Sashe 76
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Don haka na kalubalanci zuciyata na gargadeta da kakkausar murya a kan haramci da rashin dacewar abinda ta ke so! Haka na samu taimakon kiyayyar da mahaifiyarsu ke mun ya zagwanyar da 50% na soyayyar, kawai dai na bashi matsayin wani mutun precious a zuciyata (wato mai darajjah) kuma har yau, har gobe hakan ne ba abinda ya canza. Domin in har zan manta Faisal wanene a gare ni? To kuwa zan manta wane ne Daddy Makarfi.
Yayi min dimbin alheri kwatankwacin na Daddy na, tun ban san kaina ba. Kawai na budi ido na gan shi tare dani, cikin karimci da ingantacciyar kulawa.
Ko a sanda uwarsu ta yi min shamaki da su, na kuma alkawarta ma raina na rabu dasu har abada, na tambayi kaina a lokacin anya zan iya rabuwa da Faisal? Na bawa zuciyata amsa nan take da cewa, aah! Faisal wani mutum ne mai muhimmanci, kima da daraja a zuciyata da bazan taba iya rabuwa da shi ba. Haka lokacin da ya bar ni ba zato ba tsammani, na yi kuka nayi kewa na shiga kunci mara misaltuwa.
A hankali na dinga sanyawa zuciyata salama tare da kokarin yakice shi a raina amma na kasa, sabida wata ingantacciyar kauna ce nake yi masa ta daban a zuciyata.
A sailin ne kuma Alameen ya shigo cikin rayuwata. A lokacin da zuciyata ta rasa aboki, take cikin kadaici. Lokacin da nake mai tsananin bukatar taimako. Sai ya zo da wata irin soyayyah mai shiga rai ya shimfidata a zuciyata, irin wadda ban taba ji ba. Irin wadda ko a mafarki ban taba yin na tsintar kaina cikin ta ba.
Soyayya ce irin wadda ko muryar sa na ji, sai na ji gabban jikina, zuciya zuwa kwakwalwata gabadaya sun amsa! Idan dosowa yayi inda na ke, babu inda baya girgiza da kadawa a jiki na. Na tambayi kaina ashe dai wannan itace soyyar ta hakika, waccan da nayi duk a cikin gigin kuruciya ne kuma sabo da shakuwa sune tubalan da suka ginata a birnin zuciyata.
Wannan ita ce natural love kuma love at first sight wadda daya bazai iya rayuwa mai dadi ba tare da soyayyar dan uwansa ba, wadda kobo ko sisi ba zai iya sayen ta ba; saukakka ce daga indallahi!
Kwatsam, kaddara da mutuwa suka yi mun yankan kauna, a lokacin da muke gab da cikar burin zuciyoyin mu. Duk da cewa ta wani bangaren zan iya cewa ni na jawo amma na amince kaddara gaba take da komi.
Na ji ciwon rasa Alameen yadda harshena bazai iya furtawa ba, zuciyata bazata iya kwatantawa ba, ba don na yi imani da Allah da duk abinda ya saukar a gareni, mai dadi ne ko mara dadi? Da na tabbata babu abin da zai hana ni fita daga hankalina, sai dai komai ina dangantashi daga Allah ne.
A duk sanda na tuna Alameen ina yi masa adduar neman rahma kuma na tabbata wannan ita ce kauna ta karshe da zan nuna masa. Ni kadai na san ciwon da zuciyar nan ke mun Hunainah, ni kadai na san kadaici da maraicin da nake jin ya sameni.
Na dauka wannan ne lokacin da Faisal zai tausaya mun, ya waiwaye ni ya rungumeni, ya bani soyayyar da na rasa ta dan uwan sa mu debewa juna kewar Alameen, to amma abinda na fahimta shi a yanzu kiyayyar da yake mini da da hali, da ya koreni daga gidansu, da da hali, da ya dauki fansar dan uwansa a kaina. Yana gani na muguwa mayaudariya kuma maciyiya amanar soyayya.
Na rasa yanda zanyi da zuciyata Hunainah, na rasa wanda zan fadi wa abinda ke damuna idan ba ke ba. Na san ke kadai kika san irin ciwon da nake ji ke kuma ce kawai zan iya gayamawa na ji sanyi a zuciyata Hunainah.�
Hunainah kuka yar uwar ta Intisar ma kuka. An rasa mai rarrashin dan uwansa. Ita Hunainar da aka gayawa labarin don neman kwarin gwiwa da shawararta sai tafi victim din ma karaya da zub da hawaye. An rasa mai lallashin wani. Hakika tafi yar uwarta jin ciwon wahalolin da take fuskanta a rayuwarta. Tunda uwarsu ta haifeta kawo girmanta bata taba hutawa ba. Bata taba ganin mai SIRADI iri-iri a rayuwa irin Saratu-Inteesar ba. Daga wannan bakin-ciki ya gushe sai wannan ya bullo. Gaskiyarta ne tabbas ba don ta kasance yarinya mai karfin imani ba da ta fita a hankalinta. Kalaman Hunainah ga yar uwarta shine;
“Ni na tabbata Ya Faisal na son ki. Wannan son da yake miki tun kina tsumman goyo ba abinda ya canza domin soyayya ta gaskiya bata taba gushewa kamar yadda bata tsufa, saidai masoyan su tsufa. Balle ku da yanzu nema kuke kan ganiyar kuruciyarku.
Kawai dai zan iya cewa yana jin zafin ki wanda na san as time goes on zai daina ne, ki fidda damuwar komi a ranki, domin karatun ki bana wasa bane in bah aka ba zaki sha mamakin mugun kayen da zaa dinga yi miki.
Ki bar komi a hannun Jallah mai kowa mai komai, wanda Ya halicci Faisal, Ya halicci Alameen, Ya halicci Inteesar ya sanya soyayyar juna a zukatan su. Ki bashi ikon zaba miki abinda ya san shi ne mafi alkhairi a rayuwarki.�
Hakika nasihar yar uwarta ta nutsar mata da zuciya. Tayi damarar karfafa zuciyarta da kokarin yakice duk wata damuwa da ke damunta, tareda daura aniyar fuskantar karatun ta da dukkan iyawarta. Gabadaya daga Alameen har Faisal ta sanyasu cikin wani fai-fai na tarihin rayuwarta ta baya inda ta budewa kanta sabuwar rayuwar data tarar a gaba.
Duk dai a lokacinne kuma tabi jirgi zuwa kasar Korea domin gano mahaifiyarta kamin lokacin da aka diba musu na fara karatun ya cika. Inda ita Hunainah hutu ne zata je na karshen semester wanda daga shi in ta koma zata shiga mataki na uku. Hidayah da maigidanta Najib sun koma gida Nigeria inda Hidayar zata fara karatu a jamiar Enugu inda mijin ta ke aiki kenan.
Daddy ya zaba mata Al azhar dake Egypt ne sabida dadadden burin da ya dade dashi kan son Saratun ta zamo mai amfani ga dumbin alummah da fasahar da Allah Ya bata, wannan shine dalilinsa na zabar mata Medicine and Surgery.
Hakika sun ji dadin hutunsu a Korea tareda mamarsu. Duk wani daddaurewa da takewa Inteesar a da, yanzu ta daina jan ta take a jiki fiye dasu Hunainah. Ita kadai tasan dimbin tausayin da yarinyar ke bata wanda ita din bazata iya maganta mata matsalolin da Allah Ya daura mata a rayuwarta ba.
Gabadaya ta kare, sai tsayinta da farin kadai dama jikin ba wani jiki na azo a gani ba. Ta kan yi mata nasiha da ta kara dayanta Allah a alamuranta yana sane da ita, ba wai mancewa yayi da ita ba.
Da sannu zata samu madawwamin farin-ciki a rayuwarta kamar kowa. Hakurin ta da kudurin ta na alkhairi a kan kowa, ba zai tashi a banza ba.
A lokacin Haj. Hadiza cikin ta ya tsufa sosai, haihuwa yau ko gobe. Zahrah an sanyata a nursery tayi wayo sosai ba abinda bata cewa. Ta gaya musu Daddyn su Hunainah yayi retire suna jiran kwanakin da aka deba musu su cika su koma gida bakidaya. Su Inteesar sun ji dadin hakan sosai.
Daya ga watan Junaiuru na sabuwar shekarar suka koma makaranta. Inteesar ta samu sauyin rayuwa ta fannnoni da dama, haka tsarin karatun Al-azhar yana burgeta komai cikin nutsuwa babu takurawa. Suka durfafi karatu babu kama hannun yaro, balle data fahimci abin na yi ne, mai wasa sai ya kwashi kashinsa a hannu sai ta kara dagewa tareda bada himma sosai.
How much do you like this story?
5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four
*@Takori*
Page6ï¸âƒ£
Bayan Watanni Uku
Lallai babu cutar da Allah ya saukar a doron kasa ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba. A yau Hajiya Nafisatu Bello Makarfi, ke sauka daga matattakalar jirgin KLM cikin filin jiragen saman da ke garin Kaduna. Dr. Rehab Mohammed tare wasu daga likitocin asibitin meritime su biyu sune suka yo mata rakiya daga Birnin Miami da lafiyarta da hankalin ta sumul kalau, inda yayan ta Faisal da Nasir suka zo taryenta, kar kaso ka tona zuciyar su mai cikke da godiya ga sarki Allah da ya baiwa mahaifiyar su lafiyarta sumul kamar ba ita ce ta tafi bata san abinda take yi ba. Suka rungume juna daya bayan daya cike da kewa da farin ciki, a yayin ne wasu hawaye marassa dandano suka zubo mata.
Ba komi ta tuna a lokacin ba face ranar da Alameen ya zo ya dauketa a air-port zuwa gidan iyayen ta ranar da ta dawo Dubai, kuma ranar da ta kasance ta karshe a tsakanin su. Ashe wani bakin cikin na nan yana jiran ta, shine rasuwar mahaifiyar ta Hajiya Iyami. A nan kuka ya zamo mata sabo.
Yayan ta sunyi nufin tafiya da ita gidan mahaifinsu inda ita kuma ta nuna aah, suje su fara rokar mata gafararsa tukunna, bazata koma masa gida ba da yawunsa ba, kuma ta san har ga Allah ta zahince shi kwarai da gaske, in bai yafe mata ba ta san hakkin sa kadai bazai barta ba. Baa maganar hakkin Saratu da Saratu da ke kanta.
Ta roke su su nema mata gafarar wadannan bayin Allah kafin ta zo da kanta neman gafarar su. Ta tabbata hakkinsu ke ta dawainiya da rayuwar ta.
Komawarsu gida suka tadda labarin duk suna asibiti, Ihsan ce ke nakuda tun shekaran jiya haihawar ta zo da tangarda, daga karshe dole mahaifinta ya sa hannu aka shiga da ita dakin tiyata bakunan su cike da adduoin samun saa domin hakika ta jigata, duk wani mai imani dole ya tausaya mata.
To alhamdullahi an yi nasarar fiddo jariri katoto da shi lafiyyaye. Daddy ya amshi Babe da niyyar yi mishi addua da lankaya mishi kalmar shahada amma sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske! Yayi tazbihi ga Allah ya tsarkake shi a zuciyar sa, ya kara imani da buwayarsa da isar mulkinsa akan komi.