Sashe 13
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji ya yi kirjin shi yayi wani irin bugawa da karfi! Ya hadiyi wani makalallen miyau da ya tokare a makoshin sa da kyar, ya zuki iska ya fesar cikin takaici ya ce,
“Kenan you don’t love me Halimahhh?� (Ba ki so na Halima?).
Ta ce, “Sam, ba haka ba ne Al’ameen…� Ya riko hannuwan ta duka biyu cikin zafin nama a zafafe ya ce, “To yaya ne?�
Ta daga lumsassun abnormal idanunta ta dube shi, shi ma duban ta yake impatiently (A kagauce) ta ce cikin raunannar murya.
‘You said so many things to make me happy, and try your best to make things work out okey for me. If I could describe your kindness, I would be describing an angel. If I should describe your love, I would be describing my whole heart. U are a gift Al’Ameen, from Glorious God to me, you are an angel! How could I say I don’t luv U (Ta yaya zan ce ba na son ka?)
Illa iyaka ana son duk abinda dan adam zai gabatar, ya yi kokari kada ya saurari ra’ayin shi, ya saurari ra’ayin na gaba da shi.
Ka ga kaman shi Daddy ya girma har ya kusa tsufa, ya yi edperiencing wasu al’amura na rayuwa, musamman auren da aka gina a kan soyayya, wanda mu da muke kasa da shi ba mu yi ba.�
Al’ameen duk da cewa maganar ta ta farko ta yi mai dadi, ta kuma wanke shakkun da ke zuciyarsa, amma ya kasa fahimtar ko me take nufi da wannan murdaddiyar magana? Bai san san da ya ce,
‘Shin me ye tsakanin ki da Daddyn gidan nan?�
Anan ne ta fuskanci shirmen da take shirin tafkawa, da sauri ta ce
“Babu, sam babu, illa a dan zamana tare da su na fahimci cewa shi mutum ne irin sauran mazan jiya masu kaifin tunani da hangen nesa.�
Ya ce, “To magananniya, kina ganin wrong choice (Zaben tumun dare) za ki yi wa rayuwarki kenan a hada rayuwa da Aminu?�
Ta ce, “Kash! Ana baka kana kin amsa, na riga na amince da Al’ameen-Al’ameen ne100%, illa just what my sociology told me, ka yi hakuri a bar maganar sai ka dawo din?�
To Al’ameen ya tafi Niamey da kwarin gwiwa da dukkan goyon baya na zuciyarsa kan amincewa da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba, dari bisa dari zuciyarsa ta amince da ita. Ya lura bayan nutsuwa, yarinyar mai hankali ce da sanin abinda take yi uwa-uba kyakkyawan tunani da hangen nesa she leave no stone unturned tamkar ba karamar yarinya da ba ta kai shekaru ashirin ba.
Hakan nan akwai wannan kalmar ‘class� a tare da ita ba daya take da sauran matan da ya sani ba wannan daban ce, ta san mutuncin kanta, ta san baiwar da Allah ya yi mata na ‘ya mace mai darajjah. Duk rudewar da mata ke yi a kan shi a Miami, ita ba ta yi surprised! (Don Allah mata mu dinga jan mutuncin mu a komai).
Ya yi duk abin da zai yi a Yamai cikin kwanaki uku rak ya turo kayan shi ta jirgin ruwa. Ranar da zai dawo ya shiga kasuwa a Yamai don bude ido kawai, ba abinda ya dauki hankalin shi irin kayayyakin matan su da ya tabbatar za su yi kyau da Halimar shi tun da itama tana yanayi da su, ya ciko akwatuna masu kyau da kayan matan Zindar, Niamey, Maradi da Damagaram da niyyar in sun yi aure da Halimar shi zai bata ta dinga yi mai kwalliya yana ganin ta kamar ‘yanmatan Niger. Hatta necklaces da duwarwatsun adon su ya saya mata, su wannan da niyyar su zai ba ta a matsayin tsaraba da zarar ya koma.
Ya tsaya a wani kantin turare ya saya wa Hajiyar shi saitin Givenchy (for women) da take amfani. A ranar ya sauka a Abuja.
Masu aikin fenti ya tarar suna ta yi a kowanne sako a gidan. Khaleel ke gaya masa wai Aunty Saratu ce za ta dawo sati mai zuwa. Har ran shi ya ji dadi, amma sai me?
Ya shiga sashin Hajiyar domin ya sanar da ita dawowarsa, ya kuma bata tsarabar ‘givenchy’n da yayo mata, ya ji shi a kulle gam da mukulli. Ya kwalawa Furkan kira ya ce,
“Kai Hajiya ta je anguwa ne?�
Furkan ya ce cikin rashin jin dadin al’amarin “Ya Aminu rabu da Hajiyar mu kawai, wallahi tana bin shawarar su Anty Suwaiba ne kawai, suna kai ta su baro. Yanzun wai ta koma Kaduna saboda Daddy ya ce da ita Maman Intisar za ta dawo, ba ka ga irin zagin da ta yi wa Daddy ba a gabanmu har mu da muka goya masa baya.�
Al’ameen ya rasa me ma zai ce? Ba tun yau ba wasu halayen na Hajiyar shi ke ba shi kunya da takaici ba, yanzu da girman ta a ce ta yi yaji ai ba karamin abin kunya ba ne a garesu, bai taba ganin mace mai kishin kishiya irin ta ba, wanda a shekarun ta ya isa a ce ta bari, ta kame girman ta, amma ashe wasa farin girki? Ko zama bai yi ba a lokacin ya zari mota ya nufo Kaduna cikin unguwar Kabala Custain, ainahin gidan kakanin su na wajen uwa.
Tun daga get maigadi yake sanar da shi duk gidan babu kowa sun tafi hutu Dubai har Hajiyar.
Ya girgiza kai a daren ya dawo Abuja, amma bai koma gidan su ba, gidan sa da Daddy ya ara masa wanda cikin ‘yan kwanakin babu abin da ba a zuba a ciki ba na jin dadin rayuwa, sai su da suka ki zaman gidan, anan ya kwana.
Ya kira Hajiyarsa a washe gari, yana ba ta hakuri ta dawo ko don darajar su, amma sai ta sa masa kuka wai su da uban su so suke su taru su kashe ta. Ya ce, “Amma dai Hajiya ko za ki Dubai ba yanzu ne ya dace ba, sai a ce bakin ciki ya kore ki, ai kamata ya yi ki bari sai ta dawo tukun duk in da za ki sai ki je. Ya ya za ai mu kashe ki da bakin cikin mu bayan ke ce wadda ba mu da ya ita a duniya? Ki yi hakuri ki dawo don Allah.�
Ta ce, “In dai ni ce uwar ka Aminu, to ba kai ba Saratu ko ta shigo gidan, in har kana son in dawo.�
Ya ce ya amince, amma fa in har ta dawo din. Ban da abin Hajiya shi ina ma ya zauna a gidan balle ya shiga harkar su (sai ka ce wani lokacin kuruciya). Shi dai har ga Allah lallaba ta yake yadda take so don kar ta zubar da kimar ta a idon mutane, tunda kowa ya ji ba ta gidan ya san me ta yi wa tafiyar, shi kuma ba zai so zubewar mutuncin uwarsa a idon kowa ba duk lalacewar ta kuwa, duk da cewa ita din halin ta sai ita.
Karfe goma na safe, ya shirya cikin danyen boyel navy green, haka motar da ya hau a yau ‘Kia� ce, lemon green, koren takalmin fata ne a kafar shi kirar Italy. Daman Al’ameen ba dai iya cool dressing ba, ya yi amfani da farin mudubin ido don ado kawai, ya nufo gidan su cike da nishadi.
Ya saki kan motar a shararren titin Atiku Abubakar, har ya tadda katafaren gidan su yana bin sautin Alicia Keys, iskar damuna na kara armasa masa hantsin tare da gudanar masa da wani bakon nishadi, in da duk ya motsa kamshin turarrukan sa Ultraviolet da Vanderbilt da yake yawan amfani ke tashi. Al’ameen kenan.
Ya duba kicin bai gan ta ba, ya leka dakin da suke kwana nan ma ba ta nan, ya leka dakin Dela babu alamar ta, gabansa yayi mugun faduwa, sai ya tsaya a kofar kicin din cikin zakuwa rike da ‘yan makullan shi yana zuba idon ganin ta inda za ta bullo. Zuciyarsa fes, take a yau domin hakika ta azabtu da rashin ganin Halimarsa for long four days (Tsayin kwanaki hudu).
Daga can lambun gidan ta bullo rike da ribdediyar goba koriya shar da za ta hadawa Daddy guava juice sai ta ga bakon da bata zata ba, tsaye kofar ofishin ta. Ta saki baki galala! Da gani na jin dadi ne ta ce,
“Lah! Al’ameen saukar yaushe?�
Idanun su ke kallon juna tamkar sun hadiye junan su don so da kauna. Ita kanta ta yi kyau a yau, domin ta yi wanka kenan ta sanya daya cikinr iguna da skirt din da ya sayo mata kalar su black and pure white, sai doka kamshin brut (body spray) take, hakan nan curarren gashin ta mai kama da gammo yau ya sha wanki ya ga mayuka kala-kala da ya shekara bai gani ba sai sheki yake a cikin sassanyan hantsin na Litinin. Ta yi mai tufka daya kwal murtukekiya jelar sai yawo take a gadon bayan ta, she look so cute kwarai cikin kayan.
Ita kanta ba ta san nishadin me ta tashi da shi a yau ba? Haka kawai tun da Dela ta ce da ita Hajiya ta yi balaguro Kaduna ta tashi ta fetse kwalliya, ashe rabon gwarzon masoya Al’ameen ce. Ya bude mata dukkan hannuwan shi amma sai ta noke ta cilla mai katuwar gobar da ke hannun ta, ya mika dogon hannunsa ya janyo jelar gashinta da karfi, don zafi ba ta san sanda ta fada jikin shi ta yi maza kuma ta ture shi ta ce (Dela da ke makale jikin kofar dakin ta, tana leken su, ta daura hannuwan ta a ka ta ce, “Na shiga uku ni Dela, kar dai yarinyar nan ba ta san Aminu ba?
Za a aikata da na sani! Ko da yake duk laifin uwarsa ne…ikin ta babu inda baya rawa saboda kaduwa, yau kam ta yi dana sanin sa masu idon da ta yi, da bata ganowa kanta wannan kayan takaici ba, wai an ce ka bar abin da ba ruwanka izuwa abinda bai shafe ka ba, sa-ido sana’ar banza).