← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 90

Sashe 85

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faisal ko motsi ya kasa, durkushe kawai yake tamkar mai neman gafara. Zuciyar sa ta cunkushe da tunaninnika daban-daban. Ya rasa abinda ke masa dadi, ya rasa abinda ke sanyashi tsanar duniyar da abinda ke cikin ta, ya rasa abinda ke sanyashi nadama a kan Intisar. A ganinshi ai shi ya dace a tausayawa ba ita ba, shi da bashi da saa, shi da yake son maso wani? Shi da bai ci riba ba ko kankani a soyayyar daya wanzar da rayuwarsa a yi mata?

Amma wai har shine uwarsa zatayi masa baki a kanta, bayan ita din nan ba abun tausayi ba ce; muguwa ce, mayaudariya ce, azzaluma ce kuma mai son kanta da farin cikin ta kadai? Ya girgiza kai wasu zafafan hawaye suka zubo bisa lallausar kumatun sa, ya ce cikin matsanancin takaici, “Yanzu Hajiya me kike so in yi?�

Ta ce, “Ban sani ba, shashashan banza kawai. Kana zaune har wani zai aure ta baka cikawa kanka kowanne buri ba, baka cimma wani farin ciki a rayuwar ka ba, ka zo a banza zaka koma a hofi, kana ta kunci da dacin rai kai daya babu wanda ya san kana yi sakarai kawai. Yanzu yanzun nan ba sai anjima ba ka nemeta ku sasanta, ai na san son ta ke lalata ka ba wai ban sani ba, zuba maka ido nayi in ga iya gudun ruwan ka, amma naga abin naka bana kare bane, wanda bai san abinda ke masa ciwo ba.

Ya yi murmushin takaici ya ce, “Hajiya, tunda muke a duniya, na taba ce miki ina son Intisar, so na soyayyah, da har kike cewa in aure ta?�

Ta dube sa a lalace ta ce “Ai fa, shine naga ka bar kasar baki daya saboda tsoron, kada son daka ke yi matan ya fito kowa ya gane, sabida bakin cikin bazaka iya aurenta ba alhalin tana kanwar ka da kuke uba daya? Shi ne kake bata min domin ta, kake yin fito-na-fito da ni duk a kanta. Tun a lokacin na dago ka Faisal, kawai na godewa Allah daya bani ikon cika alkawarin da nayi wa Babanku na cewa bazaa taba ji daga baki na ba ita din ba yar sa bace, na tabbata a lokacin da sai ka aure ta, koda ni din zan ki amincewa.

Wannan shine babban dalilina na kara boye maku maganar, don ina ganin bakin ciki na na karshe a rayuwa kuma wanda zai kayar dani a lokacin shine ka aure ta.

To amma dubi yadda Allah ke juya alamuran rayuwarmu gaba daya ta yadda mu din bamu tsammana ba, bamu taba zato ba. Ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa magana ta a yau Faisal zaka yi nadama mara amfani a gaba dayan ragowar rayuwar ka, irin wadda na yi, danuwan ka ya yi. Ka yi amfani da sauran damar da Allah ya baka a lokacin daya dace, domin in ta wuce, ba zata taba dawowa ba!�

Ta fada tana kada yatsanta Ibham, lokaci guda kuma ta mike ta bar masa dakin idanun ta cike da hawaye.

Ji yayi zaciyar sa ta karye, duk wani sauran kuzari da ke tare da shi ya kare. Ya mike ya fito daga dakin, shi kansa bai san inda ya ke jefa kafar sa ba, kawai ya tsinci kansa a tsakiyar falon gidan.

To ina zai dosa cikin gidan nutane karfe goma sha biyu da rabi na dare? Ban da dai uwa-uwa ce kuma dole a bita da yadda ta ke so. Banda ma rigima irin ta Hajiya to ya je yace mata me? Shi fa ko nambar wayarta baya da ita. Above all ma yana ganin magana da ita ma bata lokaci ne tunda ba wani amfani ke gareshi ba.

Na farko Intisar-Intisar ce har kullum a gare shi, the past memories will forever remain fresh in him, sai dai ai shi bata son shi, Alameen kadai take so. Shi ba komi bane face yayan da ta ke kauna. Me yasa Hajiya ba zata dubi wannan ba? Me yasa bazai cigaba da zama a matsayin da ta bashi ba ko don tsira da daraja da mutuncin sa da take gani?

Tunanin hakan ya sanyashi juyawa, tare da kokarin maida kwallar da ke neman bayar da shi. Amma sai Najib ya tokare masa hanya da kafar shi ta dama.

Ya daga ido ya dube shi fuskarsa babu alamun wasa hakan nan bacin ransa ya ninka na koyaushe, ya fito baro-baro cikin idanun sa. Najib din bai kalleshi ba don shi kansa ya razana da tension din da yaga Faisal din a ciki, wayar sa kawai yake latsawa cikin murmushi, cikin saa kuwa bugun farko ta shiga, ita din ce kuwa ta dauka da alama dai cikin magagin barci ta ke, cikin rarraunar muryarta kamar koyaushe tace Yello! Ya Najib ya aka yi? Ya ce ki yi mun afuwa, na katse maki barci. Ki sakko yanzu nan falo ina son ganin ki personally, is vital ki zo da sauri. Da haka ya katse wayar ya maida aljihu. Ya dubi dan uwan shi yai murmushi ya ce,

“Gata nan zuwa, kayi hakuri da shishshigi na, I just dont want to loss you, as I lose Ameenu! (Bana son rasa ka, kamar yadda na rasa Aminu) kuma na rantse idan ka cigaba da azabtar da kanka kai ne da wahala, in ma dukanta ne ka yi, amma ka ke tunawa a kullum duk laifin da kake tuhumar ta da shi, bata aikata ko daya ba, zargi kawai kake kuma wallahi in baka yi wasa ba zaka yi nadama mara amfani.

How much do you like this story?
5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four

*@Takori*

Page🔟

Shikam ya shiga uku, wai meyasa kowa ya budi baki sai yace zai yi nadama a kan Intisar? Bai taba yin nadama a rayuwar sa ba, kuma har abada ba zai yi ba! Ita ce dai ya kamata a gayawa wannan. Intisar din wace ce?

Wannan daya rike a hannun shi tun tana jaririyar ta? Wannan da ya ci kashin ta ya ci fitsarin ta, yasa mata feeder ya cire mata pampers itace wata mutum da zai yi nadama a kan ta? Yayi murmushi cikin takaici mara misaltuwa ya bude baki don baiwa Najib amsar da ta dace da shi, babu shi babu alamar sa.

Nitsatstsen takunta ya jiyo tana saukowa daga saman bene, bai san daliliba kuma ya samu kansa cikin gigicewa da dimaucewa. Wannan tsohon son, wannan tsohuwar kaunar da an ka ce bata taba gushewa sai dai masoyan su gushe, to balle su da suke ras, a bisa ganiyar kuruciyar su. Wai wannan Intisar din Aunty Amarya ce yau ake lika mai yana cewa baya so! Intisar din shi da baya hada kaunar ta data kowa a rayuwar shi. Intisar din da ke zuwa cikin mafarkin sa, tsayuwar sa, zaman sa, tafiyarsa da duk wani alamari da yake gabatarwa.

Intisar din da zuciya ke kuka domin son ta, gangar jikin ke azabtuwa domin kaunar ta, yawun baki ke kafewa, gudun jinin jiki ke daskarewa, tunanin shi da hankalin shi gabadaya ke gushewa a duk lokacin da yaji sassanyar muryar ta.

Wannan murmushin, wadannan abnormal lumsassun idanun, wannan takun mai kamar na mage catwalk, wannan da wancan, kai everything about her that drives him crazy idan ya bar su a yau, shikenan?

Sai ya juyo cikin wani irin slow motion da yafi kama da umarnin zuciya zuwa abinda take matukar so. To itama din kallonshi take, cikin wani yanayi na mamaki da rashin abin cewa. Suka yiwa juna kuri da ido, kowanne na kokarin gano boyayyen sirrin da ke cikin zuciyar dan uwansa. Ba shakka ta ga abubuwa da dama cikin kwayan idanun shi;

bayan ciwon so da ya illata su, akwai rashin yarda, tuhuma, zargi da yanayin nan na yaya zan yi da son ki? Ta dai tabbatar bazata iya jure ganin irin wannan kallon na zargi da yake mata ba sai ta juya masa baya, a yayinda hawayen da take tattali suka samu yanchin kan su. Ta daga kafa da niyyar hawa bene domin komawa inda ta fito amma ina! Kafar tace bata san wannan ba, bata amince ba.

Wannan Ya Faisal ne fa? Har yau, har gobe wannan Yayan ne da babu kamar sa, Yayan da zata iya sacrificing (sadaukarda) komi nata domin farin cikin sa including rayuwar ta. Shine yau cikin wani tsohon burin daya dade da shi, amma ta kasa taimakawa wurin samar da shi a gare shiashe kenan ita ta cika butulu, dan adam mai manta alkhairi, kaza ci ki goge bakin ki.. ta sake girgiza kai da karfi kamin ta samu kanta zube a gaban shi da dukkan guiwoyin ta.

Kuka take na fitar hankali, kuka irin mai gigita duk wani mai imani, kuka take irin mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta balle Faisal? Ya dira hannuwan shi duka biyu a bangon da ya ke jingine cikin muryar da ta razanata, ya ce,

“Enough .. is enough Intisar! Ba tun yau ba ai nasan so kike ki kashe ni, kamar yadda kika kashe min Ya Ameenu? To amman wallahi ko zan mutu bata dalilin ki ba; baki isa ba, kin yi kadan ba a haife ki ba har yau ko wacece ke!

Uwa ta ta ce idan kika sake zubar da hawaye domi na bata yafe mun ba, wato tunda kin kasa kashe ni shine zaki sa bakin uwa ya lalatani?

Abinda bata taba gani ba sune suka zubo a yau. Yayi kokarin kau da fuskar sa don kar ta gani, don a ganin sa ba karamin ci baya bane Intisar taga hawayensa, hawayen ma domin ta. Kenan ta yi galaba a kansa, kenan shima ba zai iya controlling zuciyarsa ba kaman Alameen in dai a kan Intisar ne?

Sai yayi saurin juya mata baya tare da saurin sanya hankici ya share idon sa amma ita din bata fasa kukan ta ba har da sheshshekar da ke kara kona masa zuciya.

Ta kama kafarshi ta dama, wani irin karaya, da ya ji zuciyarsa tayi shi kansa yayi mamaki, hakannan kalma ko daya ta kasa fita bakinta, yace sakar min kafa da wata murya tamkar ba tashi ba.
Chapter 85 · 0% Book details