Sashe 41
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Intisar daga inda take tsaye ta dinga dariya ta ce, “Goggo menene kuma kwantan ‘yammata, ai mace bata kwantai komi girmanta, zata samu kato dai-dai girmanta� Faisal sai ya juyar da kai, bai san san da yaja tsaki ba, yayi kicin-kicin da fuska, ya ce,
“Wai ke Goggo baki da zance sai aure-aure, to har nawa Babyn take? Ko sakandire bata gama ba fa, ita wannan kifin rijiyar ma tana fita ne balle wani mummunan ya ganta yace yana son ta?�
Ta harare shi a ranta tace bari in tura ma haushi nima, kaima ba kana da budurwa ba? Ta ce a ladabce.
“Wa ya ce ma bani da saurayi Ya Faisal?� Faisal ya fiddo ido cikin barazana ya ce,
“Eh, Baby kin san abinda kike fada kuwa?� Ya kara bude baki kaman zai kara cewa wani abu, kafin ya bara cikin kada ido ta sake cewa,
“Allah Goggo ina da saurayi, amma balarabe ne mutumin Turkey, shine malamin chemistry din mu a Riyadh sunan shi Dr Alhassan, ya taba zuwa nan ma kuma ki tambayi Mama.� Ta kara duban Goggo da dukkan idanu, tana murmushin da ke kara mata kyau da kwarjini, lokaci daya tana satar kallon Ya Faisal da wutsiyar abnormal (marassa lafiyan) idanunta don ganin irin sukar da kalamin ta ke yi.
Ba shakka ta ga sauyawar fuska da idanuwan shi bakidaya irin yadda bata taba gani ba, taci gaba da cewa,
“Baki gan shi ba Goggo, dogo kyakkyawa jawur da shi, idanun nan kamar na Ya Najib, hancinsa zirit irin na Ya Faisal, muryar shi.�
Haba! Faisal ya gama zuwa wuya tun kamin ta karasa, tun can fa sauraron ta yake ‘absent-mindedly� da tunanin ba Saratu-Intissar ke wannan maganan ba, yarinyar da har kullun yake gani ‘as a kid� bai san yaushe bakin ta da idanun ta suka bude har haka ba, ita ce har take yabon kyawun namiji, abin mamakin ma har a gaban sa!
Bai san sanda ya cafko hannayen ta duka biyu ba ya yana kallon ta cikin ido da idanun shi da suka rine ‘completely� har wani (blue-blue) suka koma suka rine da abin da bata taba gani ba, ya durkusar da ita gaban Goggon, shima binta yai suka durkushe yana huci kaman yunwataccen zaki ya ce,
“Maimaita abunda kika fadi yanzun Intisar, Goggon bata ji sosai ba� ta tsorata, ta razana kwarai da yanayin sa haka tsatstsauran rikon da yayi mata ya gigitata, sai tasa kuka. Goggo ta yi salati ta ce,
“Sakar ta, sakar mata hannu, sake ta nace, idan ka karyata fa?�
Da alama bai jin ma abinda Goggon ke fadi domin gabadaya baya a hayyacin sa yace
“In an karya ta sai me Goggo? Yanzu wannan tsakuwar yarinyar ce take yabon kyawun maza, ina ta koyo wannan fisarar?� Ta ce,
“Na fada din, Goggo shekaran jiya waya na yi mishi, in gaya mishi Daddy ya dawo, wata Inyamura ce ta dauka tace min wai…� ya kara tsananta matsar da yayi wa hannun ta tare da murje yatsun kafar ta da karfi da nashi yatsun, ta saki kara don zafi amma bakin ta bai mutu ba, hakannan bata yi shiru ba da gaya wa Goggon yadda sukai da yarinyar shi a waya. Ya ce,
“Nace da ke na santa?�
“Ya santa mana Goggo, cewa tayi fa wai ya shiga wanka, idan bai san ta ba, ya za ai har ta san inda yake wanka? Wa ya sani ma,…�
Faisal ya soma daldalle mata baki da yatsun shi da karfi nan da nan dan bakin ya haye, dai-dai lokacin da Najib ya shigo, koda yake ya dade yana kallon su yana son tirsasawa zuciyar shi rashin amincewa da abinda kwakwalwar shi ke son fahimtar da shi, ya shiga tsakani ya janye kanwarsa ya ce,
“Wonderful! Abin mamaki, abinda cikin gidan nan ba wanda ya taba gani, abinda ko a tunani ba’a taba kuskuren tunanowa ba, wai Faisal da Intisar yau aka gani a rana?�
Su kan su sun ji kunya ba kadan ba, don haka ba wanda ya amsa mishi kowanne sai huci yake kaman ya cinye dan uwan sa, Goggo Jummai ta kyabe baki ta sunto wani goron a habar zanin ta, ta kwashe wanda ta gurza a magogi da farko ta hambuda a baki tana mamulawa ta ce,
“Ai kai kadan ka gani, baka ji ba har tonon asiri sukewa junan su,� Faisal yayi tsaki ya fice har zuwa lokacin idanuwan nan suna rine a (blue) kamar na wanda ya kama matar shi da kwarto, ita kuwa ta cigaba da gaya masu yadda suka yi da yarinyar shi a waya bata ko sanya comma, (wakafi) balle fullstop (aya) zuba kawai take kaman ‘ya’yan kanya Najib ya daga mata hannu “wait, excuse me please Inteesar, for Allah ’s sake, ina ruwan ki da budurwar Faisal, kin isa ki hana shi yin budurwa ne?�
Ya zazzaro mata manyan idanun shi, ta sunkuyar da kai cike da matsananciyar kunya kafin ta daure ta ce,
“To Ya Najib shima ina ruwan sa don nayi maganar saurayina sabida Allah sai ya murmurde ni yana neman balballa ni?�
Najib yayi murmushi ya juyar da kai, kwakwalwar shi kaman ta tarwatse, yanzu kam ya tabbatarwa kansa abinda tun shigowarsa zuciyar shi ke gaya mishi yana karyatata da gangan, amma sai ya basar tunda mai ilmi ne, ya juya ga Goggo da son wanke mata nata zargin ya ce,
“Goggo da ganin Saratu kin san anyi irin kannen mijin nan ne, masu kishin son da Yayun su ke nunawa matansu, masu so a raba musu kauna da matan Yayyunsu ‘equal� (dai-dai wa daida) wanda kuma wannan ba zai yiwu ba. Mata fa matsayin ta a zuciyar mijin ta ya zarce yadda duk kike tsammani, kasancewar ta wani bangare na gangar jikin sa, zuciyar sa da hutun sa, zata bashi abinda ke kanwa bazaki taba bashi ba, zata kula da shi da rayuwar sa ta hanyar da ke kanwa baza ki taba yi ba.
Hakannan daga jikin ta ne zai sami ‘ya’yan da zai yi alfahari da cewa nashi ne, mallakin shine, ta yaya matsayin ku zai zo daya? Kazalika shima Faisal yana tsananin kishin ki so wani fiye da wannan ingantaccen son zumuncin da kukewa juna, yaya za kuyi rayuwa da haka?
Don haka dole ya ji zafi da farko, amma daga karshe dolen shi ya dangana ya danka ragamar rayuwar ki ga abokin rayuwar ki na har abada bayan shi, don kuwa shi ba auren ki zai yi ba ko a garin gaba-gaba muke bare gari na Addinin muslinci, so kusa ranku a inuwa sassanya, ku yayyafawa zuciyoyin ku ruwan sanyi, dole kowannen ku zai sami abokin rayuwa na daban. Ba rarrashin ki nake ba, gaskiya kawai nake gaya miki. Do u get me (kin fahimce ni?)�
Sai ta mike tana kunkuni na alamun rashin yarda, sai dai wannan Yaya Najib ne bai yuwuwa ya fadi ta fadi, yanada wata kima mai yawa a idonta, amma da ba shi ba ne da tace da shi;
Idan har auren kowannen su na nufin kawo sauye-sauye da canje-canje ne cikin rayuwar so da kauna, shakuwa da ingantaccen son zumuncin da suke wa juna ne ita da Faisal, to ita ta yafe nata! Zata zauna haka tare da Ya Faisal a gida daya, a gaban Daddy Makarfi, matsayin yayanta kuma nata abokin rayuwar har abada!! Ita dai bata son zancen budurwar Faisal ko kadan, za kuma su ci gaba da fada har da ba hammata iska idan ta sake jin zancenta.
How much do you like this story?
5/9/22, 09:56 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Su Goggo Jummai basu tafi a ranar ba sai washegari Laraba, Baffa yace Intisar ta shirya su tafi tare ta karbowa Daddy rubutun da za’a fara yi mai na tsarin jiki duk sati, in yaso sai su dawo ita da direban da zai kai su. Suna ta jiran Ado da ya tafi cefane har shabiyun rana bai dawo ba sai Daddyn ya kira Faisal yace ya je ya kai su.
Ko kadan ranta bai so tafiyar nan da Faisal ba, ita yazu ko hanya bata so ta hada su sabida haushin sa da ta ke ji akan budurwar sa, har Addu’a take garin Allah yayi ya sake wayewa ya koma inda ya fito.
A motar Hajiya (bolbos6) aka yi tafiyar, Baffa da Goggo na gidan baya suna taunar goron su suna hirarrakin su tamkar wasu yara sabbin aure ga sanyin A/C na ratsa su, Goggo har da su aje mayafi a gefe da ganin su dai kinga ‘yan gatan tsoffin da ‘ya’ya suka hucewa takaicin duniya, jikokin su Faisal da Intisar na gaba.
A yau dressin din sa (bery-simple) wato sanye yake da caftan na shudiyar shadda ‘yar mali kalar ta kama sosai (dark-blue) kansa ba hula, silipas ne ‘chips� a kafar sa yana murza sitiyari cikin gwaninta, kamar kullum parmanent (tabbataccen) kamshin sa na (5,000 Doller Perfum) ya na tashi a hankali cikin motar cooly, wannan kamshin dake sa mutum gyangyadin da bai shirya ba.
Ita ko ‘yar lelen gidan Makarfin sanye take da kamfala shadda ghanilla baka da aka yiwa dinki senegalese, maimakon dankwalin kayan ta yi amfani ne da siririn farin mayafi da yake dinkin babba ne sosai, baka ganin komi nata sai shacin kayatacciyar fuskarta dake manne da farin (medicated-glass) dinta sai ko santala-santalan yatsun hannunta farare sol kaman ka taba jini yayi tsartuwa data kawata da zobba na farin zinare wato (white-gold) kwaya biyu rak, ba abinda ke tashi jikin ta face sassanyan kamshin turare ‘zandaria� bakin ta cike da chingum mai tsananin kamshi (hubba-bubba) tana tauna (bery-gently). Daga ita har Faisal kowanne shan kamshi yake wa dan uwan kaman bai taba sanin sa ba dadai duniya.