Sashe 37
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duka sai ta basu dariya, daga kawun har ‘ya’yan sai da suka murmusa. Hakika Hajjo na kaunar Yayar ta fiye da kowa a duniya bata hada matsalar ta da ta kowa “a’ah Hajjo, Hadizah ta dage taga diyar ta Fatimah a Riyadh, shine muka zo mu bincika, don yarinyar wai ta taba gayawa su Hidayah a Lagos gidan su yake kuma a nan Bictoria Island� ta dafe kirji tace “anya? Yanzu haka ‘yar farar yarinya zata gani tace ‘yar ta ce, tunda tasa abun a ranta har ya dameta, ta jawo mana rikici da mutane ana zaune lafiya.
In banda neman tada zauna tsaye ma irin na Ya Hadizah, ta yaya ‘yar data bata a kauye za’a ce an ganta a babban birni irin Riyadh?�
Yace “Uwa ce, kada ki musa mata?�
Hidayah tace “kuma dai Anti Hajjo kin san babu inda Allah baya ikon sa. KUN-FA-YA-KUN ne fa, wanda in yace ‘kasance� sai ya kasance. To in banda iko da kudurar tasa ta yaya kuma kuka tsinci kanku a France daga kauye ko ruga kamar yadda Mama ta bamu labari?
Wallahi ni kaina daga ganin da naiwa Saratu da farko na san jinin Mamar mu ce, ko ke kika ganta za ki yi mamaki, in banda haske da ta fi Mama, da digon tawadar Allah dake gefen hancinta ba abunda ba irin naku bane a jikin ta sai ko ‘beauty-point� da bata da shi irin naku, ko yau kika ga Saratun wallahi sai kin dangantata da Mamar mu. A yadda na ji ta cikin raina a sanda na fara ganin ta, babu banbanci da yadda nake jin Hunainah�.
Maganar yarinyar ya ratsata kwarai, ta dage kai sama kamar mai irga ‘ya’yan taurari tace “shin ya sunan mahaifin ta?� Hunainah tace “Baba Makarfi ne ko Bello I’m confused?� Hidayah tace “Bello Makarfi, exactly sunan kenan�.
Hajjo ta dafe kirji, ta mike ta soma safa da marwa a kayataccen falon ta, bakinta na mai kakabin sunan da ya karade talbijin da rediyoyin gida Nijeriya tace
“Bello Makarfi, kuna nufin Brigadier Bello Makarfi? Dan takarar kujerar shugaban kasar nan da suka shirya juyin mulki a shekarar baya?
Ya zauna ne a wancan gidan dake kallon nawa, a sanina baya da wata diya mace, duk ‘ya’yan sa maza ne su goma cif, in ma ya haifa ban taba ganin ta ba, amma na san manyan ‘ya’yan sa su Faisal da Najib, don na kan gansu sun wuce a mota ko kuma tsaye a harabar gidan sai dai ko gaisawa bamu taba yi ba, a bakin Hassan ma na ji sunan su.
Mutane ne ‘unsocial� watau wadanda basa shiga shirgin kowa. Ba zan karyata ku ba tunda ban san gaibu ba amma Makarfi yana kulle tun bara, don haka kuzo muje gidan Bello Makarfi. In Allah yasa Fatimar mu ce zan gane�
“ta yaya?�
Ta juyo ta dube shi tana murmushi
“jini baya boyuwa Baban su Hunainah. Yaya ta sha gaya mun a ranar da aka sace Fatimah, Baban ta ya tsaga mata biyu-biyu a tsakiyar kirjin ta na family din shi. Hakannan Fatimah nada tawwadar Allah a gefen hancinta da diga-digan ta tun tana jaririya� Bashir ko magana baya iya yi, ta sake yin murmushi.
“In kuma duka wannan bai yiwu ba, akwai shari’ah, akwai kuma likita mai auna jini, balle ma nasan ba yadda za’ai su ce ‘yar su ce in dai da gaske tsintar ta su kai iyayen ta kuma suka ganta�.
Hidayah da Hunainah duk sun yi tsit ne kamar ruwa ya cinye su. ‘Yar dan takarar shugaban kasa? Kada su je a harbe masu Aunty da Daddy in sun ce Saratu ‘yar su ce. Saratou ta sha gaya masu yadda iyayen ta da Yayyun ta maza ke son ta kasancewar ita kadai ce mace a cikin ‘yan uwan ta maza goma ris! Rana daya su kawo masu wannan magana mai rikitarwa?
Ita kuwa Hunainah sabanin tunanin ‘yar uwar ta ne. Ita tunanin da ta ke shin wace irin runguma zata yiwa Saratu a yau a matsayin ta na shakikiyarta ta jini?
Ta sha kimanta nedt haduwarta da Saratu Bello by destiny or phenomena�., (cikin wata kudura da irada na Ubangiji) tun bayan rabuwar su a Kingston.
Da da ne, a guje zata ruga ta rungumeta amma yau har bata san irin wadda ya dace ta yi mata ba.
Gidan da ta nuna masu kadai tace nan ne gidan Makarfi ya firgita su don ko a turai da U.A.E da suke zagawa samun mai irin wannan mahaukacin ginin kaman ba za’a mutu ba sai an tona. Baban su bai biyo su ba tukunna yana can masaukin sa don haka Hajjo tasa ‘ya’yan ta biyu a gaba suka doshi gidan Brigadier Bello Makarfi.
Rashin sa’a! Lallai ya tabbata gare su, ‘what was eben more unfortunate (babbar rashin sa’ar ma) get din gidan a garkame ya ke da wani irin azababben kwado, shi kansa kwadon yayi kura futuk tabbacin yayi shekaru biyu a hakan. Kafafuwan su sun sage, yawun bakin su ya kafe kat, tunanin su ya kare haka dabara ta kare masu. Shin me kuma za su yi su ceci rayuwar mahaifiyar su?
Wani kabila ne ya shawo giyar shi yayi tatul yana tafe yana tambele kamar ya kife, daya zo gabansu sai ya ja birki, ya dakata ya zaro ido yace
“wow�, gorgeous!� wato kyawawan yara.
Ya dubi Hajjo yana washe baki ya sake cewa “Madame, will u dash me dat rose Babe, plz?� Ya nuna Hunainah, wadda idon ta yai jage-jage da hawaye ta manna mai harara.
How much do you like this story?
5/8/22, 21:04 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page9ï¸âƒ£
Abuja, Ranar Litinin
Karfe Hudu Da Rabi Na Yamma
Intisar ta tashi da matsananciyar damuwar da bata san ko ta mece ce ba a safiyar yau Litinin. Wani irin kunci ke damun ta a zucci da bata san ko na mene ba kamar koyaushe wani sabon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi?
Ta rasa meke damun ta kwata-kwata, don haka ne ma ta langabe a gado tun safe har yamma ko falon su bata leko ba, bata ko so Anti Saratu ta ganta, don ta san muddin ta ganta cikin wannan halin to ita da kwanciyar hankali sun yi hannun riga kenan.
A lokacin ita kuma Antin cike take da farin-cikinn samun ‘appointment� da ‘Afribank,� don haka ne ma tun safe bata nemi Intisar din ba tana ta aikin takardun neman akinta, sai da ta gama tas ta ankara da rashin Intisar din a falon tun bayan da ta karya kumallo. Tasa murya daga falon tace “Saratu!�
Ta yi doguwar mika gami da dan tsaki cike da jin zafi, amma ba da Antin take ba, na damuwar da ta cuzguna rarraunar zuciyarta ne, ta mutstsike ido gami da tattare curarren gashin kanta cikin bakin ‘hair-bound� ta zura kyawawan kafafun ta cikin farin takalmin bakin gado (bed-side shoe), ta murda marikin kofar dakin cikin matsananciyar kasala ta fito ta tadda Antin, saye da doguwar riga ruwan makuba mai hade da hula, amma bata sanya hular a kanta ba.
Ta dube ta cike da murmushi irin wanda rabon da ta ganta da shi tun kulle Daddyn su tace “kin san meye ne?
Wani abin alheri ne nan ke shirin samun mu, amma na gan ki rather-moody today, wani abu ne ya faru ban sani ba?�
Ta zauna bisa kafafun Mamar ta, ta kwantar da kai bisa gwiwoyin ta tamkar dai zamanin kuruciya, kodayake ita har girman ta baka rabata da yaro dan shekaru uku, son jiki kuwa ko mage haka ta ganta ta kyale. Muryan ta a karye tana dibar bangon dakin tamkar mai tunanin wani abu tace
“nima na kasa gane meke damuna, amma Mamar mu, mafarki fa na yi yau wai an tafi da Daddy za’a harbe…�
Kafin Antin ta samu damar cewa uffan, itama Babyn ta karasa zancen ta sai dirin motoci suka ji, mota ba daya ba babiyu ba, hakannan ba uku ba, Intisar ta nufi bakin taga ta leka da sauri, abinda ta gani ya gigita ta (Daddyn su ne ke fitowa daga mota).
Ta kwalla ihu tace “Daddy!� Anti Saratu ta mike a gaggauce zanin ta na kuncewa tayi sa’ar riko shi, da gudu itama ta leka ta tabbatar Saratun ba karya ta ke ba sai tayi waje.
Ita ko Intisar sai taji hawayen dadi da farin-ciki na kwararo mata, ta jingina bayanta da bangon tagar idanun ta a rufe.
In har tana da wani buri daya saura a rayuwar duniya to a yau, ya cika. Ta daga hannuwanta sama ta shiga kwararo yabo da godiya ga sarki Allah jikin ta na wani irin kyarma da karkarwa tamkar wadda aka sanya cikin sanyin kankara.
Daga bayanta Khalil ya zungureta yana dariya kamar bakin shi ya tsage ya ce,
“To ki je, ke kadai yake nema, ke kadai yake kira, ke kadai yake tambaya Inteesar!�
Ta nufi sassan Daddyn da sauri faram-faram kamar zata tashi sama, Khalil na biye da ita a baya, amma ji ta ke saurin da ta ke dinnan ba zai sadata da Daddyn a yau ba, sai ta kara a guje.
Shima Daddyn ya taso ne ya je nemanta da kansa don yana ganin ta ki zuwa ne sabida tsoron Hajiya Nafi.
A bakin kofar shiga falon sukai karo da juna, a guje ta rungumeshi tana hawaye ta ce,
“Daddy kai ne, ashe dama akwai ranar da zaka dawo?�
Ya kalleta. Ya ce,
“Saratu, ke ce kika lalace haka! Ina Al’amin Hajiya da ya tafi ya bar mun iyali cikin wannan ukuba?�
Ya saki Inteesar ya juya ga Hajiya tamkar ita ce ta boye mai Aminun, ta sunkuyar da kai bata ce komi ba sabida zuciyar ta dake kuna, don ita kanta bakin-cikin da Al’ameen ya kunsa mata yana da yawa amma bai tambaye ta ba sai akan tsinanniyar ’yar sa? Idan ma yana nan din shi bawan su ne da zai nemo masu abincin?
Duka yaran gidan basa nan sai Khalil kadai ya ce,
“Daddy, muma tunda ka tafi, bamu kara jin labarin sa ba. An aika mai cewa an kulle ka amma ya ce wai ba ruwan sa.�