← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 90

Sashe 42

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka yake (speading) har suka fice jihar Neja ba wanda yace da dan uwan sa uffan, ya mika hannu ya karo karfin na’urar sanyaya mota domin Faisal Allah ya halicce shi mutum ne mai son ya ji shi jike cikin raba, ko kadan bai son zafi don haka fatar shi har wani santsi take irin na mazauna kasar sanyi nan ko tsabar hutu ne kawai, ya danna kaset na wakar Sani Aliyu ta (Shehu Kangiwa Jagoran Jihar Sokoto) yana kada kai cikin nishadi, yana rangaji da dogon wuyan shi yana buga sitiyarin da hannun shi daya, dayan ko yana cigaba da tukin sa hankali kwance yana bin wakar da ‘rhythm� din da mawakin yayi amfani sak.

Inteesar ta kama kanta da hannu bibbiyu, tuni kan ta ya soma sarawa, ta tsani ‘melody� na wannan wakar domin ciwon kai yake haifar mata ba tun yau ba, ta sha gayawa Faisal duk cikin kasusuwansa ba wanda ta tsana irin wannan kaset din, tun kuma daga ranar bai kara sawa ba, to yau ko don yana jin haushin ta ne? Oho! Sai ta kwantar da kanta cikin cinyoyin ta tayi shiru, kanta na cigaba da sarawa.

Sun yi nisa sosai kuma ya gyara murya ya kure sautin sosai ta yadda su Goggo da ke baya ba zasu iya jin me yake cewa ba yace

“wayyo Ronke, nayi missing dinki amma ‘by the way, gobe I’yanzu da yardan Allah ina Ilorin� tayi tsaki baya ga wani tukuki daya zo ya tokareta a kahon zucci, ashe ma kabila ce Yayan da bata hada shi da kowa a duniya zai auro masu?

Tuni idanin ta suka cicciko da kwalla, ta dago ta dubeshi da wutsiyar ido kana ta maida duban ta a tsirrai dake tsere a gefen titi tace.

“Ai sai ka aje mu, ka koma can garin naku wajen Rakiyar tunda kuwa kuna wanka tare ba dole kayi kewar ta ba?�

Yayi dariya sosai sabida Rakiyar da tace ya bala’in bashi dariya yace “ke Sis wanka da Ronke shine ya dameki, ni ko kyakkyawar fuskar ta nake kewa, da kissable-lips dinta, gata da iya dressing dan kuwa shigarta tana burgeni� ta kuwa shaka, ta kule ta haye suntum, fiye da tsammanin sa ko numfashi da kyar take furzarwa, wai a gaban ta? Ya Faisal ke baro wannan kazamar magana? Amma Allah wadaran wannan Ronke data gurbata mata tarbiyyar dan’uwa.

Shi ko Faisal ko a jikin sa, har wani lumlum yake da ido wai yana tunanin Ronke.

Basu bata lokaci ba a Makarfi suka karbi sakon su suka fito sai ta bude kofar baya ta kame abinta domin bata son kuma jin zancen wofinnan na Ronke. Faisal ko ya kudure zancen Ronke yanzu ya fara, ya kai hannu ya shafi kyakkyawan saisayen kanshi zuwa dokin wuyanshi, ya dubeta idanuwan shi sunyi kasa sosai kaman suna neman rufewa don kansu yace “nayi maki kama da Ado direba ne?

Allah ko Ronke dana ke mutuwar so bata isa ta kame a ‘owner-side� in tukata ba, Allah wallahi kuwa baki isa ba don haka cikin biyu dole zaki zabi daya.

Ko dai ki koma gidan tsoffin da kika fito, ko kuma ki komo mazaunin mai zaman banza don kowa ya ganki ya san zaman banza kike� sai ta gyada kai kamar kadangaruwa, zuciyar nan ba sai an tona ba don takaici, ta fito ta banka kofa ta fada gidan.

Goggo na sharar tsakar gidan da yayi kura futuk sabida kwankin da sukai basa nan ta ganta ta jawo kujera ‘yar tsugune ta zauna daga can gefe tana cika tana batsewa, kiris take jira ta fashe tace “ke lafiya? Me kuke jira tun dazun baku tafi ba, anya ‘ya’yan nan kuna jiyewa kanku tafiyar daren nan da ake jiye maku?�

Tace “a’ah Goggo ba laifina bane, Ya Faisal ne yace in dawo a bani kudin mota in je ni tasha in shiga motar kasuwa� Goggo ta ce “akan wane dalili? Ki ga mun dan nema, bari inje In tadda shi� taja mayafin ta data rataye a jikin kyaure ko tsayawa yafawa bata yi ba tayi waje.

Kafar sa daya cikin motar daya a waje yana bin wakar Hassan Sarkin Dogarai ta Dacta Mamman Shata, don shi Faisal wadannan wakokin namu na gargajiya sune (hobby) din shi, ya kan ce yakan tsinci kansa cikin nishadi a duk lokacinda yake sauraron su, musamman cikin halin kunci, damuwa, confusion, ko a yayin da ya rasa sanin hakikanin abinda ke damun zuciyar sa.

Goggo ta tsaya a kan shi na ‘yan dakiku ba tare da ya sani ba, ta nazarci abubuwa masu dama a tare da shi cikin ‘yan dakikai, sai ta koma lallashi tamkar mai magana da yaro karami ta ce

“wane irin neman magane ne wannan Faisal, wai maiyasa kuke hakane kai da ‘yar kanwallen kuma ai sai kowa yayi maku dariya, na dauka tun jiya zancen ya mutu? Ban san ka da riko maras dalili ba.�

Ya rage sautin radiyon yace “sai ki tambayeta dalilin ta na kamewa a baya in tukata, an ce da ita ni direban gidan su ne?�

Goggo Jummai tayi dariya irin tasu ta manya, amma zuciyar ta tayi nauyi, har yaushe zasu dauwama suna boyewa jinin su da sauran jama’ar dake tare da su wannan boyayyen sirri, musamman yanzun data fahimci yana neman zama cutuwa ko kwara ga Faisal da ita kanta Intissar? Har yaushe za’a dauwama a hakan? Ko makaho ya shafa idanun su zai bada tabbacin soyayya suke su kan su basu sani ba.

Ita kam tana ganin da Bello yayi tunani da bai dauki matakin boye wannan al’amari ga kowa ba tunda ko watarana, Saratu za tayi aure, zancen duniya baya taba boyuwa koda kuwa a karkashin gado aka sanya shi.

Auren daya cikin ‘ya’yan shi shine gata na karshe da zai yiwa rayuwar yarinyar in har kaunar da yake ikirarin yi mata ta gaskiya ce.

Su kadai suka san asalin ta suka san ciwon ta duk tabon dake jikin ta baza su taba kin ta ba, to boyon na mene ne? Idan babu wannan akwai mutuwa, zai iya mutuwa a sanda komi zai bayyana garesu suzo suna cewa ashe da bai mutu ba da bazasu sani ba ina amfanin haka?

Ita kadai take tunanin ta, tama mance a inda take tsaye, da wadanda take tare da su, duk suka dubeta, kamin Intisar din ta kai hannu ta bude murfin kofar bayan motar, karar kofar ne ya maido ta hankalin ta ta dubeta tace “a’ah, shiga gaban ku tafi� ta dubi Faisal tayi murmushi tace

“Da abokan wasa kuke sai ince son junan ku kuke, amma duk wannan ce-ce-ku-ce banga dalilin sa ba, sai aka ce wani abu zai ragu a jikin ka don Saratu ta zauna a bayan mota ka tukata?�

Yayi saurin cewa “Allah Ya so ba su din bane, ko su din ne Allah Goggo ban ga me zan ci da wannan kodaddiyar yarinyar ba�.

Intisar ta kai hannu a hankali ta shafo dogon karan hancin ta, ta kare masa kallo tsaf cikin ‘yan dakiku, ta so ace akwai makusa tattare da Faisal a yau ta rama wannan cin fuskar amma BABU! Komai nasa yayi masa dai-dai ya kuma dace da yadda Ubangijin halitta ya tsara mishi abinshi kai kace shi ya zabawa kansa, tako’ina, Faisal Bello bai da makusa.

Ita ko tasan fara ce jazur, kenan farin ta yayi yawa har ta kode? Wasu kwalla suka zubo sharr, tayi saurin sharewa da bayan hannun ta.

Goggo ta rasa ma abinda zata ce tace “oh ni Jummai! Allah kayi mun maganin abinda yafi karfina, ka iya min abinda bazan iya ba, nace shiga gaban ku tafi Saratu jayayya ba ta da amfani, Allah ya kiyaye hanya�.

*****

Tafe suke tamkar tafiyar kurame, to ba wanda yace da dan uwan sa ci kanka, har suka fita shiyyar Kaduna kwata-kwata, yace a ransa bari dai ya kara tsokanota. Ya dibi yanayin ta kana ya maida hankalin sa a titi yace,

“kin san meye ne baby? Abinda ke kara sawa in so Ronke, shine murmushin ta, tamkar na ‘yammatan hurul-eeni yake, tafiyar ta ko kin san catwalk to haka take. Idan tayi dariya jerarrun hakoran ta masu haske kamar kankara na sawa in mance da kowacce ‘ya mace a duniya, muryar ta tamkar sarewa na kwantar da hankalina.

Tana kishina kamar mijin ta, ranar da kika yo mun waya kwana tayi tana kuka. Idan ta rungume ni Intissar mancewa nake da kyawun kowacce diya mace a duniya sai ita Ronke Adeyemi Olayemi…�

Sai a lokacin ya lura Saratu kuka take haikan, kuka take tun karfin ta baka da zuci. Zuciyar sa ta tsinke hadi da wani mummunan faduwar gaba da ya sameshi duka a lokaci daya, komi ya tsaya mishi cik.

Duk wani haushin ta da yake ji sai ya kau, tausayin kansu ya maye tunani mafi rinjaye cikin zuciyar sa har bai san shi kansa Faisal yake tausayi ba ko ita Saratun?

Shi fa ba mahaukci bane, hakannan a shekarun sa, tunanin sa da matakin ilminsa, ya isa ya fahimci irin kaunar da sukewa juna daban take da wadda ‘yan uwan jini daya ke yiwa junan su. Kar dai ya kasance Allah ya jarrabcesu da son junan su alhalin suna uba daya? Mai yasa Ubangiji zai jarrabce su da wannan musiba? Yayi saurin jan istigfari ga sabon da zuciyarsa ta bijiro tare da kokarin kawar da wannn bahagon tunanin.

Idan yasan zuciyar sa, ya san abin da ke damun ransa, ya san nata ne? Yanzu haka ma ita a binda ke damun ranta daban ne,. to in ba haka bane mai yasa suke kishin juna? Bai sani ba! Ba kuma ya son ya sanin, don sanin baya da amfani.

Idan kuma ya dage sai ya sanin ba abinda sakamkon binciken nasa zai haifar face (bakin-ciki) tunda ko ko a garin gaba-gaba ake ba za’a taba barinsu su auri juna ba, to suma suna hauka ne? Kai Allah ya sauwake su ce suna son junan su, yaya ma hakan zai taba kasancewa? Ba komi ke kimsa masu wannan halakar a zuci ba face Iblis dan lis, (diabolical feeling). Don haka ya rage gudun motar ya safka a titi yace da karfi “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem!�
Chapter 42 · 0% Book details