Sashe 26
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun a shekararta ta farko a makarantar sunan ta ya yi tambari a set din su, ta yi sadikai (abokanai) da dama, ‘ya’yan Larabawa bila-adadin saboda farin jinin ta da shiga rai. Harshen ta ya juye da larabci ziryan. Larabci na hakika kuwa ba kala daya ba, ba kala biyu ba, tun daga na Hijaz, Maghrib, Yemen, kudanci da arewacin Istanbul babu wanda ba ta yarawa saboda cakudo da mu’amala da jinsi-jinsin dalibai ‘yan asalin kasashen.
A shekarar ne kuma aka bata Nakeebatul-fasl wato (class monitress), shugabar ajin su saboda duk tafi ‘yan ajin focusing a hankali a hankali malaman su ke gane hakan don a komai ita ce a kan gaba.
Uniform din su farar shirt ce sol da bakin tie, hade da bakin skirt sai farin ribbon da bakin sandal kirar Turkey. Ba kasafai suke haduwa da Khalil ba da ke bangaren maza in ba wani taro na makarantar ya hada su ba kamar quizzes ko debates da makarantar ke shiryawa a kai akai.
A shekarar ne ko kusan karshen shekarar aka kawo wasu yara mata guda biyu daga France, hostel din da take, daya a saman gadon ta daya a gefen gadon ta ke da ganin su kin ga half-cast wato ruwa biyu, suna magana da harshen Faransanci a junansu, maimakon Larabcin Saudiyyah da ya fi yawa a makarantar.
Yara ne da ko za ta girme su da kadan ne, kyawawa amma farin su mai duhu ne, hakan nan ba su da yawan gashi cancan, wanda ke nuna ‘yan asalin Ifrikiyyah fatar jikin su da irin maganar su shi ke nuna girman Faransa ne ko kuma dai sun zauna a France na lokaci mai tsawo.
Sai da daddare ta kwanta ta shige cikin bargo bayan ta yi addu’o’in da take yi ta shafe jikinta, amma barcin ya ki zuwa, tana ta tunanin wadannan yaran da ta ji sun shiga ranta farat daya tana kuma tsoron ta kula su su yi mata wulakanci don da alamun su ‘yan jin kai ne sai me? Kawai ta ji sun juye harshe zuwa zallar Hausa kamar jakan Kano, ta ji ta saman gadonta ta ce,
‘Hunainah kin yi barci ne?�
Ta ce, ‘A’a, Allah na kasa barci Yaya Hidayah, wannan Balarabiyar ta kasan gadon ki kawai, haka kawai na ji ina kaunar ta don kamannin su da Mamin mu in kin lura har ya yi yawa. Amma kalli ko kallo ba mu ishe ta ba, ko ta gane mu ba Larabawan ba ne oho.�
Wadda aka kira Hidayar ta cafe, ‘Kamar kin san abin da zan ce miki kenan. Amma Allah ya kai mu gobe duk inda Larabci yake zan koye shi a gobe dole mu zama kawayen ta Allah�.�
Dariyar da take ta faman babboyewa ce ta kubuce, ta rasa dalilin da yasa mutane da dama basa gane ita Bahaushiya ce a makarantar, don su ba su san ma wata kabila wai ita Hausa ba, hatta malamanta sunanta ne kurum yake fallasa ta domin sukan ji shi banbarakwai har ba su iya fadi dai-dai, su kan tambaye ta nationality dinta a kullum amsar ta ita ce,
“Ana Nigery (ni ‘yar Nigeria ce).� Daga haka ba ta kara komai a kai.
Dariyar ta tasa duk suka tsorata suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su ta ce da su, ‘Ma’ana Arabi, (Ma’ana ni ba Balarabiya ba ce), nima Bahausa ce kamar ku, ku sauko mu yi hira.�
Duk suka dirgo gadon ta suka dubi juna, sai kuma suka tuntsire da dariyar gane ashe dukkan su tushen su daya.
“Sunana Saratu Bello, na zo daga Nigeria.�
Hidayah ta ce, “Muma duk ‘yan Nigeria ne. Amma an haife mu a France. Sunana Hidayah Bashir Sambo kanwata Hunainah. Baban mu ke aiki anan sai kuma aka cilla mu Russia, daga baya ne aka turo mu nan, nan din ma an ce ba da dadewa ba ne za mu tashi, saboda aikin da zai yi anan temporary ne. Sunan garin mu Shanono a cikin Kano, ke kuma ya sunan garin ku?�
“Mu a Kaduna muke, daga baya kuma muka koma Lagos yanzu duk gidan mu suna can Lagos.�
“Mu ma muna zuwa Lagos wata unguwa Bictoria Island akwai antin mu Hajjo mu kan je hutu wurin ta.�
‘To ai mu anan arear ma gidan mu yake, in kin wuce gidan Major General Shitu Allazi.�
Karamar wato Hunainah da ta zuba mata ido kawai tunda suka fara surutun su ta ce,
“Allah kamar ki daya da Mamar mu, end of the year, wato karshen shekara za a kai mu gida hutu, za ki bi mu Maman mu ta gan ki?�
‘Idan school ta amince min sai mu je mana kafin mu tafi gida, amma akwai yayana Khalil yana bangaren maza sai dai in tare za mu je?�
Gaba daya suka hada baki suka ce,
‘Ba sai mu je taren ba?.�
Daga ranar fa kawance ya kullu, inda duk ki ka ga Intissar kya ga Hidayah da Hunainah, dakin cin abinci, wajen daukar darasi, dakin karatu da wajen wasannin motsa jiki duk tare suke zuwa. Su ci mai kyau su sha mai kyau su zauna a mai kyau, kada ki so ki ga yadda suke wani irin girma cikin shekara guda kacal.kamar kajin gidan gona.
Ga Hidayah da shegen tonon fada da ‘ya’yan mutane sai su taru su shigar mata wani lokacin kuma ta zame ta bar su a ciki don duk ta fi su wayo, ba ‘ya’yan Larabawan kadai ba har ‘ya’yan manyan Saudiyyah yaran nan ba sa kyalewa kamar kasar ta uban su ce. Hakan nan kowacce na ji da basira da kwakwalwar da Allah ya hore mata komai su ne higher ita Hidayah a fannin sport ta fi kauri kasancewar ta doguwa sosai.
Kwanci tashi ba wuya gurin Allah kuma dama masu iya magana suka ce wai shekara kwana ce. Yau ga ranar tafiyar su hutu ta zo, an jinkirta tafiyar ‘yan Nigeria saboda babu jirgin su zuwa washe gari. Da taimamkon Dr. Alhassan kasancewar shi mutumin Intissar aka bar su bin su Hunainah da kuma kasancewar gidan gidan Jakadan kasarsu ne, ita da Khalil suka bi direban su Hidayah da cewar mota za ta je har can washe gari ta dauke su zuwa airport.
Gidan su Hidayah na Shari� Palastine ne a cikin birnin Riyadh. Tun daga gate Saratu ta tabbatar su ‘yan gata ne, amma gatan da ta ga ana gwadawa su Hidayah ya dame nasu ya shanye.
Har a jikin kofar shiga falon gidan an mammanna card na Larabci da Turanci da Faransanci, masu dauke da rubutun “U’re highly welcome kids.� Wani kuma an rubuta “Marhaban bikum ya bunayyah.�
Ta yi tsaye hannu a haba tana kallon Mamar su Hunainah na katantanwa (juyi) da su a tsakiyar falo tamkar ta maishe su ciki ta sake haifo su don kauna, shekara guda ba ta gan su ba. A ranta ta ce, “Nima dai insha Allah gobe I yanzu ina jikin Antina, nima ina jin dumin Mama na.�
Ba ta ankara ba ta ji Mamar su Hunainah ta rungumeta ta baya, ta sumbaci kuncin ta na dama wani dadi ya ratsa ta irin wanda bata taba ji a duniya ba, ita ma ta maida mata da irin hakan, gaisuwar garin kenan “Marhaban bi kum asdi’ka’l� wato barkan ku da zuwa abokan mu.
“Ya Rabbi!� Haka ta fadi tana ja da baya. Wannan kama da yawa take tamkar ta yi kaki ta tofar. Tunaninnika daban-daban take sakawa tana warwarewa a ran ta amma ta rasa na kamawa. Su ko su Hunainah sai dariya suke abin su suna kyakyatawa suna fadin dama sun kawo Saddikar su ne (kawar su) Inteesar don ita ma Maman ta ji irin mamakin da suka ji da ganin Saratu.
Jikin ta ya yi sanyi kalau, tuni ta jike kashirban da gumi. Tasa masu aikinta suka yi entertaning ’ya’yan ta da bakin su domin ta nemi duk wani tunani da kuzari da ke tare da ita ta rasa.
Su kan su masu aikin da suka dubi Intisar, suka kuma dubi tangamemen hoton uwargijiyar su da ke kafe a falon sai suka ce ‘Subhana Rabbiyallazi iza ya kulu li shai’in kun fa ya kun.� Ma’ana tsarki ya tabbata ga Ubangijin da in ya ce kasance, sai ya kasance. Domin wannan kama da yawa take.
Ambassador Bashir Sambo, shi ne mahaifinsu, baya gari a wannan lokacin. Duk kokarin Haj. Hadiza na neman layin shi abin ya ci tura a wannan daren, duka wayoyinshi a rufe, kamar ta dora hannu ta ce Wayyo Allah! Jikin ta har wani irin rawa da kyarma yake.
Ita kanta ta kasa tantance me ke damun ta game da bakuwar ‘ya’yanta? Haka ta kwana cikin zullumi da ci da zuci, wani abin takaici kuma da sassafe sai ga motar Kingston College a kofar gidansu ta zo tafiya da su airport tana kwance a daki wani matsiyacin zazzabi ya rufe ta, Khalil ya ja hannun kanwar shi ko wanka ma ba su yi ba balle karin kumallo suka shiga motar suka tafi. Karfe goma na safe suna cikin jirgin Mea International wanda zai sada su da kasar su ta haihuwa, Nigeria.
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page3ï¸âƒ£
Ko kafin a dawo hutu, lokacin aikin su a Riyadh wanda dama na wucin gadi ne ya cika, an cilla Bashir Sambo kasar Korea aikin Jakadanci. Su Hunainah sun yi bakin ciki ba kadan ba na rashin sallama da kawar da suke so kamar ran su ga shi kuma basu taba tunanin yin musayen lambar waya ba.
Hajiya Hadiza, ta roki Allah ya cire mata wannan tunanin da ke addabar zuciyarta yake kuma neman wargaza mata farin ciki, tunanin cewa wai diyar ta Fatimah ta gani. Shi maigidanta ma da ta fada masa dariya ya yi ta yi mata wai tasa abin a ranta ne ba dole ya yi ta yi mata gizo ba?
Dama duk ‘yar farar yarinyar da ta gani ta ce tana kama da ‘yar ta Fatimah yau kuma kacokan ta ce ‘yar ta gani dungurungum.