← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 90

Sashe 19

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwar su abin sha’awa ce ga kowa barin ‘yan mazan ‘ya’yansu masu tsabar kama da juna. Duk da kasancewarsa ba mazauni ba baya sake da tarbiyyar ‘ya’yan shi. Islamiyya dole ne su je ta da yamma haka da dare ya aje masu malamin Addini da ke karantar da su littattafan Addini irin su Kawa’idi, Ishmawi, Sirah, Arba’una Hadith, Nurul-Mubeen da sauran su. Idan kuma sun tafi makarantar boko ba su dawowa sai karfe hudu na yamma, domin akwai special edtra lesson da yasa ake masu after school hours. Don haka duk cikin yaran Hajiya Nafi kaf babu dakiki kowanne kwaro ne wajen karatu, idan har ka ji su suna tafka musu to a kan karatun su ne, don kowanne ji yake ya doke dan uwansa a hazaka. Haka lafazin da ke fita bakin su a shekarun su zai ya ba ka mamaki, babu wanda ba za ka ji shi da ma’ana ba. Ga hadin kai, ga baiwa babba girmansa koda shi ke binsa a haihuwa.

‘Ya’yan Brigadier ba su san wani abu wai shi yawo ba ko raini ga na gaba. Basu iya zagi ba, basu iya karya ba, basu san yaya ake yin su ba. Haka idan sun dawo daga lesson din dare, kafin su kwanta karatun su ya koma wuyan Anti Saratu.

Saratu, diyar Baffan Brigadier ce, auren zumunci ne a tsakanin su, zumuncin ma irin wanda aka zama daya din nan kamar wa da kanwa na ciki daya.

Ta kammala digirin ta na farko daga Jami’ar (Edeter) da ke U.K, inda ta karanci Insurance zallah. Wannan kuwa daurin gindi ta samu daga murdadden dan boko dan uwan ta Bello, wanda ya dauki nauyin komai na karatun ta shekaru hudu cif a matsayinta na kanwarsa wadda nauyin komi nata ke kansa tunda ba’a yi mata aure ba.

Ta dawo gida tana da shekaru ashirin da hudu da haihuwa. Rikicin auren ta da Alhazai biyu shi ya yi sanadiyar auren ta da yayanta, ko ko in ce daga gatse.

Da fari Baffan su ya kira Brigadier ne ya ce,

‘Ka ga karatun nan dai kai ka daurewa Saratu gindin yinsa, ga shi ta dawo kowa ya zo ta ce ba ta so ga illar shi, kana nufin auren ma ka daure mata gindi ta ki yi?�

Ya ce, ‘A’a Baffa, Saratu na son yin aure, ba ta samu wanda ya kwanta mata ba ne har yanzu. A yi hakuri a kara mata lokaci.�

Baffan ya yi salati ya ce, “Shekaru ashirin da hudun za a karawa lokaci? To wallahi ba a gidana ba sai dai ka dauke ta ka kai can gabanka ta zauna. Duk kun ja min surutu a gari, ban isa in je wajen daurin aure ba sai an nuna ni ana zundena ga wanda ya aje uwar mata a gida wai boko. Idan ba kya son shi Alhaji Saminu saboda mata uku, shi wannan ministan fa mai mata daya saboda Alah me ye laifin sa?�

‘Yar auta Saratu sai ta kwabe fuska, ‘Gaskiya Baffa ya fiya tumbi, rundumi, ina zan kai wannan kayan jigida?�

Brigadier ya yi dariya shi ko Baffan sandarsa ya dauka zai buge ta Bello ya tare, ya ce,

“Ni za ki kawowa fitsara don ki nuna min ke kin je turai kin fetsare? In gaya miki Mungo-Park ma kakan-kakan ku mun ga iyakar sa balle ke, kuma tunda ba kya son Alh. Aliyu sai ki tattara ki bar min gida ko a daina ganin ki a garin nan ana nuna ni a wajen daurin aure.� Ya soma kuka.

Brigadier ya ce, “Baffa duk abin bai yi kamarin haka ba, kash…�

‘To, to na ji bai yi zafin haka ba, ai sai ka gaya min me kuma ku ke nufi? Ka ce karatu, an kare, sai kuma me? A sani a bakin duniya ko me? Ba kwa auren junan ku kowa ya huta? In kuma shi ma tumbin gare shi to don uban ki zo ki fice min a gida ki koma can turan ki auro bature sardidi sannan ne ki ka burge ni.�

Dariya ce ta kama su dukkan su, ya yi murmushi ya tausasa murya cikin rarrashi, ‘Allah ya ba Baffa hakuri, abin bai yi zafin haka ba sam, Saratu kin ji me Baffa ya ce? Me zai hana ni ki aure ni?�

Kunya ta kama ta, ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Sai dai a ranta hakika ta yi na’am da auren Yayan ta, don dama tuni ta dade tana sha’awar yiwuwar hakan, don duk duniya ba ta ga namijin da ke burge ta kamar shi ba. Sai dai me? Tana masifar tsoron Hajiya Nafi, don ta san ta kwarai kamar yunwar cikin ta kan azababben kishi a kan mijinta da suma da suke dangin sa balle sun aure shi? Baffan ya ce,

“Za ki amsa ko sai na yi kwallo da ke?�

Ta zabura ta fake a bayan Yayanta, cikin tsoro ta ce, “Baffa to Hajiyar su Aminu fa?�

Brigadier ya yi murmushi, “Ke manta da ita, ba abin da za ta yi miki, kin amince ko Saratuna?�

Duka suka yi wa juna lallausan murmushi har suka bai wa Baffan kunya, ya mike yana karkade buzun shi ya yi cikin gida.

Ba karamar badakala aka kwasa da Hajiya Nafi ba kan auren Saratu, don cewa ta yi munafurci ne su Baffan suka kulla mata don dama sun tsane ta, amma in ban da haka a rasa wadda za a kakaba masa duk cikin dangin nashi sai yarinyar da suka tashi gida daya?

Kwanan ta goma a yaji babu wanda ya je bikonta da ta ga abin ba na wasa ba ne, dolen ta ta dawo ta tadda amarya a rufaffen sashin da ba kowa, kamar ta yi hauka, ta hana kanta ta hana kowa a gidan nan sakat da bala’i.

Da ta ga wannan ba zai mata ba, domin kamar tana zuga su ne su kara likewa juna sai ta koma bin malamai da ‘yan tsibbu, ta mance Saratu kanta ‘yar malam ce, ba kowanne karabitin asiri ke kama su ba.

‘Ya’yanta ke ta tausar ta da cewa ta kwantar da hankalin ta har Najib na cewa,

“Maman mu in ta zo me za ta yi miki? Maman mu ba a kan ki za ta zauna ba.�

Shi ko Faisal cewa ya yi, ‘In dukan ki ta yi Ya Aminu zai rama miki.�

To sai ya kasance ita Saratun mace ce mai ilmi na zaman duniya ta san yadda take tafi da abokiyar zaman ta cikin lumana. Amma har inda nan ke motsi, Hajiya Nafi kafarta ba ta bar gidan ‘yan tsibbu ba da ‘yan bori ba a hana Saratu haihuwa.

To sun ci nasarar wannan kam, tunda ance abin gaskiyar mai shi ne. Amma kullum mijin su kara son ta yake saboda hankalin ta da tunani.

Rashin haihuwar ta ba su danganta shi da kowa ba face Allah. Su kan ce lokaci ne har yanzu bai zo ba. Shekarun ta biyar a gidan wadanda in kin dube ta ba za ki ce ta hada ashirin da taran ba. Tana aiki da Insurance Company na Kaduna.

Haj. Saratu baka ce bakin da akan kira black beauty. Mace ce da ta lakanci kalmar ‘gayu� duk da shekarun ta still ita ‘yar gayu ce komai kuma cikin gayun da bokon take yin sa. Rakiyar Brigadier aiki duk ita ce haka in za shi abroad domin hutu ko aiki duka Aunty Saratu ce mai rakiya. Ita Hajiya son ‘ya’yanta ta sani sai maida kobo ya koma dari.

*****

Ta sanya baby a ruwa ta yi mata kyakkyawan wanka, tana mai tazbihi ga Al-Khaliku Sarkin kaga halitta ta yadda ya suranta wannan yarinya tamkar diyar Larabawan Masar. Wani irin so ne ke huda bargo da tsokar jikin ta na ‘yar da ba ta san ko ta wa ye ba!

Ta ciro bebin daga ruwan tana nannadewa a tawul kenan su Khalil suka shigo, wani na ture wani, kowannensu na cewa shi zai fara goyon bebin da Daddy ya ce ta haifa suna makaranta. Dadi ne ya kamata ta ce, Najib ne zai fara goyawa tunda duk ya fi su karfi.

Najib shi ne da na uku a ‘ya’yan Hajiya, yaro ne mai kunya sai ya sadda kai a ransa yana cewa yaya ma za ai ya goya mace? Ya ce, ‘A’a Anti ai mace ce, da dai namiji ne sai in goya.�

Faisal da tun shigowar su yana durkushe gaban jaririyar ya yi farat ya ce, ‘Gafaracan da Allah malam ni in goya, anti ni za ki na goyawa baby kullum.�

Ta sa masa bebin a baya tasa zani ta kulle masa. Najib da yake duk ya fi su wayo har Faisal din da ya girme shi ya dubi bebin sosai ya ce,

“Antin mu a haka wani sai ya ce bebin nan ta yi wata uku?�

Gaban Antin ya bada dam! Sai kuma ta yi dan jim, kafin ta ce,

“Ai su dama lafiyayyun babies haka ake haifan su da girman su.�

A ranar kwata-kwata Faisal bai bar Anti da raino ba, shi ya zabi kaya overall na babies masu kyau cikin kayan da Daddy ya jibge mata ya sanya mata ya shafe mata jiki da olive oil.

Haka Antin ta ce da su nonon ta ba ya da lafiya don haka doctor ya ce a dinga shayar da baby da madarar NAN. Faisal shi ya sanyawa babyn feeder a baki yana ta zuga ta wai ta yi sauri ta shanye ko ta yi saurin girma su dinga tafiya makaranta tare.

In sun dawo ta bi su Islamiyya kafin su kwanta ya koya mata ABCD. Su kuwa sauran sun zagaye ta in ka dauke Al’ameen da ke makarantar kwana, suna ta yaba kyawun kanwar su, a cewar su ba su taba ganin baby mai kyawu kamar ta ba, ji suke tamkar su lashe ta don so, babu kamar Faisal, da kyar suka bar ta gun uwarta, don sun dage sashin su za ta kwana ko sauro ba za su bari ya taba ta ba, sai da Antin ta ce da su cikin dare za ta yi masu kuka sannan suka hakura.
Chapter 19 · 0% Book details