Sashe 6
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A Makarfi gidan Baffansu ya tadda kannensa su Najib sun zo suma, nan gidan Baffan ya kaure da murnar ganin Ya Aminu. Ya dade rike da kyakkyawar babyn ta Zarah, yana kallon ikon Allah don kamar su da Faisal har ya yi yawa (Zahara ce autarsu ‘yar amaryar babansu da ya saki). Ya ce, “Anty ko za ki ba Ihsan rikon Zarah don Allah.�
Shi Al’ameen bai da masaniyar rabuwar Antin da Daddyn shi ya dauka wankan jegon dai take kamar yadda Hajiyar su ta gaya masa, sai ta murmusa ta ce, ‘Ban ga Ihsan ba, amma tunda na san a America aka aurota ba za ta so rikon dan da ba nata ba.�
Ya yi murmushi ya ce, “Amma za ki ba Intisar?�
Ta ce, ‘Idan mijin da ta aura na kirki ne ba?�
Da haka ta kashe zancen, ta lura Al’ameen bako ne kawai daga Miami, bi ma’ana bai san komai ba cikin al’amuran da suka faru cikin rayuwarsu.
Ba yadda Al’ameen bai yi da ‘yan uwansa sa ba kan su tafi Abuja tare, amma sun kiya wai a cewar su tafiyar dare za su yi wa Enugu.
Abinda ya lura dukkanin su bakin su daya har Antin suna boye masa wani muhimmin abin da ke damun su ba sa so ya sani, ko ma meye. ai in ta yi wari zai ji ne tunda yana nan a kasar ba inda za shi. Ya kyale su da alkawarin har Enugu zai kai masu Ihsan.
Wurin karfe goma na dare ya koma gida, a daidai lokacin Daddy na kokarin hawa sama shi kuma yana kokarin sauka, sai suka yi kacibus, dukkanin su suka yi wa juna murmushi mai cike da kauna irin ta da da mahaifi.
Daddyn ya ce, “Ina ka yi ne Aminu tun safe ko gama hutawa ba ka yi ba?�
Ya ce, “Masu cinikin fili man ke ta min yawo da hankali, amma yanzu mun daidaita da wani a Addis-Ababa Crescent.�
Daddy ya ce,
“Abin da nake gani ya fi kawai ku yi amfani da gidana da ke ‘Colorado Close�, don ba mutunci ba ne abar yarinya a gidan su har sai an gama ginin, gobe in Allah ya kai mu za ni mu gana da shi Dr. Argungu, don dama mun san juna sai dai ban taba tsammanin za ka hadu da ‘yarsa ba ma balle har mu zama daya.�
Ya dan murmushi kadan, don ya lura su dai su Daddy suna son auren nan nasa ko don cikin samarin ‘ya’yansu kaf babu wanda ya yi auren fari ne? Bai sani ba. Daddyn ya kuma cewa, ‘Mun daidaita da kamfanin Julius Berger da za su yi ma ginin tun safe in ka samu filin?�
Ya ce, ‘A’a a sallame su kawai don tuni na yi magana ta komfuta da kamfanin da ke yi min gini a Miami, ina son aikin su sosai, za su zo su cikin dan lokaci kankani za su zuba komai.�
Ya ce, “Babu damuwa, duk yadda ka ke son haka za a yi.�
Al’ameen har ya juya ya dawo yana sosa kai ya ce, “Af Daddy, na je fa Makarfi?�
Ya dawo shi ma da dukkan attention dinsa gare sa cikin sanyin jiki ya ce, “Yaya ka baro su, suna lafiya ko?�
Ya ce, “Kowa lafiya, Zahrah ta yi girma da wayo sosai, shin sai yaushe za su dawo ne?�
Daddyn ya lura sam Al’amin bai san ya rabu da Aunty Saratu ba, ga shi shi kan sa a lokacin babu abin da ke damunsa kaman, shin wai ma ya a kai ya saki Saratu? Me ta yi masa? Iyaka tunaninsa ba ya ce ba, bai sani ba. Kuma wai har Intissar ta tafi, amma ya kasa wani abu a kai? Ya ce cikin jin nauyi.
“Al’ameen na fa rabu da Saratu, amma gobe insha Allah ka raka ni biko, shi kenan? Allah ni kaina bana ce ga actual sabanin da ya faru ba, wanda kwata-kwata bai taba faruwa ba.�
Al’ameen ya yi shiru ba don komai ba sai don tausayin mahaifin shi da ya lullube shi, ya san irin wannan nadamar, ai shi zai gayawa kowa nadama mara amfani, to amma me yasa Hajiya ta boye masa komai? Ba mamaki don ba ta son duk wani abu da ya shafi Saratu, ta kuma san a wannan lokacin ba zai goyi baya ba, to ko Intisar da ke Riyadh ta san wannan?
Ya ce, ‘Ba komai Dady, haka Allah ya tsara, amma insha Allah komai zai daidaita, don ni Aunty Saratu ba ta min komai ba, heart and soul (Baka da zuci) kamar da, sannan in na sami lokaci zan je Riyadh in ga Saratu karama (Intisar).�
Daddyn ya ce, “Au! Ta koma makarantar ne?�
Ya ce, “Hakan dai aka ce da ni�
“In za ka din, sai ka yi min magana mu tafi tare, rabon da in sa Saratu a idona tun ranar da Saratu babba ta bar gidan nan.�
Da wannan Al’ameen ya kwanta, al’amura, ya rasa da wanne ma zai fara, tabbas ran Hajiya zai sosu in ta ji har da shi aka je mata bikon kishiya, bikon ma na mutanen da ta ki jini fiye da mutuwarta, to amma wannan ba zai hana shi gyara sunnah ba. Shi kawai hakan nan ya ke kaunar Anty Saratun saboda yakanar ta da abin da ya yi masu na rashin kyautawa can baya, amma ba ta damu ba, ba ta kullace shi ba, kai ko a fuska ba ta taba nuna masa ta san abin da yake ciki ba. Uwa-uba karin zuri’arsu daga gare ta.
Hajiya wata irin halittar Allah ce, ba a iya mata. Dole ya raka Daddy. Sai ko tunanin murdaddiyar ‘yar aikin Hajiya, da son jin labarin ta da son sanin dalilinta na wannan aikatau din ya fi kowanne tunani mamayar 70% cikin kalbin shi. Amma dare ya yi nisa, yana kuma da muhimmin signing din takardu domin karbar licence daga hukumar lafiya ta kasa a goben haka ma zai raka Daddy Makarfi duka a goben in Allah ya yarda. Ya so kwarai ya ga yarinyar a yau, to amma da safe ma tana firgita in ta ga mutane bare da daddare?
Haka ya kwana da sake-sake, shi kam zuciyarsa ta amince mai da ya taimaki kyakkyawar ‘yar aikin nan ta samu rayuwa mai kyau, don yana ganin idan ta ci gaba da irin wannan aikatau din mai matukar wahala (for her age), za ta yi asarar kuruciyar ta ne yarinyar ta da ita.
Washe gari ta na goge-gogen kicin wurin karfe tara na safe, kasancewar a yau ta kammala komai da wuri ba kamar jiya ba, sauri take ta je ta huta sakamakon danyatsan ta da ke mata zugi, ga kuma menstrual pain (ciwon mara) da take fama da shi, don ma ta samu yanzun ya dan lafa, amma jiya kwana ta yi tana kuka, saboda azabar sa da radadin da danyatsan ke mata, ba wai don aikin ya kare ba, tunda kuwa nan da awa daya za ta soma aikin abincin rana.
Al’ameen ya kwankwasa lockers din kicin din da yatsun sa biyu a hanzarce ta juyo sai ya sakar mata murmushi mai nuna sannu, ya ce, ‘Na ga ba kya amsa sallama, shi ne na ce bari in miki ta bature, watakila ke din Baturiya ce, ban sani ba?�
Ba ta amsa ba, illa juyawa ta ci gaba da cleaning din ta tukuru, da gani ka san aiki ne da ya riga ya zame mata jiki, a ranta ko cewa take kai wannan mutum yana son matsanta wa rayuwata. Why?
Ya tura hannuwan shi cikin aljihun wandon basachi da ke jikinsa yana kallon ta kurum, duk wani motsin ta a kan idonsa ne, nutsuwarta da yaukin ta a komai yana burge sa har bai san adadin mintocin da ya bata a hakan ba can ya ce, ‘Wai ke ba kya magana ne?�
Nan ma ba amsa tamkar da dutse yake magana, ta koma ga juye snacks da ta kammala a cikin babbar roba a ranta ko cewa take wai wannan ina ruwansa da ni ne? A kan me ya damu da ita da zai ce lallai sai ta yi masa magana yana bin ta bashi ne? Ita fa duk wani da ya shafi Hajiya ba ta son gani, amma a zahiri ta rasa me yasa ba ta ko iya hada ido da wannan bako ko iya dubansa. Kwarjnin shi na da ban tsoro, shi kadai amma duk ya cika kicin din.
Ta sha ganin maza masu kyau da cikar halitta a cikin duniya da nan cikin gidansu, amma ba ta taba ganin mai kyau tsararre da ilhama kamar wannan bakon ba, to amma an gaya masa ko mutuwa ta yi ta dawo za ta yi wa jinin Hajiyar gidan nan magana? Ba ta ankara ba hakan nan ko a tunanin ta ba ta kawo zai shigo cikin kicin din ba, ya doso ta cikin daure fuska tamkar bai taba dariya ba tunda uwarsa ta haife sa, ta yi kamar ba ta gan shi ba ta juya ta ci gaba da aikinta, sai ya fizge robobin ya kifar da duk abin da ke ciki a dandaryar kasa ya yi wurgi da robar, ya kuma bi su yana takewa daya bayan daya yana rugurguza su yadda ba za su moru ba.
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page4ï¸âƒ£
Ta bi cake samosa spring-rolls da doughnuts din da ta shafe awanni hudu cur tana aikinsu tun karfe shidda na safe da kallo rugurguje a kasa, tare da kiyasta irin azabobin da za a gana mata a kan wannan snacks, amma wannan ba karamin mugu ba ne, sai hawaye sharrr! To saime? Kafin ta gama tantance what will happen nedt (Me kuma zai faru?) Al’ameen ya kai mata wawura yana kokarin lalubar cikin ta tamkar mai shirin kwashe mata ‘ya’yan hanji da kayan ciki gaba daya cikin gigita, mamaki da tashin hankali ta ce.
“Wayyo Dela, na shiga uku zai kashe ni.�