← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 90

Sashe 39

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubuwa da yawa na faruwa a bayan Al’ameen masu dadi da marassa dadi. Taso a ce yana tare da su a yanzun tamkar sauran ‘yan uwan shi, ta tambayi kan ta ko maiyasa Al’ameen ya gujesu, baya ko tuna su?

Bata sani ba, duk a kan nadamar abinda ya aikata ne ga ‘yar da ta tsana fiye da kowa Al’meen ya guje su, har kullum har kuma zuwa lokacin ya kasa daina ganin kansa a matsayin azzalumi akan Saratou.

Ya cigaba da cewa, “Don abinda zan fada ya zamo darasi a gare su.

Bana nadamar zamowana soja mai kare kasarshi takowannne fanni, kamar yadda har gobe ba zan yi ba.

Abinda zan fadi muku yanzun ina so ne ku dau darasi kan cewa a wannan zamanin da muke ciki, babu aboki nagari, babu wanda zaka amincemawa, abokai sai su kai ka su baro ga fitinar da bazaka iya fidda kanka ba, su tsundumaka cikin masifar da baka san farko balle karshenta ba.�

Ya mike tsaye, hannuwan shi ya sarke a bayan shi ya juya masu baya cikin tuno tsohon bacin rai na wani abu daya taba ma mutum zuciya matuka, dukkannin su sun yi tsit ko tari kwakkwara babu wanda yayi, su dai kawai so suke su ji me ya kai Daddyn su ga abinda suke da tabbacin ba laifinsa bane, to me ya tsunduma shi?

“Rannan ina zaune a falon Janar Benga, ina sauraron fitowar sa a sabili da kiran gaggawa da yayi mani, sai na iso kuma a dai-dai lokacinda aka ce yana ganawa da baki, na kishingida cikin kujerar falon farko da zummar in jira shi, to amma sai na rika jiyo tashin muryar sa yana cewa da bakin sa shifa ya gaji da tsarin mulkin president (mai ci a yanzu) sabida yadda ya hana masu yin yadda suke so kamar yadda suka yi tsammani, suka kuma yi yarjejeniya da shi kafin su tsaya masa ya samu ya haye, su shirya juyin mulki kawai su turani in maye gurbin sa domin ni ina da sanyi, zan bar su su yi yadda suka ga dama da kasar mu, amma muddin suka bijiro min da bukatar su naki basu goyon baya, zasu shirya min tuggun da zan yi nadamar shiga na soja.

A lokacin na fito, ko ganin abinda yake gabana bana yi sabida tashin hankali, don nasan su Benga sarai kamar yadda nasan yunwar cikina, masifaffun sojoji ne da babu abinda bazasu iya ba in har suka sa kansu don su suka san yaddda sukai suka raba president da Marshall Damijo duk irin matsananciyar amintakar dake tsakanin su kuwa, na shiga mota direba ya dawo da ni gida.

Ke Saratu in zaki iya tunawa a ranar babu yaddda ba ki yi ba ki ji abinda ke damuna naki gaya miki har kika yi ta kuka.

Na kwana ina saka yadda zan yi in fidda kaina daga wannan tsaka mai wuya da suke neman turani, wanda a lokcin da za’a rantsar da ni, na yiwa kasata alkawarin bazan taba yin wani abu ba bisa doka ba, ba zan taba cin amanar kasata ba, idan kuma har na nuna hakan na tabbata Benga Delsu da jama’arsa ba zasu kyaleni in zauna lafiya ba, sai na yankewa kaina shawarar yin ‘retire� in koma kasuwanci cikin ruwan sanyi in barwa Allah al’amura na, na kuma amince cewa duk wata cuta ko daukaka da zata sameni to da sani da yardar sa ne.

A washegari na aika takarduna na yin murabus daga aikin soja kwata-kwata, ai dai na fita daga kowanne irin shirin suma.

Ashe dai tuya nayi na mance da albasa, don kwata-kwata sati daya a tsakani na ji su Benga ma sun yi ritaya, a dalilin an soke mulkin soja a lokacin, amma manya-manyan su irin su Marshall Shu’aibu Damijo, Shitu Allazi da Janar Delekonkwo duk basu yi ba, ban kawo komai a raina ba, don ban zaci zasu waiwayeni bama tunda sun ji na bar ‘military� ashe dai kuskure nayi. Don a dai-dai lokacin aka soke ‘military-rule�

Ranar wata asabar ina hutawa a gida aka ce dani Benga da Shitu na son gani na (seriously private) wato cikin tsananin sirri, nayi Addu’a kan Allah ya raba ni da sharrin wadannan miyagu kamin in je.

Bayan mun gaisa, sun kuma gamsu da matakan tsaron da ke falon, suka gaya min bukatar su na cewa su Shittu zasu shirya kashe president ta hanyar sa masa guba a abinci da za’a sa kukun sa ya aiwatar akan wasu adadin biliyoyin nairori, in yaso ni sai su tsaida ni takara a jam’iyyyar da zasu kafa mai karfin gaske in samu ‘by all means� (koda ta magudi ne) sai in barsu su tsara min irin mulkin da suke so a yi.

Hankalina ya tashi, cikin zafi na zazzagesu na kuma gargadesu kan cewa wallahi babu ruwana, idan kuma suka sake sako sunana cikin al’amarin su, to kuwa zan tona musu asiri duk da kakkarfar abotar dake tsakanin mu kuwa.

Sai suka yi murmushi suka bani hakuri, tare da tabbatar min zancen ya wuce har abada, suka tafi.

Kawai sai ji nayi har a bakin Faisal wai na tsaya takarar shugaban kasa? Duk an bi an manna posta na a ko’ina, president da kansa ya neme ni a waya yace a she takara na shiga haka ba sanarwa? To yana mun fatar alhairi. Sai ma na rasa me zance.

Na kira Benga a waya nace ban ji dadin cin mutuncin da su kai min ba, wannan ai kazafine, suna sane da tsakanina da president ya za suyi min kage kan abinda bani da masaniya a kai?

Sai cewa yayi su ba su bane, basu ma san anyi ba, don shi a lokacin ma yana Cameroun, amma inyi hakuri zai bincika ko su Marshall Shu’aibu ne. Abinda yace da ni kenan.

Ranar da suka shirya wanzar da komi sai kukun da suka damkawa amanar abin ya kira president ya tona masu asiri, har kudin da suka bashi ya danka mai da takardun yarjejeniyar cewa ni za’a tsayar. Ni da nake amininshi tun muna NDA, nida ya taimaka ta kowanne fanni a soji, hatta karatun Al’ameen a turai shi ya dauki nauyi har yau kwandala ta bata taba yin ciwon kai ba, amma wai dani aka hada baki za’a kasheshi har lahira, (a tunanin shi fa), an ce mun president har kuka yayi kan cin amanar da yake tunanin nayi mishi, a take ya bada oda da shelar a kame mu duka.

Rannan ina magana da Najib a kan hanyata ta dawowa daga Makarfi dibo jikin ka Baffa, motocin soji suka yi mana dabaibayi, nace da direbana ya tsaya amma saboda rudewa sai ya karawa motar wuta, nayi mai tsawa maimakon ya tsaya sai ya kara gigicewa ya kara gudun motar fiye da (300), ba sai suka sakarwa tayoyin motar (bullets) ba, motar ta hantsila ni na fado bisa titi cikin jini, shikuwa tuni ya dagargaje a ciki.

Duk irin rauninnikan da ke jiki na haka suka kakaba min ankwa a ranar suka tafi damu Kiri-kiri.

A Lagos aka kaini asibitin bariki nayi jiyya ta tsayin watanni uku kafafu da hannayena duka daure da ankwa jikin karfen gado, ban taba zaton zan rayuba, sai dai da yake wuya bata kisa sai in kwana ne ya kare.

Bayan na warke aka tafi damu Enugu daga ni har su Benga ba mai ce da kowa uffan don takaici.

A daren ranar abinda ya sani kuka tun farkon al’amarin shine da aka daura min camera daga gidan talbijin na kasa NTA, CNN da BBC domin watsa labarun cewa an kama mu dumu-dumu kan son yiwa kasa juyin mulki, karkashin jagorancina ni Bello Makarfi. Nayi kuka irin wanda ban taba yi ba a rayuwata, sharri ciwo ne da shi balle irin wannan dana tabbatar za’a harbe ni ne a banza a inda ko gawata baza’a yi mata sallah ba, sai dai ta zama ta ungulu da tsintsaye.

Bana kuka don zan mutu, sai don mutuncinku da zai tafi terere, a sanadiyyyar wulakantacciyar mutuwar da nayi! Aka dawo damu (Imo State prison) da abin yayi kamari aka cilla mu South-Africa ta jirgi, inda aka cigaba da bamu tsatstsauran tsaro.

A wannan dan tsukin na fidda rai da rayuwa kwata-kwata sai na maida al’amurana ga Allah, dare da rana ina rokon shi yayi mun rahma ya inganta rayuwar ku bayan raina.

Mun shiga kotu ranar Alhamis inda aka tafka mahaukaciyar shari’a, shaidu suka tabbatr da sa hannun mu duka nan da nan ka yankewa Benga Delsu da su Shitu hukuncin kisa da bindiga.

Ni kuma da babu kwakkwarar shaida a kaina, ban kuma amsa laifina ba, haka shi kansa kukun ya tabbatar babu ni a sanda aka kirawoshi, duk da irin kokarin da lauyana yayi suka san yadda sukai suka zurmani aka yanke min hukuncin life � imprisonment (daurin rai da rai), sai na daga hannu nace Allah yasa hakan shi ya fiye mun alkhairi da ku baki daya.

Shekaranjiya ina kwance aka ce in taso, a gidan gwamnatin Delta, dayake an maido ni jurun din Delta State, President ne na gani tare da mukarrabansa wato gwamnonin Nijeriya gabadaya, ya debo su don su zo su bani hakuri an gane bani da laifi kwata-kwata a yau za’a maido ni gida.

Na tambayi yadda abin ya kasance aka gaya min cewa Shitu da Marshall da za’a harbe su suka roki alfarmar a basu lokaci su farke komi, ba kuma nufin su a yafe musu bane, illa su fadi gaskiyar yadda Benga ya turani cikin al’amarin, don ya nemi hadin kaina na yi mai barazanar tona musu asiri, suka fadi inda za’a samu shaidar komai akan hakan a gidajen su, suka kuma roki da a kyaleni ko hakkin da ke kansu ya ragu, sun tabbatar alhakina ne ya janyo masu tonon asiri. An bani hakuri, an kuma bani tarar bata mini suna da sukai ta biliyoyin nairori tare kuma da sabon albishir din cewa sati mai zuwa in shiga (presidential office) a matsayin mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokoin Mulki.�

How much do you like this story?
5/8/22, 21:04 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two

*@Takori*

Page🔟
Chapter 39 · 0% Book details