← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 90

Sashe 21

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aminu ya mike ya tura hannuwan shi aljihu, ya dube shi cikin haushi ya ce,

“Kai dai la’ananne ne, kullum kana gindin wadannan miyagun ko? Ko da yake na san ba laifin ka ba ne, ba mamaki kai ma an kai sunan ka wurin mai buzun nan na Makarfi.�

Hajiya ta tuntsire da dariya, amma su yaran hankalin- su bai kai su gane ko da wa yake ba, ya mikawa baby hannu ya ce,

“Come on beautiful baby.� Sai ta saki hannun Faisal ta tafi gare shi cikin yaukin ta na halitta, don wannan kira ne da ba mai yi mata sai Daddyn ta, kira ne da Daddyn ta ke mata.

Ya kalli Hajiya suka kifta ido, (za a yi mugunta kenan), ya dauke ta cancaras kamar ya dau kofin shayi, Hajiyar na cewa,

“Kai dai Yayan kobo ne, kawo min babyn nan, kai Faisal je ka ce masa yana zuwa.�

Ya juya jikinsa a sanyaye cike da rashin jin dadin barin baby tare da su, don azaba tun tana rarrafe Aminu ke gana mata kala-kala, amma ta ki ta gane ta guje shi, sam-sam ba ta da wayo, yanzu ne za a mata abu yanzun ne za ta manta in har ba karatu ba ne.

Aminu ya yi hanyar kicin din Hajiya dauke da baby a kafadun shi ya fiddo markadadden tattasai danye cikin firji ya cika kofi ya bude bakinta ya shiga dura mata bayan ya daura ta a saman deep freezer din tana ihu tana zillo, hawaye ya hade da majina shi ko cewa yake.

“Sha maza beautiful baby, ko kya koyi magana, pepper soup ne.� Sai da ya dure mata tattasan nan duk a cikinta, ya cika ruwan kankara a cup ya sake dura mata, ya wanke mata baki tas, ya sake ta a kasa sai ta fadi talau, ya yi dariya ya kama gabansa.

Faisal ya koma daukar baby, ba kowa a falon sai Hajiyar, ya ce, “Hajiya ina kanwata?�

Ta ce cikin halin ko in kula,

“Nan na ga ta yi hanyar kicin.�

Duk da shekarun Faisal a lokacin ya san mahaifiyarsa bata kaunar Intissar yadda ba ta kaunar mutuwar ta. Ya kan tambayi kansa ko me yarinya karama kamar wannan ke mata? A guje yake kiran Intisar har kicin, abin tausayi, sai ya gan ta kwance bisa tiles din kicin din idanun ta a rufe tana fidda wani irin miyau tsinkakke, ba alamun barci take ko idon ta biyu sai wani irin nannauyan numfashi take a wahale, ya sungume ta ya sa a bayan shi yana gudu har yana faduwa ya nufi sashin Anti Amarya.

Yana kuka yace, ‘Anti Intisar ta mutu! Ban san me ta ci a kicin din Hajiya ba.�

Antin ta amsheta ta tabbatar ba mutuwa ta yi ba, sai dai jikin ta da ya yi wani irin jagab, kamar an yi mata duka. Ta yafa mayafi ta fito ta kira direba ya kai su wani private hospital nan kusa da su.

To likita ya yi wa baby allura ta amayar da tattasai tsurar sa, ya basu gado don ta huta, nan Daddyn ya isko su Aminu na biye da shi, ya tambayi abinda ya faru da Saratun, Antyn na share hawayen da suka cika mata ido ta ce,

‘Oho ni na kasa gane wannan abu! Na ke jin firji ta bude ta sha ruwa kuma ta sha tattasai? Amma a shekarun baby duk da ba ta magana da kowa, ya isa a ce ta san ruwa wallahi, koma wa ya ba ta ai Allah yana gani.�

Aminu ya kau da kai, shi ko Daddy bai ce komai ba, don bai san ma me zai ce din ba. Ya tabbata duk cikin ‘ya’yansa babu mai kin Saratu sai ko uwar su, ita din ma yanzu ba ta nunawa, abin da ya dauka kawai ko dai baby ta dauka lemu ne kawai. Wannan ta wuce.

Rannan direban yara bai zo ba har bakwai da rabi ga shi ranar Litinin ce, Hajiya ta iske Daddy tana ta fada wai Emma bai zo ba yara duk sun matsu su tafi kar a duke su, to saboda baya son mitar ta ya kira Aminu ta wayar hannun shi ya ce ya kai yara makaranta.

Sauran yara na baya, Khalil da Intisar na gaba, kan ka ce me ye wannan fada ya kaure tsakanin Khalil da Intisar wai sai ya biya ta littafin ta da ya cika da zanen biro. Aminu ya cire lafiyayyen hannun shi ji ka ke kau! Ya wanke ta da marin da ba a taba yi mata ba, ya ce,

“Ko uwar ki ba ta isa ta yi surutu ina tuki ba.�

Ta gigice ta sa kuka da karfin gaske, ya ce, ‘Lalala! Ki yi min shiru, shegiyi mai zakin muryar tsiya.� Ba ta yi shirun ba sai ma kara tsananta kukan ta har da ihu, ya kai hannun shi na dama ya ciro ta daga mazaunin ta, na hagun kuwa yana murza steering wheel cikin gwaninta, ya tura ta inda yasa kafafun shi, idan ya taka totur ita ma ya taka ta, duk yaran suka yi tsit kamar ruwa ya cinye su cikin kaduwa.

Faisal kuwa da ba zai iya jurewa ba tuni ya soma yi wa Ya Aminun kuka ya daga Intisar kar ta mutu, sai da suka zo makarantar ya kashe motar, ya juyo ya dube su ya fiddo manyan idanun shi ya ce, ‘In ji wani mai tsautsayi cikin ku ya ce na mari Intisar ko na yi mata wani abu, uhn, sai na babballa yaro, ya kuma yi kwanan store Bismillah.�

Yana fadi yana hada kan Faisal da Bello yana gwarawa don wai su ne manyan munafukai, gaba daya suka sa kuka har wadanda ba a daka ba, ya ce, ‘To ku yi shiru, ai in ba ku fada ba ba zan saku a store ba.�

Duk suka yi shiru, ya ciro ta fuskar nan ta yi suntum da kuka ya zaunar ta cinyar Faisal ya ce, ‘Lashe hawayen ki I said!� Da sauri ta sa harshe tana zukewa. Ya bude masu kofa suka fice, ita ko baby kafa yasa ya cillo ta ya ja motar shi ya tafi.

Ranar wata Alhamis Malamin Islamiyyar su ya zo, duk suka fice har sun fara daukar darasi, ita ko baby ta make a bakin kofa ba ta tafi ba tana so su gama ficewa ta sha majinar ta ta koshi tukun, ta yi can hanyar baskwata ta soma fyace majinar a hannun ta tana lashewa tana kuma zakulo tasono tana dannawa a baki kamar an ce da ita juya can, sai ta hangi Aminu tsaye jikin balcony (baranda) yana zukar sigari abin shi yana danna waya, ta saki baki galala! Don ta sha jin Daddy yana yi wa su Faisal hudubar cewa duk mai shan sigari dan iska ne, kuma cikin su duk wanda ya sha sigari ba shi ba shi. Jikinta ya yi sanyi lumus, yau ga dan iska ta gani a zahiri.

Jikin shi ne ya ba shi wata kila ana kallon shi ya juyo da sauri suka hada ido, ta juya za ta gudu kafin ta yi taku uku ya danko ta ya ce,

‘Wai ke munafuka ko, au majinar taki ki ka zo sha to yau kuwa za ki dandana kudar ki, kin zo ganina ina shan rothman ko?�

Cikin kuka ta ce, ‘Allah ni majina na zo sha.� Iyakar firgita ta firgita da shi ya kama kunnuwanta ya murde da karfi ya manna mata wani azababben mintsini a wuya ta kara tsananta kukanta, ya ce,

‘Ina shan rothman?�

Cikin gigicewa Ta ce, ‘Eh.� Ya shiga daldalle mata baki da yatsun shi biyu, da karfi ta ce, ‘A’a, ban gani ba Ya Aminu.�

Ya sassauta rikon da ya yi mata ya ce,

‘Daga yau na sake ganin ki kina lasar majinar nan sai na yanke hancin kowa ya huta, kazamar banza mai shan majina. Wane yaro ki ka gani yana shan majina a gidan nan ko don ke uwarki ‘yar kauye ce, za ku taru ku mayar mana da gida matattarar ‘yan kauye.�

Ta ce, ‘Allah ba zan sake ba.� Ya sake cewa, ‘Kin gan ni ina shan Rothman?�

Ta ce, ‘Allah ban gani ba.�

Muryar ta har ba ta fita saboda kuka da razana. Ya yi murmushi ya sakar mata kunnen ya ce, ‘Tafi wurin malam.�

Ai tun kafin ya karasa rufe bakinsa har ta kusa kaiwa, ya yi dariya ya shige cikin gida yana baiwa Hajiya labari, a fusace ta ce,

“NI da Allah rabu da ni, tun yaushe na hana ka shan tabar nan, in ba zaka bari don komai ba ai ka bari don lafiyarka, tunda aka fara haka wata ran ai Daddyn da kanshi zai kamaka, na kuma tabbatar maka duk ranar da hakan ta faru ba kai kadai ba har ni uwarka sai mun kasa kurbar ruwa a gidan nan, me ye amfanin taba ga rayuwar dan Musulmi ban da cutarwa, wallahi ko bayan raina ka kara shan taba ban yafe maka ba!.�

Yasa hannu ya dafe kai ya ce, “Haba my dear Mum, ki ji tausayina, ki janye wannan furucin naki a kaina, Aminun ki ne fa, insha Allah daga yau na daina amma ki sa mun albarka.�

Ta yi murmushi ta ce,

“Ai don ka san lagona ne, to Allah ya yi maka albarka.�

Aminu ke koya masu assignment amma baby tana kwance jikin Mamarta ta ki tashi, ta dube ta, ‘Baby yau ba ki da assignment ne?�

Ta ce, ‘Eh.� A dan tsorace don ba ta saba karya ba. Antin ta lura karatun ne yau ba ta so, ta ji ba dadi a ranta, ta shiga daki ta bude jakar ta ta fiddo littafin Maths din ta da yake shi aka fi ba su aikin gida, ta ga aiki na jiya da na yau duk ba ta yi ba, ta fito rike da littafin a hannunta ta ce,

“Babyna, me yasa yau ki ka yi min karya?�
Chapter 21 · 0% Book details