Sashe 15
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
‘In tsaya, uwarku ta karasa kashe min ‘yar? Ban san me Saratu ta tsarewa Hajiyarku ba haka Faisal, wannan karon ba zan taba amincewa ba!�
Bata kuma tsaya da gudun da take ba, hakan nan hawayen ta ba su bar ambaliya ba.
Tana tsaye tana farke buhun semovita don zubawa cikin ruwan zafi tafasashshe, Aunty Saratu ta rungumeta ta baya, yayin da hawayen ta da ke ta kwarara suka dinga sauka a kirjin Inteesar! A fusace ta juyo, a zaton ta Al’ameen ne ta ce,
‘What a nuisance, Aminu?�
To amma sai ta ga mamarta, da ko a mafarki ba ta zaci sake gani nan kusa ba. Idanuwanta suka bubbude gaba daya tamkar sa fado. Ta kai hannu ta shiga tattaba ta a gigice ta dai tabbatar ita din ce hanci, ido, baki fuska, babu abinda ya canza a jikinta. Ta bude baki kamar mai son yin magana amma sautin ya kakare ya ki fitowa sai dai labban ta da ke motsi yanayin motsin na nufin, “Mamana?�
Aunty Saratu ta janyo ta ta rungume tsan-tsan a kirjin ta cikin yanayin fita hayyaci ta soma cewa.
‘Saratu? Haka Nafi ta maida ke? Allah ya isa tsakanina da Hajiya Nafi, ba zan taba yafe mata ba haka duk jinin ta, in Allah ya yarda sai ya ga tozarci a rayuwa…�
Faisal ya yi saurin toshe kunnensa yayin da gaba daya suka rikice da kuka. Yana ji yana gani ana bin su da mugun al’kaba’i, a kan laifin da ba nasu ba, a kan abin da bai shafe su ba, a kan abin da in da yana nan� ba zai taba faruwa ba!
Yasa hannu ya matso kwallar da ta tarar masa a kwarmin ido, kafin ya ankara tuni sun fice daga kicin din, ya mara masu baya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki. zuciyarsa cike fal da nadamar zuwa Najeriya.
Shin me ya yi zafi haka? Me Hajiyarsa ta yi wa Intisar din sa haka da zafi? Ya san Aunty Saratu mace ce mai dumbin hakuri, tabbas yau an kure ta an kuma kawo ta bango, tunda har ta kai ga furta wannan kalami.
A babban falon Anty Saratu kuka diyar ta Saratu ma kuka, maimakon farin ciki. Tun suna ba Goggo Jummai tausayi har suka koma ba ta haushi ta mike ta na gyara daurin zanin ta tace,
“Jami, na fasa kwanan gidan nan, tunda Saratu da Saratu ba su san yarda da hukuncin Allah ba.�
Jami ma ta ce, “Kya fada dai Hajiya Jummai, kuma tunda komai ma ya zama tarihi, ni ban ga amfanin zubda hawayen ba. Dubi irin wannan duniya da Bello ya shirya masu amma duk ba su gode Allah.�
Intisar ta rike hannun Goggonta ta ce,
“Ki yi hakuri Goggo don Allah, daga yau ba za mu sake kukan nan ba, ban taba zaton Mama za ta dawo ba ne, ko a mafarki.� Ta share hawayenta.
Goggo Jummai ta shafi kanta suka koma suka zauna tana kara yi masu nasiha kan muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi.
A yau kam Antin da diyar ta kwanan bakin ciki da farin ciki suka yi a zaune, in suka ce idanun su sun runtsa ko na sakan daya to sun yi karya, kowanne na bai wa dan uwan shi labarin bayan rabo. Intisar rungume take da kanwar ta Zarah da ba ta san an haifa ba, tamkar ta tsaga kirjin ta ta sanya ta don so da kauna.
Amma sam yarinyar nan ba ta gayawa mahaifiyar ta irin azabobin da Hajiya ta rika gana mata ba ta dai ce ita ke yin girkin gidan kawai, wannan ya dan sanyaya ran Antin.
Daddy ya je meeting Lagos sai a washe gari zai dawo, duk da haka ya yi wa Antin waya ya ji yadda suka iso ta ce sun iso lafiya cikin alkhairi, ya ce idan ya iso a goben sati mai zuwa za su tafi Riyadh su dubo Saratu karama.
Ta ce, “Wace Saratun kuma ban da wannan da muke a kwance tare?�
Daddy ya yi shiru cikin dogon tunani, can ya ce, ‘Aminu ya ce da ni Saratu na Riyadh?�
Ta kara tabbatar da abinda Mal. Sidi ya ce da ita, na cewa Daddyn baya cikin hayyacinsa a duk tsayin lokacin sai ta ce,
‘Shi Aminu ba bako ba ne? Yaushe har ya yi zaman da zai san me ke faruwa cikin gidan?�
Ya ce shi kenan tunda ga Al’ameen a gida, ya kamata a sake mata glasses a kirawo masa ita.
Ita dai a tsorace ta gaishe shi, amma wai sai yake ce da ita wato tun tuni ta zo hutun ‘yar boye take yi mai a gidan ko? To ta yi asarar tsarabar da ya yi niyyar kawo mata…� ta jingina da bango, hawaye na karshe na zubar mata ta ce,
“Ni dama na san wancan mutumin is not my real Dad (Ba shi ne babana na hakika ba), ban kuma taba kullatar Daddy na ba, even once (ko da sau daya).
A kullum ina yi masa uzri, gare ni duk yadda rayuwa ta zo� a karbeta�, ayi mata uzuri da abubuwa guda biyu; Faisal da Daddy Makarfi.�
Aunty Saratu na share mata hawayen da hannunta ta ce,
‘Kin ga Faisal ya dawo?�
Ji ta yi tamkar an kwara mata ruwan kankara, ta zaro ido ta ce,
“Haba don Allah! Allah Sarki Brother!! Wallahi ban gan shi ba sam.�
Antin ta ce,
“Ni dazu da na kusa haukacewa saboda bakin cikin uwar su ko kulasa ma na yi?�
Ta ce, “Ayya Mamar mu! Ina laifin Hajiya zai taba shafar Ya Faisal, ina!�
Sai wasu hawayen sharrr!
Ta ce (cikin rarraunar murya),
“Ni don farin cikin dawowarku ma ke da Ya Faisal, domin Faisal, na yafewa Hajiya har cikin raina.�
Sai Antin ta bi ta da kallo, zuciyar ta cike da mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, bata daukan al’amuran duniya da zafi, ba ta da daukar kunci ko kadan, yanzu ne za a yi mata abu yanzun ne za ta manta tun tana mitsitsiyar ta. Amma ba ta manta alkhairin da mutum ya yi mata ko yaya yake. Saidai ta manta batancinsa gareta.
Tana mamakin irin kaunar da take musu, tana mamakin irin kaunar da take wa Daddyn ta da ‘yan uwanta maza� ina ma a ce wannan shi ne bakin cikin yarinyar na karshe a rayuwa?
Wannan tunanin ya kara mata kauna da tausayin yarinyar, ya kuma dugunzumar da zuciyar ta duk a lokaci daya, ta yadda duk wani farin ciki da ta zo da shi sai ya dushe zuciyarta ta koma bakikkirin. Ta roki Allah kada ya nuna mata ranar da Saratu-Intisar za ta fahimci�
me za ta fahimta?
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page9ï¸âƒ£
Karya Fure Take
Al’ameen na gidan shi tun jiya bayan ya sauke Faisal yana faman aikin takardun tsare-tsaren ginin asibitocin su da fasalin da yake so a yi wa gidansa, wanda zai kasance cikin asibitin. Wayar Ihsan ta katse shi, da ya duba ya ga lambar ta ne sai kawai ya kashe ya ci gaba da aikinsa.
Karfe shida na yamma ya baro gidan ya biya ya yi wa Halimar shi sayayyar su ice cream da dangin sa kana ya wuce.
A harabar gidan ya ga bakin motoci da dama lambar Enugu tabbacin yau gidan a cike yake da ‘yan uwansa, a ransa ya kudurce yau sai sun gaya masa ko fushin me suke da iyayensu.
Ya ratsa ta lafiyayyen falon Hajiya zuwa babban falon gidan ya shiga da sallama cikin muryar sa ta kasaita nan ya tadda su (complete family as earlier). Ba karamin dadi ne ya ziyarci zuciyarsa ba, domin ganin su a hakan ya tuna masa da abubuwa da dama da suka gabata cikin rayuwarsu.
Najib, Faisal, Bello mai sunan Daddy, Faruk, Yasir, Nasir samarin Daddy da sauran kannen da ke bin su sun cika falon sun kawata shi, kowannen su ji yake da boko wanne-ne-ba-wanne-ne ba! Bai san da ya murmusa ba, sai baiwa Daddy labari suke na abin da ya shafe su, to amma me?
Abin ne ya bala’in daure masa kai, ya rikita kwakwalwarsa, ya kasa tantance me yake gani?
Halimar sa ce kwance rashe-rashe bisa doguwar kujerar da Daddy din shi ke zaune, ta yi matashi da kafafusna yana karanta mata labarin kwallon kafa cikin jaridar Punch da su Najib suka shigo da ita. Kamar sun hada baki suka ce,
“Gaskiya gobe za a je bikon Ihsan wa Dr. Al’ameen, mun matsu da mu ganta.�
Daddy ya aje jaridar bisa ruwan cikin ‘yar lelensa, ya dube shi ya ce,
‘Ku kyale shi dai, nake jin wata ya gano yana so ‘yar doguwa kyakkyawa anan din, don kwanaki har man gashi da ‘dryer� ta gashin mata na gani a wata leda da ke hannunsa bai san na gani ba.�
Gaba daya suka kwashe da dariya har ita da ba ta san takamaiman da wa ake cikin su ba, don a kwance take, ta juya masa baya tana fuskantar Anti Saratu da ke shayar da baby Zarah.
To amma shi bai yi dariyar ba, maimakon haka da kyar ya iya daga kafa ya karasa har saitin kanta ya ce, “Halimah!� Da wata irin murya mai sanyi da rashin kuzari.
Da sauri ta mike zaune ba tare da ta juyo ba, ta san dai ko ba jima ko ba dade dole zai san matsayin ta na hakika a gidan, kuma dama ita hakan take jira kafin ta iya yarda su yi aure, wato sani da amincewar Daddy da Mamarta!