← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 90

Sashe 47

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki ta shiga dakin Antin sai ta tadda ta tana wani rubutu da ‘chalk� a bayan kyauren bandakin ta, tayi abinda ya shigar da ita ta fito. Da ta tabbatar antin ta shiga wanka sai tazo ta karanta, ba komi bane illa (off-duty 29/9) wato Daddy ya dakatar da ita girkin sa a ranar ashirin da tara ga watan tara.

A da, kullum ta Allah masu aikin gidan kan shigo da kayayyakin abinci iri-iri daga katon na juices zuwa na sauran kayayyakin bukatar yau da kullum amma yanzu kwata-kwata ‘store� din su ba komai duk na Hajiya Daddy ke cewa su kai.

Rannan taga Antin ta debo kudi ta kira direban cefanen gidan tana lissafa mai abubuwan da zai sayo mata. A daren ranar ta shiga dakin Antin ta gaya mata kawar ta Hajiya Zainab na kiran ta a waya, sai ta taddata rub da ciki tsakiyar gadon ta tana girzar kuka.

Tayi saurin komawa da baya ta kife wayar ta kifa kanta a jiki itama tayi ta kuka har Allah ya gajishsheta. Ta tabbatar Anti na cikin matsananciyar damuwar yadda Daddy ya yi watsi da su. To amma maiyasa bazata gaya mata ba su taru suyi ta kukan tare?

A rayuwar ta, bata taba ganin Anti tana kuka ba. Mace ce tamkar da maza; zuciyar ta mai tauri ce, ba kowanne kankanin abu ke sata kuka ba. Shin ko wannan shine gaskiyar abunda kunnuwan ta suka jiyo mata kwanaki?

Me yasa su basa dauwama a farin-ciki ne? Ta tambayi kanta wai meyasa rayuwar su ke juyawa ne tamkar a majigi?

How much do you like this story?
5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three

*@Takori*

Page2ï¸âƒ£

Alhamis, 1 Ga Watan Rajab
Da Karfe Bakwai Dai-Dai Na Safe

Ya shigo sassan su kamar abin arziki, ga dukkan alamu yayi shirin ofis ne yana magana a waya. Dadi ya kama Inteesar don rabon ta da ganin sa ma har ta manta. Kacokam komi nashi ya maida shi hannun Hajiya.

Itama Antin tayi shirin tafiya aiki, ya zo ya wuceta fuuu� kamar guguwa ko kuma wanda aka tankado tana zaune a falo ko dubar sashen da take zaune bai yi ba ya fada dakin Antin.Tana zaune tayi tagumi da hannuwa bibbiyu cike da damuwa, sai ta jiyo hayaniyar su, Daddy na cewa.

“Wannan lalataccen aikin daga yau na soke shi, don ba mutunci na bane, na kuma gaji da maganganun da ake yada mun akan na bar matata tana aiki alhalin ban rage ku da komi ba. Meye amfanin ni in fita ke ki fita waye mijin? Sam da sake, ba kuma zai yiwu ba sai a sake lale, wannan ba tsari na bane.

Don wa nake nemowa ba don ku ba ina na gaza a bukatun ku?�

Tace “da da ne ka ce in bar aikin a sanda kake mijina sai in bari ba a yanzu da kake Mijin-Hajiya ba. Da baka san ci na ba balle shana, uwa-uba bani da hakkin matar aure don ni ba mutum ba ce koko don anga ina shiru kuma sai a sa bakin ciki ya kasheni in ban fita na nemowa kaina abinda zan ci ba, kokuwa mu dabbobi ne ka daure?

Ita matar ka da ke fita kasashe kwana da kwanaki tana cinikin ta ita ba’a kawo ma gulmar ba sai ni mai zuwa aiki in dawo?�

Ya soma nuna ta da dan alin shi “idan zaki yi rainin ki, da dibar albarkar ki, ki tsaya a kaina, don in kika tabo uwar ‘ya’yana sai in kakkaryaki baras-bas irin yadda ake karya karan raken takanda, ki na ji ko?� (Yana nuna irin baras-bas din da zai yi mata da hannayensa).

“Ashe dama baki da kunya Baffa ya rufe cikin mayafi ya bani, duk wannan sunkuye-sunkuyen kan naki na munafurci ne?�

Tace “oho dai! Dadin ta dai ba cewa akai tilas ka aura ba, tayi aka yi mana dukkanin mu muka amsa, ni banyi nadamar tsohon da aka lika min ba ina gabar kuruciyata sai kai? Ka sani dai ko yau kasuwar ta watse dan-koli ya ci riba, zan kuma iya auren kamar dan ka AMINU wanda yasan darajar aure ya kuma rike ni da mutunci ba kamar kai shanyayyen tso…�.�

Fauuuu! Ya dauketa da mari yace “ni kike gayawa wannan maganar? Idan ba aure ni ba Yayanki bane? Banza gantalalliyar turai dama auren irin ku (kwantan ‘yammata) ai sai mu din. Amma tunda kin ce zaki auri kamar da na, to je ki na sakeki ki auri kamar Aminun in gani, ina kuma jiran katin gayyata…� tana murmushi tana zare shimfidar gadon ta tana cewa “in ma gantalin ne ai kai ka dauren gindin yin sa, da kwabon ka da nairar ka babu ko kwandala ta a ciki?

So what in an sake ni dama banga banbanci ba da wannan zaman mahon da nakeyi, baka san cin mu ba, baka san shan mu ba above all ma bani da hakkin aure ai akuyar daure ce ta samu sake, ba sai gantali ba? Aure kuma da yardar Allah Brigadier zaka sha mamaki, ke Saratou! Hado kayan ki maza-maza mu bar masu gidan su (Ardhullahi-Wasi’a) duniyar Allah ai tana da fadi�.

Har ya kai bakin kofa ba tare da ya kara kulata ba, amma jin abinda tace sai ya komo da baya, ya dubeta sosai da idanuwan shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta

“ta je ina? Sai ki gaya min in ke kika haifeta, ko ke kika kawota gidan?�

Kirjin Anti Saratu ya bada wani irin hargagi. Ta rude ta rikirkice ta kasa cewa komai. Duk wata tsiwa da ta ke ji a dole jikin ta yayi sanyi. Tun zuwan Intisar hannun ta bata kara tunawa cewa ba ita ta haifeta ba.

Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ya kasance Saratu da ke falo ta ji abinda mutumin da ta rika a matsayin mahaifin ta da bata hadashi da kowa a duniya ya fada. Sai ta zube ragwaf a kan gwiwoyin ta ta kasa magana sai hawaye shar-shar! Ke zubar mata.

Bai tsaya sauraron ta ba yayi tsaki ya juya abin shi don kuwa rokon shi take kada ya gayawa Inteesar ba sune iyayen ta na hakika ba. Yayi ficewar sa ba ko waiwaye yana kara jaddada mata kada tayi rabin awa bata bar mai gida ba, ko allurar ta baya so a dakunan sa.

Inteesar tsuma take tamkar mazari ita kadai a falo. Duk hayaniyar da suke akan kunnenta ko kalma daya ba wadda bata ji ba. Cikin dan lokacin zazzabi mai zafi ya rufeta kafafun ta suka kasa daukar nauyin ta, ko wani kwakkwaran motsi ta kasa tamkar sassakakken gunki.

Ba abinda ke ta amo a kwakwalwar ta kamar wai Daddy ya saki Mamarta kuma wai bazata bita ba?

Kwakwalwarta bata fahimci me Daddy ke nufi da “ita ta haifeta ko ita ta kawo ta gidan ba� illa tana tsammanin Daddy na gadarar shine Uban ta kawai, hakannan bata ji irin rokon da Antin ke masa ba don muryar Antin ya dushe gabadaya a lokacin.

Bata gama dawowa hayyacin ta ba sai gani tayi Daddy na (ball) da komi na falon su, yana hada crystal da marble karar babu dadin ji tamkar wani mahaukacin kare. Ya daga t.v da hannu daya ya hada ta da garu, gilassan na kwarara a kasa cewa yake

“ba dai ni na saya ba? To bazaki tsira da komi nawa ba Saratu including ZUCIYA ta mallakin watan ki ce. Cikin jikin ki ma bana so kije ki bawa kamar Aminun! Yadda kuma kika karya zuciyana sai wani ya baki (hundred %). ‘History will Insha-Allah repeat itself� (da yardar Allah tarihi zai maimaita kansa). Ina nan ina zuba idon ganin mijin ki yaro KAMAR AMEENU!!!�

Daga ji zaka san kishi da bakin cikin wannan kalma shi ya fi komi bakan ta mai rai. Gabadaya ya koma tamkar wani ‘lunatic�. Itama Intisar din hankadata ya dinga yi da kafa da hannu har sassan Hajiya. Gidan ba kowa duk suna makaranta.

Hajiya na tsaye a falonta cikin shiga ta alfarma tana saitin eriyar talbijin, ta daure fuska sosai ta nufe su tana tada Inteesar din “haba Alhaji, in taku ta hado ku da Saratu ita Intisar meye laifin ta?�

Hawaye yake sosai yana cewa “kyale ni Nafi, daga ita har uwar ta bakikkirin nake ganin su wallahi. Daga yau zan sallami duk ‘yan aikin gidannan, gata nan (ya nuna Intisar) da ke yashe a kasa cikin yanayin fita hayyaci) ita zata dinga yin komi na gidannan.

Idan kika tausasa mata ban yafe ba, idan kika dai-daita matasayinta da na ‘ya’ya na cikin gidannan Allah ya isa tsakani na da ke! Ki kaita dakin ‘yan aiki yanzu-yanzu ba sai an jima ba.�

Hajiya tayi salati tace “Alhaji duk me yayi zafi haka? Me Intisar din naka tai maka?� Ya ce,

“Ashe yarinyar nan Saratu bata da mutunci, ta dubi tsabar ido na ta zaga da girmana da mutuncina da komi. Wai Saratu ce za ta ce da ni zata auri kamar Aminu? Don ta ga ina bautuwa a kaunar ta da ‘yar ta shine zata farke mun laya aka? Allah ko zumuncin mu da Baffa zai watse bana auren! Ta je ma duk inda zata Umma ta gaida Assha…� yayi sama kamar kububuwa yana ta fadace-fadace tamkar ba Brigadier Bello Makarfi ba, mai sanyin hali kamar ba soja ba, wanda ko hantara wannan bai taba hada shi da iyalin shi ba.

Inteesar tayi tsammanin wannan mutumin da ke tsaye ba Daddyn ta bane wani ne dai mai tsananin kama da shi. Ta kasa yardarwa kanta da gangan cewa wannan juyayyen mutumin Daddy ne! Wani abu mai tsini kamar kibiya ta ji yana sokar ta a kahon zucci, yana keta tsakiyar kirjin ta don bakin-cki, takaici da mamaki.

A hankali taji idanuwanta na rufewa don kansu ba tare da ita din ta san hakan ba. Tun tana ganin dakin dusu-dusu har duhu ya mamayi ganin ta. Bata kara tsinkayar me ke faruwa a duniyar ba.

*****

Ruwan kankara ne ya farkar da ita daga dogon suman da ta yi. A hankali idanuwanta ke washewa tsayin minti goma kamin ta fahimci a dandaryar dakin Dela take kwance (mai aikin Hajiya).
Chapter 47 · 0% Book details