Sashe 2
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In yana fada mata irin wannan kallon shi kawai take ta yi dariyarta mai isar ta ta ce wata rana zai daina ne, don yana ganin ba su da kowa ne a nan inda suke sai junansu. Shi wani irin mutum ne da bai bambancewa cikin mu’amalarshi da kowa, abin nufi, mai kudi da mara kudi, mace ko namiji. Dr. Al’ameen Bello kowa nasa ne.
Don haka ya sha fama da mata iri-iri a zamanin karatunsa, daga Turawan zuwa ‘yan sauran kasashen duniya da karatu ya hada su. Ihsan A.A kadai Allah ya bai wa sa’ar koda yake zan iya cewa, Al’ameen ya auri Ihsan ne domin ceton ta daga masifar son shi da ta sanya kanta, amma ba wai don wani mashahurin so na Allah ko na Annabi ba.
Ihsan Abubakar Argungu, ‘ya daya tal ga mataimakin Governor na (Central Bank of Nigeria), Dr. Abubakar Argungu. Iyayenta mazaunan Abuja ne na din-din-din duk da cewa dukkansu aiki ne ya kawo su a garin, daman an ce wai birnin Tarayyah ne. Kasancewar Ihsan ‘ya daya jal ga iyayenta ya sanya duk wani buri na Dr. Argungu da mahaifiyarta Ann Hathaway wadda ta kasance Kirista ‘yar uslin Birnin Gwari, akan Ihsan yake.
Mahaifiyarta Ann ce mamallakiyar bankunan Savannah da ECOBANK da ake damawa dasu a halin yanzu a kowacce jiha ta Najeriya, don haka gaba da baya Ihsan ‘yar gata ce ta karshe gun iyayenta baya ga watsi da ta yi da su kan son Al’Ameen Bello.
Iyayenta sun turo ta karatun medicine ne a University of Miami, inda ta hadu da Al’ameen, wanda a lokacin ke ba da lacca cikin makarantar bangaren masu karantar lafiyar kwakwalwar dan-adam.
Tun daga wannan lokacin Ihsan ba ta kara nutsuwa ba sai da ta zamo friend din Aminu. A hankali a hankali ta yi amfani da hilarta wajen jan ra’ayinsa gare ta tana bayyana masa yadda take son shi wani zubin har tana kuka take rokon shi ya aure ta gudun kar ta sanya kanta cikin gurbatacciyar rayuwa.
Ga Al’ameen mutum mai tsananin tausayin mace, tun ba in tana fidda mai hawaye ba, sai dai sam a lokacin bai da ra’ayin aure, tunda kuwa zai sada shi ne da gidan da ya baro baya ko son tunawa. Yaya ma za ai ya yi aure, ba tare da sani da yardar mahaifansa ba da baya da kamar su? Don haka ya rungumi Ihsan suka tsunduma watsewarsu ba tare da tunanin illar da hakan zai haifar ba.
Wannan ya fi komai dadi ga Ihsan domin dama ita ba auren ne a gabanta ba, illa tana tsoron idan ta bijiro mai da irin soyayyar da ta zaba musun ba zai amince ba, kasancewarsa mutum mai tsananin kamewa daga barin jin dadin rayuwar Turai a ko’ina kuma a cikin kowanne hali ya sami kansa, duk zalamar yarinya kuwa haka za ta ga Aminu Bello ta kyale domin abin da ya kai shi kadai yasa a gaba.
To itama Ihsan din kowa da ke tare da su ya yi mamakin yadda ta samu Ameenun haka a hannu, ba mamaki, domin an ce kowacce ‘ya mace da kissarta ake haifarta, hakan nan Ihsan tun tana mitsitsiyarta take koyan kissa gun uwarta har girmanta iri-iri ba wadda ba ta iya ba, don haka duk saurayin da ta kimsawa kanta sha’awarsa ta same shi ta gama kuma da kyar ne yake kubuta daga tarkonta.
To haka shi ma Al’ameen, ta tabbatar sha’awarshi ya fi son shi yawa a tare da ita kamin su yi aure, sai dai a dan zaman da ta yi da shi ta koyi kaunarsa saboda wasu kualities nasa da ke burge ta da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.
Don haka ne ma duk wulakancin da yake mata in ya bushi iska ko ya yi sabuwar girlfriend take hakuri tana shanyewa, don ta tabbatarwa kanta tana samu nutsuwa 100% and beyond a tare da Al’ameen fiye da duk wasu maza da ta taba mu’amala da su gida da wajen. Hakan nan tana ganin Al’ameen ko a cikin maza daban ne wurin nuna kauna. Samun maza irin su a matsayin MIJI sai mai sa’ar gaske. Ba ta taba haduwa da namijin da ke gamsar da ita ba har ya kure ta kamar Al’ameen ba. Ba ta taba haduwa da namijin da ya san darajar diya mace kamar Al’ameen ba.
Don haka ta kara manne masa ta like masa tare da kara zage damtse wurin nuna masa ingantacciyar kauna da kulawar da ta sa shi dole ya so ta, ta kuma shiga yakar macen duk da ta gani tare da shi ba tare da shi din ya sani ba ma. Ta kuma alkawartawa ranta, ruwa ko iska baya raba su.
Daga baya ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa Musulmi ne, da kuma irin horon da Daddy dinsu ya yi masu, wanda da a ce yana tare da shi, hakan ba zai taba faruwa da shi ba.
Ya roki Allah ya yafe masa ya kuma nemi Ihsan da ta yi Istibra’i su yi aure, ita kuma ganin lokacin Aminun na sonta kamar me ta ce ba ta san wannan ba, jin hakan shi kuma ya fita harkarta kwata-kwata, ko a tunaninta kuma ko a mafarkinta a lokacin ba ta kawo Al’ameen zai iya rayuwa ba tare da ita ba.
Ta kuma tabbatar gab yake da ya shafe ta kwata-kwata a babin rayuwarsa in har bata amince su yi auren ba, ta amince ta saduda cewa shi din mai ra’ayin kansa ne, don haka ba ta isa ta sashi ko ta hana shi ba.
Suka yi auren su mai tsafta ba tare da sanin iyayen ko dayansu ba.
Daga baya ne ita Ihsan ta aikawa Ann cewa ta yi aure da wani likita Al’ameen. A lokacin hanyoyin sadarwa basu yi kamarin da suka yi yanzu ba. Ann din ta aiko mata da zagin cin mutunci ta waya da e-mail kan don me ta auri Musulmi ba ta auri dan Addininta ba, bayan ta yi mata alkawarin muddin ta tashi aure Kirista za ta aura, don wai sun fi rikon aure. Shi kuma mahaifinta ya ce kwata-kwata ba ta kyauta musu ba ta dauke su ba a bakin komai ba tunda kuwa har za ta iya ta yi aure ba tare da sani da amincewarsu ba, don haka ta je Al’ameen din ya maye mata gurbinsu.
To Ihsan ranta ya baci sosai da iyayenta a ganinta gata ta yi wa rayuwarta ai, domin shi kansa auren ai mutunci ne ko bature yana daraja aure, da dai ta ci gaba da gurbatacciyar rayuwar turai da babu komai cikinta sai lalacewa, kuma ba su yi mata uzuri da soyayyar da ta rinjaye ta ba sun manta an ce luv is overall, wato soyayya tana gaba da komai.
Wannan ya faru shekaru uku da suka gabata, tun daga lokacin Ihsan ba ta kara waiwayarsu ba, duk da cewa daga baya su din sun neme ta amma ta share su, don tana ganin son Ameenu ya fiye mata komai, ko in ta sauraresun me za su yi mata? Za su hana ta aurensa ne? To gara ita, shi din ko sanar da su bai yi ba, tunda kuwa a lokacin ya riga ya shafe gida kwata-kwata daga kundin tarihinsa illa sabuwar rayuwar da ya gina a gaba. Sai suka hade abinsu suka dunkule junansu wuri guda suka bude sabon shafin rayuwa cike da soyayya mai ban sha’awa.
Daga Al’ameen har Ihsan kowa na son Da, musamman ita Ihsan da take ganin haihuwa da Ameenu ne kadai zai dorar da dangantakarsu. Tana ganin in ta haihu da shi zai mallaka mata dukkan so da kaunarsa da har yanzu kwakwalwarta take gaya mata bata mallaki komai a ciki ba duk da cewa da wuya a karance shi, amma hakika ta san bata da dukkan so da kauna a zuciyarsa. Hana rantsuwa za ta iya cewa ‘yana son ta� kadai.
Wannan ita ce matsala ta farko da suka fara cin karo da ita a rayuwar auren su, kuma in har suna da matsala a auran to wannan ce. Lokacin da Al’ameen ya soma complain (korafi) wai abortion (zubar da ciki) da ta-yi ta-yi ya shafi lafiyar mahaifarta, cikin kwafa kuma sai ya ce ko ciki har nawa ta barar oho. Da haka suka fara fada, ta ce ya san tana bare-baren cikin ai ya neme ta da watsewa, don ita tun farko ai aure ta ce su yi. Yadda ta lurra Al’ameen mutum ne mai masifar son yara, ko tafiya suke bisa hanya ya ga yaro sai ya tsaya ya dauke shi ya yi kissing ya ba shi choculate da baya rabo da saye cikin kantuna.
Ranar da Ihsan ta yi nadamar aurenta da M.A.B shi ne ranar da ya ce da ita wai shi dama tun ranar da ya soma saninta ya yi mamakin maza nawa ta sani? Shi ba irin matar da ya so aure ba kenan a rayuwarsa, amma ya zai yi da kaddara? A wannan ranar ne Ihsan ta yi kuka wanda rabonta da shi tun na sallamar ta da iyayenta shekaru goma a baya.
Kewar iyayenta ya zo mata. Ta tuna masifaffen gatan da take da shi a wurin iyayenta da yadda suke sonta, suke kula da ita, suke gudun duk wani bacin ranta. Yau ga namiji kwaya daya na yi mata yawo da hankali. Sai take tambayar kanta ko me Al’ameen ke takama da shi da yake gara ta haka?
Ba ya takama da komai illa jarababben son da take masa. Ta tabbatar duk wani cin mutunci ma in da a gaban iyayenta take zai zo da sauki fiye da nan din da yake ganin ba ta da kowa sai shi. Sai dai ta kudurce a ranta koma me zai mata ko duka ne ba za ta taba rabuwa da shi ba.
Daga baya Al’ameen da Ihsan duk sun amince ba hayaniyarsu ko tashin hankulansu ne za ya ba su haihuwa ba, illa ma ya rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki, ta so da fahimtar juna, sai suka dangana. Shi Al’ameen yana addu’a ita ko Ihsan Addinin nata ma gashi nan ne, sallah sai in ya takura mata za ta yi in baya nan ko a hadu a gaba.