar. Kada ki dubi tsakanin ki da yaya na ko abinda suke miki, wannan hakkin ki ne. Ki dubi girman Allah da manzon sa ki yafe mini. Kuskure ne nayi, nasan kuma babu wanda yake sama da shi. Kiyi hakuri da abinda Faisal ya ce da ke, ban san me ye ke damun sa ba.

Hajiya Hadiza ta shigo, tana tura troller kwandon kayan abinci zuwa dining da ke gefe guda a falon ta ce wane irin abu ne haka Hajiya? Don Allah ki koma ki zauna.

Ta ce, “Aah Hadiza, ki bar ni in roki gafarar Intisar kawai, ko kwanta mata ne sai in yi, in ba haka ba hakkin ta ba zai bar ni kwanciyar kabari ba.

Intisar ta kama hannun ta ta maida ta bisa kijerar ta ce shikenan Hajiya, Allah ya yafe mana gaba daya.�

Shiru ta yi tana mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, tana mamakin kaunar da take wa yayanta. Ta na mamakin hakuri da yakanar ta da daukar alamuran duniya da sauki.

Bata zaci ko a mafarkin ta yarinyar zata taba yafe mata ba. Ta tabbata ko don wannan halayyar tata dole kowa ya sota, dole alumma su kaunace ta, dole ta zamo a bar so ga duk wani da muamala ta hadata da shi koda na second guda ne, hakika a yau ta kara tabbatar wa da cewa da a ke ita din yar baiwa ce.

Ita kuwa Intisar ta yi laakari ne da fadar Ubangiji (SWA) mai cewa hakikah Ubangiji mai afuwa ne, kuma ya na son bayin sa masu afuwa. Bata duba Alameen ko Faisal ba, ta yafe mata saboda Allah. Ta yi tunanin to me ya sameta bayan kiyayyar da ta ke nuna matan? Babu komi sai alheri. Ita ce dai har ta dangana da asibitin masu hankali. Amma ita ai gata da lafiyar ta sumul kalau a gaban iyayen da aka tsaneta don bata da su.

Sun hadu suna cin abinci gaba dayan su har Abban Hunainah, Najib da Hidayah da kuma Khalil da suka zo tare da shi. Hajiya Hadiza tace wai ina Faisal ne a gidannan?

Hajiya tace rabu da shi mutumin banza, na rasa inda ya dauko wannan bakar zuciyar kamar tsohon kuturu, ni wallahi har fargaba nake Jumaar sa ta zo ya zo garin Abuja, ya zama wani masifaffen karfi da yaji, abu kadan su Furkan zasu yi ya rufe su da fada in banda Alameen karami babu wanda ya ke ragamawa a gidannan, ban sani ba ko gamo yayi cikin kabilun nan na Lagos don ba kyau ne da su ba.

Hidayah ta tuntsire da dariya har tana kwarewa, Najib yayi saurin cika ruwa a kofi ya mika mata yace kin gani ko? Hajiya shiyasa baa son magana in ana cin abinci. Baban Hidayah ya dago ya dube shi yayi murmushi ya ce Najib ka na ji da matar nan ta ka, baka san tafi kowa fitina a gidan nan ba. Ka rage rawar kan nan da kake a kan mace, in ba haka ba zata raina ka.

Daga shi har Hidayan sun ji matukar kunya Hajiya ta ce,

“Umh-umh, kyale sa ya kula da matar sa, dubi halin da ta ke ciki fa ai dole a kula da lafiyar ta.�

Hajiya Hadiza da bata san tsamar da ke tsakanin. Faisal da Intisar ba ta dube ta ta ce, “Ke tashi maza ki je waje ki nemo man Faisal, ya zo ya ci abinci.�

Hajiya ta ce, “Ba zai wuce bencinnan na wurin masu gadi ba, ki ce da shi ya zo ina kira yanzun nan.�

Sai da kirjinta ya harba kamar ta ce wayyo Allah! Ta mike talau! Juwa ta kwasheta saura kadan ta kai kas, Hunainah ta tallafe ta tace yi a hankali, kujerar nan zata tade ki Najib ya dago ya dubesu yayi murmushi kawai ya dauke ido a kan su.

Ta fita cikin kasala da rashin kuzari amma sai ta labe a hanyar zuwa wajen bata je din ba, a ranta cewa take lallai ma ya Faisal! Har yau bai gama sani na ba, ba dai ni ce baya son gani ba, ni mujiyar sa ajalin sa to nima bana son ganin sa ko hanyar daya bi nima na daina bi. Hawayan da basa wuya a idanunta suka zubo.

Ta sa gefen rigar ta ta share ta dawo falon ta zauna a mazaunin ta tace yace ya na zuwa. Shiru shiru babu shi babu alamar sa har suka kare cin abincin.

Abinda kunnuwanta suke jiyo mata Hajiya na baiwa mamarta labari ta kasa gasgata shi, hakan nan ta kasa amincewa da abinda ta ke jin. Wai Faisal ya kawo wa Baban shi mata Bayarabiya kuma bazawara mai yaya uku da suke aiki tare a NNPC wai ita Ronke yace nan duniya ita ya ke so, su kuma sun ce wannan auren sai bayan ran su.

Hajiya Hadiza ta yi dariya ta ce,

“Ina ruwan kurucci dangin hauka. Kin san idan Allah yayi ma wata baiwa baka gani, sai dai wani ya gane maka. Amma ina mutum kaman Faisal ina auren bayerabiya?�

Najib ya ce, “To yaya zai yi Hajiya? Wadda ya ke so bata son shi, ba sai ya je inda ake son shi ba?� Ya fada ne kamar da biyu, idanun shi a kan Intisar, wadda cikin sanyin jiki ta aje cokalin da ke hannunta ta tashi ta yi dakin su da ke saman bene.

Ta sa mukulli ta rufe kofa ta tafi gaban taga ta tsaya kawai, hannayenta sarke a bayanta, wasu irin zafafan hawaye suka zubo a kumatun ta. Kamar an ce da ita juya nan; ta kalli harabar gidan ta tagar.
Chapter 82 · 0% Book details