← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta ja bargo har kanta ta kudunduna tana rawar dari. Ta ce cikin fushi, “Aminu, ba na so, kada ka sake, wannan haramun ne, idan kuma ka ki zan gaya wa matar ka ta ja ma kunne.�

Ya tuntsire da dariya ya ce, ‘Ita har ta isa?�

Ta gyada kai, ‘Har ta yi yawa.� Ya tura hannun shi a aljihun shi ya ce, ‘Zo ki ji?�

Ta harare shi cikin haushi ta ce,

“Ba’a zuwa.�

Ya mannawa wani gefen daban ido ya ce (ba tareda ya dauke idonsa daga gefen da ya mannawa idon ba),

“Ashe kadangaru ma na son kafar fararen mata? Dubi yadda yake lasar farar kafar ki cike da so da kauna.�

Haba! Da ta daka wani tsalle, sai gata makalkale jikin Al’ameen tana ihun rokon sa, “Don Allah cire min shi, don girman Allah! Sai hawaye sharrr! Jikinta na kyarma. Ya fiddo hannun shi daga aljihu rike da necklaces da zobba, abin hannu da kafa na duwarwatsun matan Niger da ya sayo a Niamey, ya russuna ya daura mata a kafa, ya daura mata a hannu, ya mike ya daura mata a wuya. Ya bula hancin ta da kwambalelen abin hancin su mai kama da awarwaro, sai da ta feso wasu hawaye don azaba, amma ta yi kyau! Ta yi kyan har ta gaji!!

Ta bishi da ido galala! Kana hannayen ta da ke cikin nashi. Da jikin sa data makale. Ta sauke idon ta ga kafafun ta, wani hawayen ya zubo.

Ya kai hannun ya shafo hawayen yana murmushi ya ce,

“Haba Halimah! Ya ya ki ke min asarar hawaye a kan kadangare? Ba kadangare ba, ko Zaki bai isa ya taba ki ina gani in kyale shi ba, sai dai ko ni ko shi. I luv u Halimah!�

How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one

*@Takori*

Page8ï¸âƒ£

1 Rabi Al-Thani (Hijriyyah)

Wata Biyu Bayan Dawowarsa

Al’ameen da Halimar shi (Kamar yadda ya nace da kiranta) sai aka soma shimfida ingantacciyar soyayya mai ban mamaki da ban sha’awa. Barin yanzu da ba su da shamaki, Hajiya kishi ya kore ta don har kwanaki suka shura tana Dubai ta ki dawowa. Su Khalil tun safe in sun tafi makaranta sai karfe shida na yamma suke dawowa don haka ba su ma san me Al’ameen ke yi a gidan ba, kai ko a mafarkin su ba su kawo ya ma san hanyar kitchen din gidan ba, to ya je ya yi me?

Ita kuwa Dela tsoron shi take, da ta gan shi za ta soma bare-baren jiki ta gaishe shi ta wuce ta bar su. Tana kakabin abin a zuciyarta ita kadai amma ba ta ce da yarinyar komai ba.

To ta ce mata me? Me ke tsakanin ki da Aminu ko me? Ta gaya masa ya ce tasa mai ido a yi mata asarar abincin ta yadda duniyar nan ta zama uhm-uhm, ba ruwanta su karata. Daga ita har Al’amin sun dauka da ba son juna suke ba, sai yanzun. Tun tana jin kunyar sa har ta gaji ta bari, domin ban dariya irin na Al’amin Allah ya yi yawa da shi.

So, shakuwa da yarda da junansu su ne muhimman tubalan da suka gina soyayyar su a kai. Haka amincewa da junan su kullum sai kara karfi yake a zuciyar kowannensu. Ji suke, daya bai iya rayuwa ba tare da dan uwansa ba.

Ba ta san me ye so ba a rayuwar ta amman Al’ameen ya koyar da ita wata irin soyayya mai shiga rai a lokaci daya, ya koyar da ita yadda za ta so shi, ta kaunace shi shi kadai a zuciyarta. Ba ta taba jin son wani da namiji a duniya irin yadda take ji yanzun a kan Ala’meen ba. To haka shi ma, tuni ya mance da Ihsan kwata-kwata a babin rayuwar shi watakila ta zama tarihi. Wadda a lokacin ta rasa nutsuwa kwata-kwata na rashin sanin makomar ta; ‘yar rakiya? Ko matar Al’ameen?

Ita kam da ta san cin amanar da kasar haihuwar ta abin tunkahon ta, Nigeria, za ta yi mata kenan da tun farko ba ta takura su dawo ba. Haka Ann ta ce da ita muddin ta name shi bai kawo kansa ba ta bar ta da Jesus ya bi mata hakkinta na haifar ta da ta yi da wahalar da ta yi ta yi da ita.

Ya tabbatar mata da amaryar Daddy ta tare zai kai masa bukatar su, kasancewar sa gwarzon uba, mai son duk abin da ‘ya’yan shi ke so ko da shi ba ya so in har bai sabawa tarbiyya da Addini ba, ya tabbata ba za a samu wani mushkila daga gare shi ba, sai dai ko daga gare ta, don ya lura son shi take amman auren baya gaban ta sam.

Duk lokacin da ya yi zancen aure ya kan lura ta shiga wani zuzzurfan tunani, sai ya ta’allaka hakan da tunanin mahaifiyar ta da ta ce ta rabu da ita tun tana karama ba ta san inda take ba.

A irin wadannan lokutan ya kan gaya mata zai zamo mata Uwa�, zai zamo Uba a gare ta. ‘Yan uwan shi za su maye mata gurbin nata ‘yan uwan, su nuna mata kauna ta jini da bata samu ba a rayuwar ta. Zai zamo mata miji kuma aboki, zai zama komai nata, zai kauna ce ta muddin ransa�, zai nesanta ta da Hajiyar da ke kin ta�, zai bude mata duk wasu kofofin farin ciki da dan adam ke burin samu!

Ta kasance cike da tunanin wa Daddy zai aura? Ta je daki ta kwanta a dandaryar kasa ta yi ta kuka. Ta tabbata ta rabu da mahaifiyarta kenan har abada! To amma kauna da kulawa irin wanda Al’ameen ke nuna mata, wani abu ne dake rage bakin ciki da takaicin da zuciyar ta ke ciki.

Ta kan tambayi kan ta yaushe ne wannan daukin da Najib ya kwadaitar da ita zai zo ne? Ko ko Al’ameen ne? Shi yasa ya dage su yi aure? Allah Sarki! Tana matukar tausaya masa, bata taba ganin mai son ta bayan Faisal, irin Al’ameen ba, ai ko ita shegiya ce ya kyautu ta aure shi hakan nan. To amma a matsayin da take kai a yanzu wa zai mata auren?

*****

12 Jumada Akhir (Hijriyya)
Rana Mai Dimbin Tarihi A Gare Ta

Faisal Bello Makarfi ne ke saukowa daga jirgin MEA International, ranar sha biyu ga watan Jumada-Akhir. Gaba daya Engineer Faisal B. ya canza tamkar ba shi ba, yana sanye cikin bakaken suit ya kuma daura thick coat saboda matsanancin sanyin da ake tsugawa, bakin takalmi sau ciki ne a kafarsa kirar Italy, hannun shi na hagu daure da agogon Rado yayin da na daman ke rataye da matsakaiciyar jaka irin wadda matafiya kan zuba passort da sauran kayan amfani na gaggawa.

Bai fara tozali da kowa ba sai Ya Ameenu da rabonsa da shi shekaru goma sha biyar. Ya karasa da gudu suka rungume juna suna juyi kafin su soma hawaye. Abubuwa da dama sun faru, na farin ciki da na bakin ciki, na bakin cikin shi ya fi yawa.

Bai taba zaton zai kara ganin Al’ameen ba a rayuwar shi, har suka iso gida kuka suke wiwi. Ya rasa mai yasa bai kullaci Aminu ba? Amsar shi ne don yana son shi, ko a cikin ‘yan uwansa Aminu daban ne. Kuma tunda har Daddy ya yafe masa shi a kan me ba zai yafe masa ba?

Bai fara tambayar kowa ba sai Inteesar dinsa, Aminu ya ce, “An ce tana makaranta amma daman kwanan nan za mu kai mata ziyara tunda ga ka ma ka dawo shi kenan.�

Ya yi shiru cikin tunani, shekarun da suka gabata suna da yawa, ya ci a ce yanzu ta yi nisa a jami’a in har lissafin da yake daidai ne. To ko a jami’ar take? Ya so kwarai ya tambayi Al’ameen sai ya share, ko da can Al’ameen na shiri da Intisar ne balle yanzun? Ya sauke shi a kofar gidansu ya juya ya tafi gidansa don yana da abin da zai yi da yawa.

Haka kuma a ranar ne motar Daddy ta sauke Aunty Saratu, Zarah, Goggo Jumami da aminiyar ta Jami a harabar gidan, sabanin da su kai da motar Al’ameen na mintuna uku ne kacal, Aunty Saratu again a matsayin matar Daddy Makarfi.

Ta kara kiba, ta kuma yi haske sosai na samun hutu da kwanciyar hankali. Baben ta Zarah na kwance a kafadun Jami tana barci suka shiga sabon sashin Aunty Saratun wanda da farko sun dauka ba a Nigeria suke ba, babu abin da Daddy bai zuba mata ba na jin dadin rayuwar duniya irin abin nan dai da ake kira Aljannar Duniya.

Dakin Inteesar kadai abin kallo ne don a naira miliyan biyu cif Daddy ya sa kamfanin edcel interior decoration suka yi wa Intisar da yake tsammanin tana makarantarsu a Riyadh.

Tun kafin ta zauna ta ke kwalawa Intisar kira tun karfin ta, sai Khalil ya shigo yana toshe kunnensa haka su Goggo suna

“Kar ki lahanta mana dodon kunne.�

Khalil ya ce, ‘Anty ki yi hakuri, ba jiyo ki za ta yi ba, don tana can sassan ‘yan aiki, bari in je in dauko miki ita kawai aka, don in na ce ta zo ko kallo na ba za ta yi ba.�

Hawaye suka fitowa Saratu sharr! Wai Saratun ta ce a sassan ‘yan aiki? Ta daura hannuwa aka ta fasa kururuwa ta ce,

“Amma Allah ya isa tsakanina da ke Haj. Nafi.�

Da haka ta kwasa da gudu babu ko dankwali tuni ya yi nasa waje, ta bi hanyar da zai sada ta da sashin ‘yan aikin. Khalil na bin ta yana kira shi ma kukan yake, a daidai lokacin da Faisal shi ma ya fito daga cikin gidan bangaren Hajiyarsu ko jakar hannunsa bai aje ba saboda kururuwar da ya ji ta gigita shi na muryar da ya tabbatar Antinsu ne, ganin Antin tana gudu babu ko mayafi bai san san da ya yar da jakar hannunsa ba ya rufa mata baya, yana

“Aunty Saratu ki tsaya!� Ta ce,
Chapter 14 · 0% Book details