← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 90

Sashe 3

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan rigimar da suka yi Ihsan ta soma yi wa Ameenu korafi da koken su koma gida ta ga iyayenta ta kuma roki gafararsu, tunda shi ba ya son nasa. Shekaru bakwai ta yi tana karatu, shekarun su uku da aure kuma a cikin shekarun tana aiki a asibitin (Baptis Health) da ke South Florida, cikin birnin Miami matsayin karamar likitar zuciya (cardiologist) kuma kwararriya a fannin heart-transplantation

Da fari hankalin Al’ameen ya tashi da wanann sabon abu ko ko ya ce rigima da Ihsan ta kinkimo mishi har ya dinga ganin bekenta, to amma shi ma da ya yi tunani mai kyau sai ya ji shi din ma ba abin da yake so irin dawowar, ya kuma bude ido ya gan shi a gaban Daddy din shi ya ga SARATU-INTISSAR din da ta sa shi barin gida, ko a wanne hali take yanzun? Yaya take gudanar da rayuwarta a hakan? Uwa-uba tausayin Ihsan, yau shekaru goma kenan ba ta kara sa iyayenta a idanunta ba, shi kuma shekaru goma sha biyar kenan sai ko yau da jirgin da suka shigo ya sauke su a birnin Ikko.

Ihsan Abubakar matashiya ce da jin dadi ke boye mata shekaru a kullum, amma a zahiri shekarunta ashirin da tara cif, don dai gajera ce kawai ba a fiya kimanta shekarunta ba, a yayin da Dr. Al’ameen Bello ke da talatin da biyar da wasu ‘yan watanni. Daga Ihsan har Ameenu kowa na ji da kyau, sai dai nesa ba kusa ba Al’ameen ya darawa Ihsan tsari. Kusan kyawun Ihsan ya fi yawa a fuska, amma ba ta da wannan fasalin na ‘ya mace sai ko ‘yar lafiyayyar fuskarta da Ameenu ke matukar so.

Sanye take cikin English wears ruwan hanta riga da wando masu kauri, amma da yake ta baro Miami a yau ta dora bakar after dress kirar Oman a kai, bata da sumar kai mai yawa don haka sau da dama gashin kanta cikin tarin attachement yake.

To yau ma hakan, sai dai ta yane kanta da gyalen abayar yayin da kyawawan tafin kafarta ke sanye cikin wani rantsatstsen ‘high hill shoe� bakin takalmi (mai tsayin dunduniya) mahadin jakarta kirar Japan. In ka dauke zobban diamond kwaya uku da ta yi wa kyawawan yatsunta ado babu komai a hannunta don ‘yar jakarta na hannun Al’ameen ne har suka shiga jirgin da zai kai su Abuja.

A Abuja Al’ameen ya riga Ihsan sauka don ta tsaya make-up dinta da baya karewa. Hannuwan shi duka biyu zube cikin aljihu ya doshi reception wato wajen karbar baki duk da dama shi bai yi tsammanin zuwan wani nashi ba.

Nan ya hango wata mata sanye da malfa mai tsananin kama da matarsa, ko ba a gaya mai ba ya tabbatar Ann ce mahaifiyar Ihsan.

Kallo daya ya yi mata ya dauke kai a ransa ya yi mamakin yadda mahaifiyar Ihsan ta kasance Kirista amma ba ta taba gaya mai ba, domin ya hango cross a sarkar da ke wuyanta.

Har ya yi gaba sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba, ya juyo ya komo inda suke daidai lokacin da Ann ta rungume diyarta suna ta kukan dadi tamkar ba wani sabani da ya faru tsakanin su, sai ya yi fatan hakan ta kasance a gare shi shima.

Ihsan ta saki mahaifiyarta ta yi mata nuni da Al’ameen da ya harde hannuwa bisa kirji yana kallon su kawai ta ce shi ne mijinta Al’ameen.

Duk kin da Ann ke wa auren Ihsan da Al’ameen, amma kwarjini da kamala irin na Al’ameen Bello, ba ta san yaushe ne ta sami kanta a mai mika masa hannu ba, ya mika mata nasa a ransa ko cewa yake wai kakar ‘ya’yana ne wannan Inyamurar kuma suruka ta ke mika min hannu mu gaisa kamar a turai? DA YA SANI� Wai me yasa har kullum yake gamuwa da DA NA SANI MARA AMFANI NE a rayuwarsa? To haka suka gaggaisa da sauran ‘yan uwanta ma gaisuwar hand shake fuskar shi ba annuri sam-sam sun nemi da ya bi su gidan su a Garki, domin ya gana da mahaifinta inda shi kuma ya nuna uzrinsa yana cike da dokin ganin nasa iyayen shima. Sai dai in ya huta ita ma Ihsan din ta huta zai zo su gaisa da shi din, ya kuma dauki Ihsan din zuwa gidan iyayen shi.

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one

*@Takori*

Page2ï¸âƒ£

Abuja

Lahadi ce sassanya kuma ranar hutun ma’aikata, cikin wani katafaren gida a unguwar Atiku Abubakar Crescent. Tamkar sauran karshen satittika tsohon Brigadier Bello Makarfi, da uwar gidansa Haj. Nafi, ranar hutu ce a gare su. A irin wannan Lahadin ba sa zuwa ko’ina su kan kasance ne cikin ‘ya’yan su a yinin ranar baki daya tare da tattauna matsalolinsu na rayuwa musamman na karatu da hanyoyin warware su.

To a yau ma suna gida, kananan ‘ya’yan su na baya-baya, wato Idris, Furkan da Khalil da ke karatu a jami’ar Gwagwalada duk suna tare da su a wannan satin suna hutu in ka dauke manyan ‘ya’yan da ke kudu.

Daddy, kamar yadda dukkan al’aummar da wata alaka ta jinni ta hada su da shi ke kiransa, kwance yake a doguwar kujerar da ke main falon shi yana magana da dansa na biyar wato Yasir da ke Enugu yana aiki ta wayar landline da ke kife bisa ruwan cikinsa inda yake tambayarsa laifin da ya yi masu suka ki zuwa gida hutun karshen shekara, kamar yadda suka saba.

Amsar da Yasir ya ba shi yasa jikinsa ya yi sanyi, to amma ya kasa tuno komai bai kuma damu da ya tuna din ba. Don Yasir ce wa ya yi “Daddy, ba za mu iya sake zuwa gida ba gaskiya, alhalin muna ganin irin rayuwar da Inteesar, ke yi ba tare da ta yi maku laifin komai ba, in ma laifin ta yi pls Daddy ba kwa afuwa? Cikin mu wa aka taba yi wa irin wannan horon ko don ita tana Mace? Bayan kuma an san cewa ita mace a komai mai rauni ce? Ko ko don Aunty Saratu ba ta gidan saboda Allah Daddy abin da Hajiyarmu ke yi ya yi daidai kenan? Ba mu da idon da za mu dubi Intisar alhalin tana irin wannan rayuwar a hannun mahaifiyarmu. Don haka Daddy, ba za mu iya zuwa gidan nan ba in har ba rayuwar gidan ce ta canza ba� za mu ci gaba da zama a nan inda muke har sai abin da Allah ya tsara…�

Daddyn na iya jiyo kukan da Yasir ya saka masa a wayar da girmansa da mukaminsa na aiki da komai. Shi kansa baya ce ga hakikanin laifin da Saratu da Saratu su kai masa ba yake ganin su bakikkirin. Kafin ya yanke tunanin da ke addabar kwakwalwarsa ya jiyo tashin ihu da iface-ifacen jama’ar gidan daga waje, haka daga sassan Hajiya, idan har ba kuskure kunnuwansa suka jiyo masa ba ya ji tamkar muryar autansa Khalil na cewa,

“Ya Aminu tun yaushe ku ka sauka? Me yasa ba ka gaya mana za ka dawo ba ai da mun zo airport taryon ka.� Sai kuma kukan Hajiya da karfi Ameenun na lallashin ta cikin tattausan harshensa. Sai kuma gaba daya lafiyayyar muryar Al’ameen din da har abada ke yi mai yawo a kwanya na tambayar.

‘‘Ina Daddy na?�

Shidewa ya yi na wucin-gadi, kafin ya tabbatar lallai Al’ameen ne ya yi masu dirar mikiya yau a gidan. Lallai Allah Sami’ud du’a’e ne, mai amsawa bawa roko a sanda ya so. Bai kuma tabbatar da lallai Al’ameen din ne ba sai da ya ji shi kwance cikin jikinsa yana kira cikin muryar nadama.

“Daddy, I know that I hurt you� I hurt you, tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanka kada ka taba yafe mini…�

Amma sai Daddy din ya sanya tafin hannunshi ya rufe masa baki, wato baya son jin abin da yake fadi. Al’ameen gaba daya ya rikice, ya rude ya kara tsanar kansa a karo na biyu da tunanin wace irin ukuba ya haifar wa iyayen shi?

Daddyn ya hade hannun Al’ameen mai taushi cikin nasa yana kara damkewa ya ce,

“Burina kadai ka dawo gare ni Al’ameen, ganin ka na rana daya ya shafe bakin cikin da rashin ka ya haifar shekaru goma sha biyar.�

A kullum dama Bello Makarfi, mutum ne mai sanyi kamar ba tsohon soja ba, balle ga iyalinsa, kowanne irin laifi suka yi masa da sun ba shi hakuri shi kenan. Gani yake in bai tausasa masu ba, ya fadi ya mutu shi kenan fa ba za su kuma samun wannan kaunar ta uba ba. Sai ya sake cewa.

“Al’ameen idan har ka dawo ne din-din-din, ni har kullum ai mai afuwa ne.�

Al’ameen yasa gwiwoyinsa a kasa ya kama hannuwan mahaifinsa duk biyun ya ce, ‘Daddy zan kasance nan tare da ku muddin rayuwata. Ni kaina nadamar abinda na aikata ne can baya ga diyar ka Intisar, shin za ka roke ta ta yafe min tunda na san yanzu ta mallaki hankalin kanta? Ban ki dawowa ba sai don ji na yi na tsani kaina, ina ganin ba za ka taba iya yafe min ba, sai ko shaidan da ke kara ingiza zuciyata ga nisantar ku. A ganina ta hakan ne kurum na ke da amfani. Daga ni har Ihsan ba za mu kuma barin garin nan na tsahon lokaci ba.�

Duk sai suka yi murmushi. To haka wannan family ya yi wunin farin ciki a ranar kamar yadda ya saba a baya. Sai Al’ameen ya ji ranar tamkar renaku irin na baya, masu cike da al’amuran da har abada ba zai manta ba.

Bai zaci kuma irin wannan yafiyar da sauri haka daga Daddyn shi ba, don haka yana cike da matsanancin farin ciki a watan Safar. Wata mai dumbin tarihi a gare sa. Watan da ya bude wata sabuwar rayuwar da kuma wasu bakin al’amura masu ban mamaki (At his thirtieth) bayan wanda ya wuce cikin (twentieth) din shi. Ashe in da ranka za ka ga da yawa, ashe in ba ka mutu ba baka kare rayuwa ba, wai me yasa rayuwar take da ban mamaki ne?
Chapter 3 · 0% Book details