← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 90

Sashe 51

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dai-dai lokacin da danja ta baiwa bangaren da take hannu, tasa ma motar giya a guje. Ta yi parking a inda suka tanada domin adana motoci kana cikin sassarfa ta fito, bakar ‘after dress� dinta rataye a kafadunta haka Jakarta na sakale a yatsunta biyu ko file dinta bata tsaya dauka ba tayi cikin gida, karar horn dinta ya fiddo ‘ya’yanta a guje suna “Mummy oyoyo!�

Ta daga karamar ta café ta ce “my dear Dijah, ince ko kinci abinci sosai?� Ta daga mata kai alamar eh, don bata fara magana ba amma tana gane duk abinda aka ce da ita.

Ta kama hannun ‘first born� dinta Bishir tace,

“Kawu na, Daddyn ku na ciki ko?� Ya ce

“Eh, tun dazu ya dawo, amma yace yau sai anyi miki bulala, kin dade baki dawo ba�

Ta bude baki, “Wayyo ni Hajjo, ka ce yau sai buzu na.� Ya ce,

“Ai boye ki zan yi cikin rigata Mummy.� Tana dariya ta ce,

“To na gode Kawu na, nasan bazaka bari Daddy ya duke ni ba.�

A haka suka karisa falonsu tamkar wadanda suka shekara basu ga juna ba. Da sassarfarta ta tura kofar ‘bed-room� din shi, baya nan. Tayi murmushi ta dan saurara don ganin ta inda zai bullo, sai ta jiyo karar zubar ruwa a famfo kadan tabbacin yana bandaki, ta karisa jikin kofar ta kasa kunne ta ce “can I come in? �(Na iya ya shigowa?).

Ya ce, “No� Ta yi dariya ta murda kofar tana cewa,

“Ai ni mazaunai ce, dole a zauna da ni.� Ya ce,

“Idan duwawun ya zama kakkausa, sai a yanke shi shi asa na roba.�

Yana tsaye ne jikin ‘sink� saye da gajeren wando kadai yana wanke hannunshi da kamkamsan sabulun ‘cleopotra� bai ko juyo ya dubeta ba, ita ko jikinta ba inda baya rawa rike da jarida, ya juya mata baya ya soma cuda farin hankicinsa cikin ruwan da ke zuba daga famfo ta ce,

“Pls, Baban Bashir dubar ni, Allah ba wasa cikin lamarina.� Bai dubetan ba dai ya ce,

“Ni kuma nace bazan dube kinba, tunda kin zama kakkausa ba sai in cire in sa mai laushi ba?� Ta ce kaman zatayi kuka,

“Be serious, don Allah?� Ya ce,

“Idan mutum ya dauki al’amarinki da muhimmanci Hajjo shine gaula, to naji zan dauwama a gaula na bana bukatar zama serious, dubi agogonki karfe nawa?� Awoyi nawa kika kara kika barmu cikin yunwa nida yara bayan na gaya miki a daina basu abincin masu aiki?�

Ta langabar da kai gefe guda, kana ta janyoshi ta baya, fuskar ta bisa kafadunshi ta ce, “To bakwa shiga kitchen din da kanku Baban Bishir?�

Ya dan juyo ya dubeta da wutsiyar ido, Hassan ya san Hajjon shi sarai, har yanzu tana shimfida mai wautarta ne yadda ta ga dama, uwar ‘ya’ya biyar a yanzun amma in ta kwaba mai wani shirmen ko dan ta Bashir baya yi ba, ya juya ya cigaba da abinda yake ba tare da ya ce mata komi ba.

A ran sa ko cewa yake, “Allah dai ya shirya min ke.�

To har gobe haka Dr. Hajjo ta ke, malama a sashen Harsuna a (Lagos State Universisty) tana karantar da harshen Faransa zalla. Ta cigaba da magiyar yayi hakuri ya saurareta, ya fito daga (toilet) din zuwa dakin barcin su inda duk ya aje kafa nan zata mayas, tana tirjiya cike da shagwaba.

A dakin barcin su ne ta russuna ta kama tafin kafarshi ya ce, “Wai ke wace iri ce ne?� Ta kakalo wani guntun hawaye can karshen idonta tace “Allah Babansu Basheer traffic congestion ne ya tare ni, kayi hakuri ka yafe don Allah ?�

Ya tintsire da dariya ya dauki jaridar ta yana dibawa. Dr. Hassan Biu har kullum ba mace a idonsa tamkar Hajjo, wautarta kuwa kullum sai abinda ya karu shi dai hakannan yake son kayar sa.

Daukaka kan daukaka suna gani a rayuwa don a yanzu haka Dr. Hassan Biu shine Ministan Kariya na kasa wato (Defence Minister), ‘ya’yansu biyar cif maza uku da mata biyu, Bashir mai sunan Babansu Hidayah kuma Kawun da bata da ya shi a duniya sai Hakimi (Abubakar) da Hafiz, Hannatu mai sunan mahaifiyarta kuma (name-sake) din Hunainah tana ce mata Maama, Dijah itace auta ta kan ce mata (Yaya Dijah) don sunan Yayar ta Hadiza ne.

Ya zauna bakin katafaren gadonshi ta zauna bisa carpet tace, “don Allah bude jaridar nan mana? Allah na kasa karantawa duk jikina rawa ya ke,â€Ya dubeta sosai ya ga yadda ta susuce ya dan dubi shafin jaridar ya ce,

“Shin ina ruwana da (birthday) din Janar Makarfi?� Ta ce,

“Wai wane Makarfin su ke nufi?� “Yace “Tsohon Brigedier General Bello Makarfi, kin san ya fita sharrin ‘coup d’état� (juyin mulki) da su Janar Delsu suka tura shi, a yanzu shine mai baiwa president (shugaban kasa) shawara kan harkokin Mulki.� Ta ce wadanda suka zauna nan ‘opposite� (gida mai kallon) na mu shekarun baya?�

Ya ce� eh, ai tun kan a kamashi suka tashi daga nan, wai ke kin san shi ne? Kin ce don Allah in karanta kuma kin isheni da tambaya kin hanani karantawar, kin san kina son ki karanta ki karanta abunki mana� ta ce “Baban Bashir, be serious don Allah, shin a wane gari Makarfi ya ke yanzun?�

Hassan ya cika da jerin gwanon tambayoyin matarsa kan Janar Makarfi, kishin ‘yan mazan ya motsa ya ce a hasale.

“So what in na gaya maki Abuja ya koma da zama? Sai ki dau mayafi ki yafa ki tafi, isn’t that good?� Hajjo ta kwantar da kai tace “Alasabbinani, maida wukar, ba abinda ya hada ni da shi baya ga Yaya Hadiza da tace diyarta da aka sace tana jaririya, su Hidayah sunyi makaranta daya da yarinyar a Riyadh, har suka kaita gidansu ta ganta ta gane ‘yarta ce Fatima, kuma wai yarinyar ta taba gayama su Hidayah cewa anan Lagos gidansu yake, gidan Bello Makarfi na nan Victoria.

Wancan zuwan da Ambasada dasu Hunainah su kai ai kan maganar ne, muka je gidan a lokacia yana kulle. Ashe iyalinsa sun tashi…� ta kwashe komi dai ta gaya masa tun farkon al’amarin, ta kare zancen ta da cewa,

“Abinda yasa tun tuni ban gaya maka ba, zancen ne naga ba wani ‘logic� (makama) ba, to amma yadda ta dage ‘yar ta ce ta gani, sai duk nima naji jikina na bani yakinin cewa hakanne, ka san UWA fa a kowanne hali dan ta-dan-ta ne, ba kuma zai taba boyuwa gareta ba walau girma, tsufa ko kuruciya.

Kana sane da cewa har yanzu lafiyarta gata nan ne kurum sabida nasihohin mutane, Hassan ka taimake mu ka kuma ceci rai don Allah?�

Jikinsa yayi sanyi lakwas har bai san abinda zai ce ba. Hajjo ta daura hannayenta bisa kafadunshi tace.

“Baban Bashir, farin-cikin Yaya fa shine nawa, bani da kowa a duniyar nan sai ita, ina boye maku damuwata ne kawai akan lamarin nan don bana son tayar da hankalin ku kamar yadda Yaya ta tayar da na Ambasada, ‘pls do something� (kayi wani abu) mana�.

Hassan ya dubi matar shi yana kallon yalwatacciyar sumarta ta filanin usli, idanuwanta duk sun cicciko ya ce,

“Hajjo, ji ni nan don Allah kar ki min kukan nan naki, I’ll try my best (zanyi iya kokori na) amma kin san mutane haka ‘top military� irin su Makarfi dosar su da wani al’amari makamancin wannan sai anyi kyakkyawan shiri, hakannan uwa-uba shaidu, shin wacce shaida muke da ita na cewa ‘yar shi tamu ce?

Wannan kwata-kwata baya a tsarin shari’ah kuma ya haura doka mai kare ‘yancin dan-adam tunda bamu da wata sahihiyar shaida. Abinda yafi yanzu ni zan fara zuwa Abuja inyi bincike in tabbatar in ma har yana da ‘ya mace a gidan, don a sanin da nayi wa Makarfi sanda suke makotan mu ya’yansa tara ne duk maza ba mace ko daya.

Kai mata ma dai da rigma kuke kuma dole a biku da yadda kuke so ana so ko ba’a so, in ba haka ba yarinyar da aka ce ta bata cikin tsumman goyo, a kauye, itace za’ace an gani a birni irin Riyadh, birnin da ya tara al’ummar cikin duniya, ko dayake kamar yadda kika ce din ne UWA ce bazan musa mata ba.

Amma da wani ne Allah ba ma zan sa bakina ba cikin wannan al’amari mai rikitarwa. Idan na tabbatar da komi zan shirya mana ‘visa� zuwa Korea sai mu taho tare da su gabadaya, ni ina cikin hutun sati biyu, ke kuma na san kwanannan zaku shiga ‘long-vacation� (dogon hutu na Jami’a) ko? Sai a shirya mai yiwuwa, hakan ya yi miki?�

Tayi murmushin jin dadi, tabbacin ya faranta mata ta ce “nagode kwarai, Honey. Allah ya kara dankon kauna�.

Minister bai yi sanya ba, a washegari ya bi jirgi zuwa Abuja, saida yasa akai mai kwakkwaran bincike kamin da suyiwa gidan tsohon Brigedier Bello Makarfi tsinke shida ‘yan rakiyarsa, amma cikin sa’a basu sami ganin sa ba yana dakin ‘meeting� tare da shugaban kasa.

Duk da haka Hassan ya baiwa sakatariyar shi ta gida katin shi wa Advisern, ya kuma bar daya cikin yaranshi yayi masu bincike kan ‘ya’yan Brigedier cikin siyasa irin tasu.

A washegari ya tabbatar mai akwai Inteesar ‘ya mace daya kwal cikin ‘yan mazan ‘ya’yan shi amma a yanzu haka uwarta bata gidan tana hannun kishiyar uwarta ne.

Ya ce shima ya yi nasarar samun wannan cikakken bayanin ne daga bakin Ado direban gidan, ta hanyar hilatar shi da cewa ‘ya’yan Birgediyan ne suke birgeshi da da mace a cikin su da ya aura, shine yake gaya mishi hakan.

A ranar Hassan da jama’arsa suka baro Abuja. Yana cike da dokin ganin farin-cikin Hajjon shi, cikin wautarta watakila tace goyon shi zata yi har da majanyi da juyi.

Ya ko gani, har ya gode Allah.

Da wannan suka durfafi kasar Korea don kulla mai yiwuwa. Zuciyar Hajjo dai bayan farin-ciki cike ta ke da taraddadin kada Allah yasa su je su kwaso mutane kasa-ya-kasa a zo a ce Bello Makarfi ya sake canza garin zama.
Chapter 51 · 0% Book details