Sashe 31
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kyar ta lallabi Dr. Alhassan amma ya ce duk san da suke neman taimako kan karatun Saratu a shirye suke da su taimaka ta kowanne bangare. Har adires din sa ya basu na Riyadh, inda yake aiki da Turkey kasar haihuwar shi inda yake zaune da iyalin shi. Ga yadda Antin ta karanci zuciyar Dr. Alhassan ma kadai ta fahimci matukar kaunar Saratu yake, kauna ta hakika kuwa, ba ta malami da dalibi ba.
Bello ya zo ya yi week-end a Abuja wannan watan. Ya ba baby wasikar Faisal da ya ce shima ta zo mai ne daga post. Da ta ki karantawa, sai da ta ga bacin ran mamar ta tukunna.
“To Mama dauko min gilas dina.� Hajiya Saratu ta yi dariya ganin yadda ta zobara baki gaba (hakan take yi idan Faisal ya ba ta haushi), ta je ta dauko mata gilashin da kanta, ta sa hankici mai tsabta ta goge mata kwarmin ‘yan lumasassun idanun ta, kana gilashin, kafin ta manna mata farin siririn medical glass din ta.
Broken heart!
Na sani, duk bayanin da zan yi ba zai gamsar da ke ba Intisar, amma kafin nan, ina farawa da baki hakuri, Allah shi ne shaida, na fi ki damuwa da rashin komawar ki karatu.
Ni kaina abubuwan da Hajiyar mu ke yi bana son su, to amma kin san ba yadda zan yi, tunda Hajiya mahaifiyata ce. A da ban yi niyyar gaya miki ba, sai don gani da na yi kin yi min wani fassara na daban a zuciyar ki. I try my best (na yi iya kokarina) in samu ko da takardar motar Daddy guda daya in saida, ki koma makaranta. Hajiya ta hana, har tana ikirarin tsine mini, idan na sake sa baki kan harkar karatun ki.
Intisar abin da ban taba tsammani ba (ko a mafarki) wai Baby ki ka ki saurarena a kan wani (matter) da ki ka san ba ni da iko. Amma kin san Allah ko da zan yi yawo ‘in nude� (tsirara) ne, sati mai zuwa za ki koma makaranta.
Daga Yayan da baya da laifi.
Ta lumshe ido abin tausayi, tausayin kanta ne ko ko Ya Faisal? Ita kadai za ta iya kiyasta halin kuncin da zuciyar Faisal ke ciki a yanzun kan wannan al’amari. Ta sani idan da abin da Faisal ya ki jini a rayuwarsa ba kuma zai iya jurar sa ba. To bacin ranta ne.
Ta san a duniya daga Daddy, Mamar ta, sai Ya Faisal a masu kaunar ta. Ta kai duban ta ga Aunty Saratu da ta yi tagumi tana kallon ta, ta yi murmushin karfin hali.
“Kin ji abin da Ya Faisal ya ce? Cewa ya yi ko da a ce zai yi yawo tsirara ne, wai sati mai zuwa zan koma Riyadh, kuma wai kin ji ashe Hajiya ce ta hana su ba mu komai na gidan nan? Shin Mama me na yi wa Hajiyar su Khalil ne ta tsane ni? Me na ke mata? Kin san Allah tunda nake a rayuwata, ban taba gaishe ta ta amsa ba, ban taba shiga sashin ta ba ta zage ni ba, ban�..� Sai ta sa kuka.
Aunty Saratu ta rasa ma me za ta ce? Tunani goma da ashirin ya yi mata rubdugu. Me za ta ce da Saratu wanda ya jawo mata kiyayyar Hajiya Nafi? Ta tsane ta don tsinto ta aka yi? Ta tsane ta don kaunar da Daddy ke mata sama da ‘ya’yanta? Ina! Ko za a daura mata bindiga a wuya ba za ta taba furtawa Saratu ba ita ta haife ta ba! Ba tun yau ba ta san Saratu tana da zuciya a kan komai.
Da suke yara in Khalil ya ba ta abu, daga baya ya dawo ya ce ta ba shi, sai ta cilla masa ta ce, ‘GA tsiyar ka nan. Ni ma Allah zai ba ni.�
Ba kuma za ta kara duban abin ba ko da ya yar daga baya balle ta dauka.
To haka abin yake har girmanta. Duk wani abu da ta san zai taba mutuncin ta tana gudun shi tana kyamar shi tana yin nesa da shi balle rashin usli? Ta girgiza kai cikin jin wata sabuwar kaunar yarinyar da ta ratsa ta, ta kada harshe ta ce,
‘Saratu in Maman Khalil na bada rahma, don Allah in ta zo kan ki kar ta baki, in ce ko karshen ta kenan?� Ta yi murmushi tana share idon ta da hankici ta ce, “Karshen ta kenan fa Mamar mu.�
Ranar Juma’a bayan an sauko sallar Juma’a, Faisal ya iso Abuja kamar yadda ya saba. Sanye yake cikin ‘yar ciki da wando ga kuma babbar riga ya ratayo a kafadun shi na babbar shadda Wagambari ruwan sararin sama mai haske (sky blue) wadda ta taimaka ainun wurin kara fiddo gogaggiyar choculate colour fatar shi mai sheki. Duk ‘ya’yan Hajiya Nafi haka suke kamar half cast kasancewarta usli Shuwa ce. Kira kamar well-fed Americans ga tsayi ga zati tamkar Babansu.
To shi Faisal karan hancinsa har wani rankwafawa ya yi kadan saboda tsayi. Kowannensu ya mallaki diggunan beauty point biyu in ka dauke Al’ameen mai guda daya a gefen kuncin sa na hagu kawai kuma shi kadai ne da cleabe wannan dan digon na tsakiyar haba yayin magana ko murmsuhi. Faisal akwai son turare (5,000 Doller), inda duk ya yi za ka ji daddadan kamshin na bibiyar shi. To haka yau ma.
Ya kalmashe cikin ‘yar lallausar kujerar computer Intissar yana kallon ta sai fama take da dogon gashinta mai santsi, ita a la dole sai ta yi kalba, ta yi ya warware, ta sa roba ta matse bakin ya sabule kamar ba ta san Allah ya yi halittar shi a dakinta ba ma.
Ba don ta girma ba, da ya amshe ta, don wannan aikin shi ne, tun tana goye, sai da ta kai aji uku shi da kansa ya bari. Ko ta yi ta yi ya gyara mata sai ya ki, ya ce shekarun ta sha biyu ta gyara abun ta. Shi kadai ya san me yake ji tun lokacin game da Baby. To balle a yanzun da ta zama cikakkar budurwa ‘yar sha bakwai, komai ya ji Tubarakallah, komai na ta ya kai ya kawo, ya yi wa fuska da zubin halittar ta daidai.
Ga ta nan dai tamkar kwalbar nan ta coca-cola mai sanya kan duk wani hadadden namiji juyawa.
Kan shi kuwa ke juyawan ta ko’ina, wani irin abu ne ke ratsawa tun daga kwakwalwar shi har yatsan kafar shi game da Saratu a yau, barin yanzun da take sanye cikin wata jar matsatstsiyar riga fara sol da ratsin baki-baki samfurin (Dolce & Gabbana) da bakin dogon siket din jeans, to amma wannan kanwarsa ce fa da suke uba daya? Sai ya yi saurin korar shaidan a zuciyar shi ya rintse ido yana jan Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, ni’imal maula wa ni’imal naseer, allahumma ajirni fi musibati hazihi wakhlif ni khairan min ha� har ya samu hakan da zuciyar shi ke yi ya lafa.
How much do you like this story?
5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page6ï¸âƒ£
Daidai lokacin da Anti ta turo kofar ta shigo dauke da jug cike da tatattun ‘ya’yan itacen tuffah da tambulan mai garai-garai. Ya mike ya karbe ta, ta tsiyaya masa ya sha suna gaisawa ta ce, “Bayerabe saukar yasuhe?�
Ya yi dariyar da ya lotsa beauty point din shi, ‘Ke ma Anty tsokanar baby za ki lankaya min?�
Ta ce, ‘ina suka yi posting din ka NYSC?�
Ya ce, ‘Ai ni na shiga uku da kasar Yarabawa, nan Ilorin din suka bar ni.�
Ta kyalkyale da dariya nan suka shiga hirar makaranta. Ya ce, ‘Aunty gobe fa Intisar za ta koma, ga bisa din ta na amso, yau ko darajar kallo ban samu daga Intisar dina ba, duba ki ga yau ko gaisuwa babu? Ni na rasa me kuma zan ce da Baby ta fahimci ba ni da laifi?�
Yanayin yadda ya yi maganar ya bala’in ba ta tausayi, ta kai idon ta ga stool din da Saratu ke zaune tana ta aikin kalbar ta.
“Wai da gaske Saratu ba ki gaishe shi ba?�
Ta saki jelar hannunta, ta juyo kadan ta cira lumsassun idanun ta a gicciye ta zube su a kan shi, cikin sassanyar muryarta ta ce,
‘Ina wuni ya Faisal?�
Ji ya yi tamkar ta ja shi da wutar lantarki, abin da bai taba ji ba a rayuwar shi. Gaba daya ya karasa kidimewa, kwayar idon shi na neman bacewa, ya yi kokarin saisaita tunanin shi ko don saboda Anti da ta kafa masu ido, cikin jarumtaka amma da kyar sautin ya fito daga makoshin sa da ya bushe rayas, ya ce, “Ba na amsawa, alhalin sai da na roka?�
Ta yi murmushi kawai cikin halin ko in kula, ta juya ta ci gaba da kalbar ta. Anti ta yi mata fada sosai amma ba ta ce ko kanzil ba. Ta samu gefen gadon Intisar din ta zauna ta ce,
‘Maganar tafiyar Intisar Riyadh a gobe, ina ganin a bar ta kawai Faisal.�
Maganar ta yi mai kama da saukar kibiya a kahon zuciyar dan adam, duk gwiwoyin sa suka yi sanyi, ya yi dagwalo abin tausayi, a ransa ko cewa yake me zai yi ya farantawa wadannan murdaddun uwa da ‘ya?
Ta ce, “Da farko dai ina son sanin inda ka samo million biyu Faisal?�
Faisal bai iya karya ba, kazalika duk ‘ya’yan Brigadier.
‘Hajiya ce ta ba ni in kai mata banki, ni kuma na ga da a kai kudi a aje a banki hakan nan kawai, ba gara na maida Baby makaranta da su ba?�
Aunty Saratu ta yi murmushi, yau kam ta kara tabbatarwa kanta Faisal yaro ne danye da gigin kuruciya ke diba,
“Yanzu saboda Allah Faisal, idan ta je banki daukar kudin ta, ta tarar baka kai ba, me mahaifiyar ka za ta dauke ka?