Sashe 22
Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk ta dabarbarce, umh, ita kadai ta san azabar da Ya Aminu ke gana mata wajen koyar da karatun nan, duk magana daya ya falla mata ‘ya’yan carbin karfe wai ta fiya jakanci, bayan kuma har ga Allah tafi Khalil fahimtar karatun, amma shi baya dukan shi,ta yi shiru ba ta ce komai ba sai da ta kara tambayarta a karo na biyu, sannan ta ce,
“Ki yi hakuri Mamana, cikina ne yake ciwo.�
Ta ce, ‘To ba sai ki fada min baby na in ba ki magani, sai ki yi shiru ki zauna ciki yana ciwo? Abinci ma ba ki ci sosai ba ya za ai ciki ba zai ciwo ba, tashi maza ki ci sausage rolls din ki ne na yi miki ki tafi wurin Ya Aminu karatu, ko kina son gobe Anti Magret ta buge ki?�
Ta girgiza kai, ba da son ranta ba ta ci kadan ta dan kurbi ruwa ta dau littafin ta da fensir ta tafi babban falo inda ake karatun.
Abin da ta fara ji da shigar ta shi ne.
“Kin yi latti, kazama mai shan majina, kneel down�. Ta shagwargwabe fuska tana duban Faisal tamkar mai neman taimako, ya rausayar mata da kai shi ma kamar ya yi kukan alamar su duka zai doke su. Ya ce cikin tsawar da ta sa ta sakin dan fitsarin da ya fara tarar mata.
“Ur hands up, ur kneels down?� Wato ta tsugunna a kan gwiwoyinta ta daga hannuwanta sama, ta yi yadda ya ce don tsira da lafiyar ta, amma duk da hakan ba ta tsiran ba, ya tsula mata carbi ya ce in ta yi kuka mai sauti sai ya ci uwar ta, ta kunshe baki, kuka kamar ya kashe ta, duk yaran jikin su ya soma rawa, don idan ya soma dukan mutum daya to kowa ma sai abin ya shafe shi, suka ci gaba da karatun a haka duk suna tsorace da shi, sai da ya ga dama ya ce ta zo ta zauna ta yi nata.
Yana nuna mata tana shan tsala, to kuka bai bar ta ta gane komai ba, sai ya zuba mata rankwashi kwaf, a tsakiyar ka ya ce,
“Uwar ki ne ta ce da ke tara a tara da daya sha biyar (9 +1 = 15)?� Ta nutsu, ta hada daidai, ya ce “To ko ke fa, daga yau ki ka sake kuskuren lamba ko daya ba zan gyara miki ba sai dai in dura miki fitsarin Bombino.� (Bombino sunan karen da yake kiwo kenan). Da haka karatun ya kare.
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
Juma’a 21 Jumada Thani
Abinci ake ci bisa dining table kamar yadda yake a al’adar gidan. Furkan ne tsakanin Intisar da Aminu, Hajiya ta kiftawa Aminu ido za a yi mugunta kenan, ya ce da Idris ya miko masa ketch-up (tumatirin kwalba) sai ya faki idon kowa ya janyo har da kwalbar pepper irin attaruhun nan da Larabawa ke sarrafawa cikin kwalba ya zazzaga ketch-up kadan kafin ya zazzaga yajin pepper din kusan rabin kwalbar a plate din shi ya cakude shinkafar ‘fried-rice� din shi, yau kam ya kudire Saratu ba za ta ci abincin ranar nan ba.
Hankalin ta na kan T.V inda ake watso shirin da take matukar so na Tom & Jerry, ya faki idon kowa ya sauya masu plate ya janyo nata ya ci gaba da ci hankali kwance, ta cika cokali ta kai bakinta ba tare da ta dubi abincin ba ta tauna ta hadiye, ba shiri ta furzo shi waje cikin plate din Daddy da Hajiya ta zazzaro ido abin dariya ta ture plate din ta mike tana tsalle da ihu.
Daddy ya mike ya kamo ta ta fincike ta yi bandaki da gudu, ji take tamkar ta tsige fatar bakinta ta huta da wannan azaba da ba ta taba ji ba.
Hajiya ta fusata da abincin da aka furzo mata ta ce, “Dubi sangartar banza don Allah, yarinya ba kwaba ba tsawatarwa da can tunda ta fara cin abincin ba ta ji yajin ba sai yanzu da ta koshi?�
Ba wanda ya tanka mata sai Anti da ta mike ta bi bayan Intisar din ta, Faisal ya janyo plate din Saratu ya dibi kadan ya kai bakin shi, ba shiri shi ma ya furzar ya ce,
‘Wuh! Allah masifar yaji, ci ka ji Daddy?�
Aminu ya harare shi ya ce,
‘Wa ya sa ta ta zuba? Ina kallonta tana ta zazzagawa kamar ‘yar kauyen da bata san mene ne a ciki ba�
Daddy ya dago a hankali ya dube shi na dan lokaci, kamar mai son fahimtar wani abu a tare da yaron, bai ga komai ba illa tarin kuruciya fal a cikin kan shi. A yau kam ya nuna masa bacin ran shi a fili ya ce,
“Ko kadan bana jin dadin yadda ka ke mu’amala da kanwar ka Aminu, kai ba ka ganin Saratu karamar yarinya ce ne? Kai da ka ke babba da ya dace a ce ka hada kan dukkan kannen ka ka rungume su, sai ya zamo kai ne ka ke nuna bambanci? To su kuma kannnen na ka su koyi me kenan daga gare ka?
Jiya ina ji fa kana tsula mata carbi wai ba ta iya karatu ba, to ba haka ake koyar da karatu da azaba ba, idan har ba za ka koya mata yadda ka ke koya wa sauran ba, ka bari na gode.
Amma daga yau sai yau, kada ka sake taba lafiyar Saratu da sunan duka, don uwar ta na maku kawaici ba zan zuba maku ido ku illa ta yarinya ba, once and for all, ka kiyayi Saratu Ameenu!.�
Hajiya ta aje cokalin da yake hannunta ta dubi Daddy a yatsine kamar za ta yi magana, ko me ta tuna? Oho! Ta maida bakin ta ta tsuke, can kuma ta ja wani dogon tsaki tsuuu! Ta ce,
‘‘Tashi mu bar wurin nan Aminu, maigida ya zo mai tabarma a bakin kofa ai sai ya nade kayarsa, mu nan ba wurin zaman mu ba ne na masu uban ne.�
Ta fada cikin yi wa Daddyn gatse, amma shi din bai tashin ba, kwantar da kai ya yi ya yi ta bai wa Daddyn hakuri har da kwallah. Sai da ya tabbatar masa ya yafe masa tukunna.
Wannan na daga cikin halayyar yaron da har kullum take sayo masa mafificiyar kauna a zuciyar mahaifin shi. Zai yi komai, zai bata wa kowa, amma ban da wadannan mutanen guda biyu; Daddy da Hajiya.
Mutum ne da ya iya takun rayuwar shi, da wuya ka fahimci abinda yake ciki. Yana da taka-tsantsan cikin dukkan al’amuran shi mawuya ci ne ka ce yau ga ta inda ya kuskuro ka, sai dai da yake an ce wai zuciyar mutum birnin sa.
Haka ne Al’ameen mugun mutum ne na karshe ga wanda ya tsana, sai dai muguntar sa tafi yawa a kan Intisar.
In kin san wata kalma wai ita ‘yan-ubanci, to Al’ameen Bello ne shugabanta. Yana son uwarsa, yana son kannensa, baya son kowa ya rabe su saboda matsananciyar kaunar da yake wa Daddyn shi. Yana da ra’ayin rikau na Malam Bature kan single nuclear family life, bai ga dalilin da Daddy zai bata masu family ba ta hanyar kawo wasu can.
A da, kafin Dady ya auri Saratu yana matukar shiri da ita, haka ko san da take karatu a Edeter musamman ya kai mata ziyara har sau biyu a matsayin ta na kanwar ubansa, yana jin dadin mu’amala da ita, kasancewarta mace mai ilimi irin yadda yake so, kuma wadda ta rage masu cikin dangin ubansu kaf, sai Baffa da Goggo.
Amma tunda ta zabi zaman kishi da mahaifiyar shi shi ma ya ce to mu buga, in ya so mai sa’a ya kwaci Daddyn.
To haka Aminu ke ta azabtar da baby Intisar kullu nau’in azabar yau daban ta gobe daban. Har sai da ya zamanto Baby in ta hango Aminu a bakin gate a guje take komawa dakin Mamarta tana haki kamar ranta zai fito, ko kuma wadda ta ga dodo, sai dai ta bude baki ta ce ga abin da yake mata ina! Tana masifar tsoron sa, tun Anti Saratu ba ta ganewa har ta fahimci baby na gigicewa in ta ga Aminu, haka ko muryar shi ta ji daga waje ta nutsu kenan, tun kuma ranar da ya hana ta shan majina ba ta kara ba, majinar ma kanta tsoron ta take ji, bini-bini tana yawo da tissue tana cewa da ‘yan uwan su goge mata, kada Ya Aminu ya yanke mata hanci ko ya ba ta fitsarin Bombino.
Shi ko in ya ga Anti Saratu a wuri ya soma yi mata wakar come on beautiful baby kenan ko taso tambayar baby sai ta fasa, ta kan dauka don yana matsanta mata wurin karatu ne.
Ranar wata Asabar ba aiki daga Aunty har Daddy suna gida ba su je ko’ina ba. Hajiya ce dai ta tafi Cape-Town can South Africa harkar gwala-gwalan su, kafin ta tafi sun shirya a nakasta Intisar yadda mutane za su daina sha’awar ta ta hanyar gurgunta wadannan kafafun nata ta zama gurguwa ta daina wannan tafiyar tata kamar ta mage, ita kuma za ta taho mai da mota End of Discussion (da ‘ya’yan gata ke yayi a lokacin) da ta yi masa alkawari. Aminu yana matukar tsoron Babansu yana kuma masifar son Hajiyar shi ta yadda duk abin da ta nuna ba ta so shi ma daga ranar ya tsane shi kenan.
Rashin imanin da yake ganawa diyar Aunty Saratu ba wai halin shi ba ne domin dai shi mutum ne mai son kananan yara da son wasa da su shi yasa yake son Khalil.