← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 90

Sashe 56

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi bai guji tashin hankalin da zai gani daga Hajiyar ba ya furta yana sonta? Koda yake yana tsammanin tsoro ne ko tausayin Ihsan ya sata furta hakan. Bai sani ba, ta fadi ne heart and soul (baka da zuci).

Ya juya ya dubi barin da Ihsan ke kwance, shi din ma tausayinta ya kamashi. Rana daya tak tashin hankalin daya jefata ciki ya ramar da ita. Barci take amma ga busassun hawaye nan a gefen fuskarta.

Tun safe bakinta ko ruwa bai gani ba balle abinci, gara shi ya samu yayi karin kumallo mai kyau. Ya nemi zuciyarsa shawarar abinyi? Ya tabbata in har za su cigaba da rayuwar aure da Ihsan dole hakkinta ya kamashi, domin zuciyar bazata taba iya wannan adalcin ba, na son wata diya mace a yanzu bayan Halimah, (Intisar diyar Anti Amarya).

Shawara ta karshe da ya yanke da zuciyarshi shine na ya rabu da Ihsan taje ko Allah zai hadata da mai sonta fiye da shi, ta kuma zauna da uwarta lafiya, shima ya sami saukin matsalolinshi.

Ya zuro kafafunshi kasa a hankali ya janyo lokar gilashin da ke jikin gadon ya fiddo wani dan (memo) da yake amfani don kananan rubuce-rubuce, ya zari biro ya daura bisa.

Kamar an ce da Ihsan ta bude idonta, a hankali ta bude ido ta dubeshi ta mike taga rubutu yake cikin wannan talatainin dare, ya rubuta sallama kenan ta fizge biron tasa kuka.

Ta san ba abinda zai rubuta a dai-dai wannan lokacin in banda saki agareta, don yana ganin hakan shine kadai hanyar samuwar kwanciyar hankalinsa ya samu ya auri wadda yake so. Ta kifa kai bisa cinyoyinsa to shiga rera kuka mai karya zuciya.

Yayi shiru yana kallon ‘ceiling� shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyar nan tashi mai cike taf da rudani. Ihsan ta san Aminunta, ta san tausayinshi da jin kai. Yana iya fasa komi don tausayi da jin kai. Ta sauka daga gadon gaba daya ta durkusa a gaban shi tana kuka hawayenta masu dumi na diga bisa farar kafarshi, tace a cikin muryar kuka

“Wallahi Aminu in ka sake ni na gwammace in kashe kaina in huta, don bazan iya rayuwar ba. Tun da har ina son ka Al’ameen akan me bazan so abinda kake so ba, ko mene ne shi balle kanwarka ta da, Intisar?�

Ta dago ta dibeshi cikin ido, babu komi ciki kwayar idonta face gesture (motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya) ta ce,

“Al’ameen ka tuna son Saratu ne fa ya kwantar da kai kamar ba zaka rayu ba, baka tunanin nima in na rasaka ba mamaki irin halin da zan tsinci kaina ciki kennan? Zuciyarka ce ke ciwon da har abada bazaka warke ba saboda tunanin ka rasa wadda kake so. Imagine yadda kake jin Saratu a rai haka nima da baka so nake jin ka.

Na jure huldar ka da mata bila-adadin a Miami, akan me bazan iya jure wannan kalilan ba? Don mace daya? Ni dai ko ukku zaka karo in har zaka barni a matsayinda nake, to zan iya jurewa. Abinda ma nayi dazu wallahi zuciyace ta ciwo ni, don ina ganin Babana da ya haifeni bai damu da farin-ciki na ba.

Amma yanzu na gane ‘So daga Allah ne�, babu kuma wani abin halitta da ya isa yayi yadda yaga dama da shi sai ko Ubangijin daya assasa mana shi a ruhi, don haka bana kishin son da kake wa kanwarka illa in roki Allah nima ya sammin ko gutsire ne daga cikin wannan son na Intissar a zuciyarka Ameenu.�

Ya kai hannu ya dagota daga durkuson da tayi bisa kafafunshi ya zaunar ta gefen shi ya ce, “Ihsan ba haka bane, ba wai bana son ki ne ba, bana sonki zan aureki? Illah don dukkanmu mu samu kwanciyar hankali.

Ki diba kiga tun dawowarmu gida muke cikin matsala, ke matsalata da ke na farko Babar ki bata sona.

Na biyu kina da azababben kishi. Irin rotsen da kikewa mata a turai a kaina yana tsoratani, kar in hadaki da yarinyar mutane ki kashe musu ‘ya ni kuma bazan juri wannan ba, iyayenmu ma bazasu yarda ba, bayan haka ma nasan Saratu akan haukar da taga kina yi ne ta furta abinda ta ce.

Ba abinda zai sa in hakura da Intisar yadda kema bazaki iya hakura da ni ba, ba yin kaina ne ba wallahi daga Allah ne. Kiyi hakuri I don’t meant 2 hurt u amma ko daya ban taba tunanin akwai macen da zan so ba haka a rayuwata har muka dawo.

Tun ganina na farko da ita ban kara tunanin kowa ba, ban kara tunanin komi ba sai ita, ban kara dubar wata mace da sunan so ba sai ita. To mai wannan son idan ya sami abin nan da yakeso Ihsan ina zai iya adalci? In zo Ubangiji ya azabtar dani kan danne maki hakkoki? I’m sorry to say, ko a yanzu bana jin zan sake samun nutsuwa ban sami Intisar ba, ina tsoron danne maki hakokki da ke kaina, don haka kiyi hakuri Ihsan mu rabu, don hakan shine kadai hanyar samuwar peace of mind na kowannenmu, watakila hakan na nufin wani kebantaccen al’amari garemu duka? Sai kiga Allah ya musanya maki da mafi alkhairi na.�

Ihsan kuka take tukuru, ba abinda take fadi a zuciyarta face la’ana da Allah ya isa ga duk ma wata mace mai sunayennan uku: Saratu, Intisar da Fatima. Tsakaninta da Intissar Li’ilafi dubune Allah ya isa kwando-kwando. Cikin dan lokaci duk ta mallake mata zuciyar miji tun kamin ya aure ta, Allah sarki! To ina ga ta shigo gidan?

Ashe lokaci yazo da zata koma gefen Aminu tayi kallon rayuwarshi da wata? Ita kuma haka Allah yaga dama da ita? To amma yaya zatayi, tunda ta amince son shi take da zuciya daya. Ta tsinewa kasar haihuwarta da tayi mata wannan cin amana. Inama batace su dawo Nigeria ba! Shin a duniya zata ki wani dan adam kamar yadda ta tsani Saratu-Intisar?

Ta tsani sunan, bata son ji, to amma me? In har da gaske tana son Al’ameen Bello, kenan dole ta tursasawa zuciyarta kaunar Saratu Bello? Tunda ta rigaya ta zamo wani bangare na gangar jiki, Jinin jiki, ruhi da kalbin Al’ameen?

Sai ta matsa sannu a hankali ta kara shigewa jikin Al’ameen kamar yadda yake a al’adarta, tamkar magen da ke jin sanyi, kanta ta kwantar bisa kafadunshi, cikin low and weak voice (mara amo kuma rarraunar murya) tace

“Aminu, ni fa na amince ina sonka, to akan me bazan so abinda kake so ba? Na rantse da Allah na amince ma auren Intisar da zuciya daya, ni ce ma zan je in rarrasheta, tunda akaina tace ta fasa aurenka.

Zan kuma yi kokarin danne wannan kishin da baka so, in kuma maganar Ann ne Allah ta saduda don ita tace in je in yi jiyyar ka a asibiti, na baka hakuri ta gane batayi dai-dai ba, don haka ka fidda shakku akan mu, don ta adalci ai ni ce mai karfafaka da kayi, kuma hakkina ne in shiga yi maka addu’ar yin adalci a tsakaninmu.

With my 100% go ahead (da goyon bayana dari bisa dari) ka je ka rarrashi Intissar ku shirya, kuma kada ka kara marar mun (little sister) na Al’ameen bana so..� da haka ta juya akalar hirar ga wadda yafi so suyi, tun suna Miami.

Tuni Al’ameen ya mance da duk wata damuwa da yake ciki, kuma hakika sunyi missing (kewar) junansu ba kadan ba, tun ranar da suka baro Miami basu kara samun kwanciyar hankali ba.

Don haka kowanensu cike yake da kishirwar dan’uwansa sun ma mance da matsalar data shiga tsakaninsu a baya. Sai Al’ameen yaji ranar tamkar irin renakun amarcinsu a beaches da resorts din Miami cikin bikini. Daga baya ma tausayi Ihsan ya rika ji, da yadda yaga jikinta na rawa, ya dubi irin cuzgunawa da maganganun soyayyarshi da ya yaba mata yanzun amma bata damu ba, burinta kadai ta nuna mishi kauna.

Sai ya janyo matarshi shima aka barje, ya kuma alkawartama ranshi ko ya samu Intisar ko bai samu ba, ba zai taba wulakanta ta ba, don ya amince Ihsan mai kaunar shi ce tsakani da Allah ba don wata tsiya daya mallaka ba, mai kuma kaunar duk abinda yake so.

A washegari wayar Ann ce ta fara tada ita daga barci, ta gode Allah Al’amin din ya shiga wanka tana cewa “Hello� Ann to shiga zaginta da cin mutunci na fitar hankali ta ce,

“kuma kin bani kunya Ihsan, mace kamarki, da gata da ilmi da aji ta dinga bin namiji daya yana garata kamar gare-gare abin wasan yara?

Wallahi kin zubar da mutuncinki, kamar yau ne ina nan a zaune ranar daya wulakantoki da kafarki zaki nemeni tunda baki sayawa kanki darajjah ba, ana nema a siyo miki kina watsarwa.� Ta ce,

“To Ann, ya na iya? Ina sonshi, ya zanyi?�

Ta kara kular da Ann to kwantsama mata ashariya ta ce,

“Son banza? Idan so cuta ne shi hakuri ba magani bane, har wata tsiyace Aminu Bello? Yana likita kina likita ki tsaya yana kada miki bindi?� Ta ce “lala! Ann, Aminu fa Malami na ne, ko a (ST. Bathalomew), daga gareshi na soma koyon psychology da psychiatry bafa wai likitan kwakwalwa ne kawai ba, koko wanda za’ace ga iyakacin field din shi kamar ni ba Malami ne a jami’o’in Miami. Kina ganinshi haka dan yaro Allah ilimin shi ya zarce tunani.�

Haushi ya ishi Ann, Ihsan ta yi nisa bazata taba waiwayowa ba. Luv is overall! Ta ja dogon tsaki ta ce,

“Kin yi asara dai, banza.�

A lokacin yana tsaye ya sakarwa kanshi shower amma bugun da zuciyarshi keyi ya tsananta, zafin da ke azalzalar kirjin shi ke neman kayas da shi, sai a lokacin ya tuna rabon da ya sha magungunan shi tun safiyar jiya.
Chapter 56 · 0% Book details