← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 90

Sashe 72

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma ni bance ayi mata na mujiya ba cewa nayi kawai a farraka tsakaninta da ku da Daddy Makarfi Jin irin batutuwan da take na tozarta kai, wadanda tabbas bana mai cikakken hankali bane yayanta suka sake yunkuri cike da karfin zuciya suka bambareta daga jikin makarar aka fita da shi. Duk abinnan da ake, Daddy Makarfi, rike yake da tazbaha idanunshi babu ko digon hawaye, a sahun gaba, wurin raka Alameen gidanshi na gaskiya.

Hakika mutuwar Alameen ta girgizasu, ta wargaza tunaninsu, ta takaita farin-cikinsu, ta azabtar da ruhinsu, ta dai-daita tunanin su, ta girgiza zuciyoyin su ta kuma nutsar da su ga kara kadaita Allah!

A wani bangaren mutuwa ce wadda baa taba yi masu ba. Sun shiga yanayi na kewa, kunci da alhini irin wanda basu taba shiga a tarihin rayuwarsu ba, ninkin ba ninkin halin da suka shiga a sailin da aka kulle Daddyn su.

Wai ance ba mutuwa ake wa kuka ba, sabo ne, to sun saba da Alameen. Yaya ne mai kyautayi da son jinin sa, da iya takun rayuwar shi. Mutun ne da ko hanya ce ta hadaku da shi a wuni daya, zaka so ka zauna da shi shekara daya. Idan zama ne na shekara ya hadaka da shi, zaka so cigaba da zama da shi muddin rayuwarka.

Yana da dimbin kirki da dimbin alkhairi. Yana da tsananin kulawa kan abinda yake so musamman iyaye da yanuwan sa, yana kuma nuna hakan a fuska, aljihun sa da zuciyar sa. To balle kuma matar shi abokiyar rayuwar shi. Mutuwar Alameen sai ya zamanto tamkar wani girgijen gini na gidan ne ya fadi, ya ruguje.

Walwala ta karanta haka zuciyoyi sun azabtu, babu mai iya yiwa dan uwan sa taaziyyah sai kallon-kallo. Ba abinda kunnuwan su suka tsana da ji kamar wani ya ce da su,

“Ya hakuri?�

Allah ya sani, da ka ce musu wannan gara kawai ka ce,

“Allah Ya Ji kan sa!�

Anan ne za ka ga wasu hawayen kauna sun zubo. Irin kaunar nan da har abada, bazata taba gushewa ba. Makarfi yaga kauna daga alummar Nigeria da wajenta kwarai da gaske. Daga shugaban kasa zuwa gwamnonin jihohinsa duka, kusoshi na mulkin soja zuwa na farar hula, likitocin Florida musamman daga birnin Miami da duk wani sako ko loko da Alameen yayi karatu ko wani aiki na wucin gadi sun barko domin jajanta masa wannan babban gibi da yayi a rayuwarsa, da cike shi abu ne da har abada ba zai yiwu ba!

Yaya goma suka saura masa amma ji yake a yanzun kam bashi da ko daya a duniya.

Ko dama can kaunar Alameen daban ce data kowa a zuciyarsa, baya hada son da yake masa da na kowa cikin yayansa. Yana son shi, ya na kaunar shi tun yana tsumman goyon sa, ta yadda har yake kiran sa BURI NA. Sai dai har kullum yana mai farin-ciki da irin mutuwar da Alameen yayi;

ranar Jumaa, cikin watan Ramadhan, da azumi a bakin sa.Wani irin hatsari amma kamar Baben dake goye a bayan mamarsa. Albarka ta uwa da uba. Kykkyawar shaida daga duk wanda ke tare da shi. Dr Rehab gurfane yayi gaban shi yana kuka da hawayensa marassa launi yana cewa

Na dade ban samu mutun mai kyakkyawar zuciya irin M.A.B (Mohammed Alameen Bello) ba! Na dade ban ga Musulmin da ya san shi Musulmi ne a turai irin M.A.B ba, na dade ban ga mutumin da ke tara halal batare da digon haram a ciki irin M.A.B ba, na dade banga mutum mai alkhairi da duk abinda ya mallaka a duniya irin M.A.B ba, ban taba samun aboki nagari mai amana kwatankwacin sa ba.

Hakika kun yi rashi babba, amma wannan ba rashin ku bane ku kadai na alummah ne. Nafi kowa sanin dimbin alherinsa. Tabbas shi ya tafi, amma aiyukan sa na alkhairi ba zasu taba yankewa ba!

Hajiya kam, daga baya saida aka dangana ga psychiatric Hospital na Kaduna da ita, domin a cewa
gamu da abinda suka kira mental disorder. Iyaka kokari likitan Alameen wato Dr. Alfred yayi wajen ganin cikin wata ukku da wasu yan kwanaki da Ihsan ke tare da shi bai zube ba. Amma na Anti Saratu ya fita, sai dai fatan Allah ya bada musanye da alheri.

Kwanan Ihsan goma kwance a gadon asibiti bata san wanda ke kanta ba. An yi mata karin jinni fiye da leda uku hakannan karin ruwa baya yankewa. A binciken kwararren likita Alfred ta gamu da ciwon hawan jinni. Don haka suka cigaba da rikonta a asibitin yayinda suka sallami Aunty Saratu tun a ranar sadakar bakwai, kuma a ranar ne Haj. Hadiza da Ambasada Bashir da diyarsu Zarah da ta zama buleliya jazur da ita suka sauka a birnin Ikko inda daga nan suka biyo jirgi zuwa Abuja cikin tsananin dimauta da gigicewa, suna masu mika taaziyya mai girma ga Bello Makarfi. Sai ya ce mu gode masa, mu godewa Allah, Allah na gode maka!

Hakikah karfin imani irin na wannan bawan Allah na baiwa kowa mamaki. Shukrah yake tare da hamdalah ga Allah a koyaushe akayi masa taaziyyar gudan jinin sa Ameenu. Ya kama hannun Ambassada yana murmushi ya ce,

Basheer? Don me ba zan gode masa ba? Sanda ya halicceni nikadai ya halitta, ban san kowa ba, bansan komi ba. A hankali ya koyar da ni in mike in taka kafafuna a doron kasa. Ya bani ikon yin aure, na haife su, amma ba nawa bane, amana ce ya danka mini ya ce in kula masa da su zuwa lokacin da zai karbi abinsa.

A duk tsawon lokacin nan daga niimarsa nake ci, nake sha, nake numfashi, na ke neman abinda zan kula da su. In ciyar dasu in tufatar dasu. Yayi min falala da niima daga duk wani jin dadi na rayuwa.

Babban niimarsa gareni shine yayo ni Musulmi, yayi nufin karbe Alameen daga gareni domin ya jarraba imani na, yaga cewa shin ni mai godiya ne ga dimbin rahmominsa da fadhalolinsa a gareni ko ko zan butulce? Sabida wannan jarrabawa kankanuwa da ya yi mini? Don haka har kullum nake gode masa, na tabbata ban fi shi son Alameen ba, kauna ta da shi shine in yi masa addua, na nema masa Rahman Allah, kuma ina rokonku ku taya ni nema masa gafara domin hakikah yana daga cikin nagartattun yaya masu shiga zuciyar iyayen su!

Satin su daya a Nigeria suke juya kasar Korea, Aunty Saratu ta gargade su ta kuma gargadi kowa da kada a sake Intisar ta ji wannan labari, wadda a lokacin take zana jarrabawarta ta karshe a secondary.

Gargadinta yafi zafi a kan Hidayah, wadda ke tare da mijinta a nan Nigeria tare da su. Ita Hunainah dama tana Jamiar Al-Azhar da ke Cairo inda take karanta physiothearaphy. Suma kan su, sun tabbatar babu mai iya dosar ta da wannan labari illa tazo ta gani da idanun ta, taji abinda kowa ya ji, koda yake ita din mai jin fiye da abinda kowa ya ji ne!

Ranar kwanaki na arbain da rasuwar Alameen an yi adduoi na musanman da sadaka mara iyaka, a yayin ne kafafuwa suka fara daukewa, sai su isu, wayyo! Ashe wanda ya mutu shine ya mutu, rayuwar sai wanda ke raye?

Jarrabawa ta karshe da ta zana ta kama ranar litinin. Bata farin ciki ba kuma ta bakin ciki duk da cewa kusan rabin burinta na rayuwa, ya cika, ta kuma ji tamkar an dauke mata wani nannauyan dutse ne aka.Ba don komi ba sai don tsananin damuwar rashin sanin makomar rayuwar ta a inda ta adana zuciyarta, wato rashin sanin hakikanin abinda Alameen ke ciki.

Kwanaki sun shude sun zama satittika, satittika sun shude sun zama watanni bata kara ji daga Alameen ba. Ta dauki laifi duka ta azawa kanta, tare da kalubalantar baudaddiyar zuciyarta. Eh, ta kirayi zuciyarta baudaddiya domin raayin rikau irin nata shi ke zalintar ta a koyaushe. Juriyarta yayi yawa har ya zama cutar kai, ta tabbata in har bata yafewa zuciyarta ba, zasu yi hisabi da ita.

Bata taba mallaka mata abinda take so ba! A kullum tana mai kalubalantar kaza saboda kaza, tana kin kaza saboda kaza, tana cewa aah a inda ya kamata tace eh. Ba ta laakari da uzrin kowa sai nata. Bata karbar uzrin kowa sai wanda zuciyarta ta yanke. Ta manta cewa kaza kan halatta kaza a inda babu kaza.

To yanzu idan Alamin yayi fushi ne ya yakice ta azuciyar sa, ko kuma Hajiyar ta ja raayinsa ya fita harkarta ina zata tsoma rayuwarta? Yaya zata yi da wannan mikin da ke narke a zuciyar ta da har yau bata sami damar amayar da ko rabin-rabin sa ba ga wanda yake ciwon domin sa? Yaya za tayi da kuncin da zuciyarta ke ciki na nadama da dana sanin hukuncin da ta yanke masa? Burin ta kawai a lokacin ta koma gida, ta neme shi ta bashi hakuri, ta gaya masa ta fi shi azabtuwa da hukuncin ta, ta fi shi shiga tashin hankali akan hukuncin ta, wannan karatun da ta yi duk a cikin karfin hali ne amma second, minti ko awa tunanin shi ne a zuciyarta, tunanin halin da yake ciki ke nukurkusar ta illa ita din mai juriya da zurifin-ciki ne. Ta amince a yi masu aure koda Hajiya zata ke yankar naman jikinta sala-sala kullum ta Allah ne har sai ta karar da ita, in har suna tare, ba zata ji zafin hakan ba, kai in ta kama ta je ta kama kafar Hajiyar ta roketa ne zata yi, ta nema mata gurbi da zata raba rayuwar ta cikin inuwar muhimmiyar zuciya irin ta dan ta Alameen.

Haka kawai ta ji hawaye sun zubo mata, ta daga kai ta dubi dakin barcin su da ke cikin makaranta Kingston College, dalibai yan uwanta ke ta hada kayansu cike da farin-cikin tafiya gida a washegari. Zaune take kurum a gefen gado tayi tagumi ta zubawa tickets din ta ido, wadanda a kayi mata booking daga Riyadh zuwa kasar Korea ta Kudu.
Chapter 72 · 0% Book details