← Book details Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 90

Sashe 35

Siradin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima Hakimin tunanin shi yayi dai-dai da na dan uwan shi, ya kara karfafa shi da cewa abin da yayi jihadi yayi, da sannu zai ga budi da nasara cikin rayuwar shi. Don duk wanda ya taimaki wani babu shakka Allah zai taimakeshi. Yayi masa Addu’ar samun aiki mai tsoka wanda zai tallafe mu har mutuwa ba tare da gazawa ba, ya kuma kara tunatar da shi hakika yayi riko da sunnah, domin Manzo mai tsira da aminci ma ya fara ne da auren Nana Khadijah a lokacin tana bazawara, ta ma girme mishi nesa ba kusa ba. Kuma mata irin Dije sai wanda Allah ya nufa da samun rahmar aure domin daga halaye, dabi’u zuwa surar ta duka babu mummuna, ta kowanne fanni ma na fi ‘yar uwata nutsuwa.

Tun daga ranar Bashir bai barin mu mu yi wani aiki mai wuya sai ya amsa ya yi. In wanke-wanke ne sai dai ya wanke mu dauraye haka in surfe ne sai dai ya surfa mu tankade, in kuwa wankin kayan su ne sai dai ya saba mu dauraye mu shanya.

Ga shi da raha kullum cikin sa Hajjo dariya ya ke don ni da wuya duk ban dariyar sa ya ga hakorana. Rannan ya ce da Hajjo mai yasa ni bana dariya ne?

Hajjo yadda suka saba da Bishir komi fada mai take bata boye mishi komi da ya shafe mu, haka kawai zan ji tana bashi labarin yadda muke rayuwa a ruga tare da Innar mu. Rannan ma ji nayi tana koya mai yadda ake tatsa harda cewa “Kawu na, Saniya fa sai da shafa a ke tatsar ta.�

Ya tintsire da dariya ya ce,

“kenan nima Hajjo sai da sannu zan samu So daga Yayar ki?�

Ta ce “meye so kuma Kawu na?�

Ya daura hannun sa bisa kirjin sa ya lumshe ido yace “So, is a feeling for deep affection, a bery strong feeling of affection…� ta yi sukutiii…� tana sauraron shi da dukkan hankalinta da iyakar fahimtar ta, tace “magana kake ko yare?� Yace “tunda baki ji ba shikenan�.

To a yau ma sai ta gyara zama, ta kalmashe ‘yan kafafunta kyawawan idanuwanta cikin na Bashir, na tabbatar wani babban sirrin zata kwaye masa, da haushi ya isheni sai na kai mata mangara da hauri da kafa, Bashir ya yi hamzarin rike hannuwana duk sai naji jikina ya yi sanyi, yayi saurin saki na ya dube ni cikin ido, wata irin kunya ta lillibe ni, wani abu ya daki kahon zuciya ta irin wanda ban taba ji ba nayi saurin sadda kai, yace

“ko da wasa, kada ki sake dakar min kanwa ko bana nan ban yafe ba, Hajjo na gaya mun, mai yasa Hadizah bata dariya?�(Don shi bai taba cewa Dije ba, ita ma Hajjo ya hana ta har ta saba da fadin Haddizar), ta dube ni tayi murmushi kana ta maida duban ta ga Bashir, ta kalmashe ‘yan idanun ta tace.

“Kana ji ba?

Can-can an mata aure, an sata a lalle ta je gidan miji, ta haifo sankaceciyar jaririya, hancin ta irin wannan (sai ta ja nata), bakin ta irin wannan (sai ta ja nawa), gashin ta curi guda. Sai barayi suka lalabo cikin dare suka dauke ta suka ranta a na kare…� (tana yi tana gwada irin gudun da barayin suka rika yi da ‘yan yatsunta). “Tun daga ranar bata kara yin dariya ba, sai ciwo, ta yi ta ciwo kaman ta mutu, ka san kowa yana son dan sa Kawu na, kamar yadda Innar mu ke son mu, tamkar yadda Addar nan gidan ta ke son Salisun ta muku ta ke zagin mu. Rannan tace mun watakila ‘yar ta ta mutu yanzu tunda ba wanda zai ke bata nono…�.

Bashir yayi shiru ya juyar da kai, bai son su ga hawaye ya ke fitaswa. Ya sa hankici ya dauke hawayen idanun shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta, shi kan sa bai san ya akai ya baro wannan maganar ba.

“Hadizah, Insha Allah za mu ga ‘yar ki Fatimah, mu hada da wadanda zamu haifa a gaba mu sa su a makaranta, suyi karatu irin nawa. Mu mun rasa soyayyar iyaye tun muna kankana, amma su Insha Allah zamu rungume su da dukkan so da dukkan kauna har zuwa ran da muka daina numfashi�. Sai ya tashi ya fice.

Matan Hakimi fa suka maida idanun su kan Bashir da duk wani takun shi cikin gidan. Wasu cikin su suka ce dakin mu yake zuwa cikin dare yana lalata da mu shiyasa ya tare a gindin mu, wasu suka ce a’ah, ai har da ranar ma abinda muke yi kenan cikin daki.

Rannan har yana gayawa Inna Kwaire magana don ta ce da Hajjo tsintacciyar mage, yace da ita sanda Yayan shi ya aureta, aka dauko farin kyallen da ake shimfidawa amare fari kwal aka same shi, don haka gara Hajjo da aka tsinto daga daji ta san mutuncin kanta, itako da aka tsinto gaban iyayen nata ai basu ga mutuncin ba.

Ai kuwa a ranar data kama Hajjo da duka sai da ta targada ta.

Da Bashir yaga abin nasu bana kare bane sai ya zuciya, ya sami Yayan shi yace ya ja ma matan shi kunne ko dukkansu yayi masu dan banzan duka. Hakimi yayi murmushi yace yanzu kai Bashir, in aka kyale ka sai ka daki matan aure da ‘ya’yan su da jikoki da surukan su suna kallon ka?�

Ya ce “to sabida Allah ina ruwan su da yaran nan ne don Allah tun da dai ba zaman su suke ba koko akan su suke zanne?� Hakimi yace

“in kana son komi ya zo karshe, gobe a daura auren ku da Dije, ku zauna anan dakin da suke har zuwa ranar da Allah zai yiwa aikin fitowa�. Bashir ya amince.

A ranar ne kuma ya samu sakon kiran (Intrebiew) daga Abuja ana kiran su a safiyar washegari, ya gayawa Hakimi kar a fasa daurin aure amma shi za shi Abuja ya san maganar aikin ne.

Karfe goma na safe Hakimi da Liman suka daura aure na da Bashir akan sadaki naira dubu biyar. Duk wasu kayan lefe da ke yiwa ‘yar gata a garin Shanono Hakimi yayi mun ni da ‘yar uwata. Har gobe, bani da abinda zan ce da Kawun nan naku Hunainah, domin yayi mun abinda ko mahaifana da suka haife ni iyakacin abinda za su yi mun kenan.

Babban alkhairin sa gare ni shine da ya hada ni da miji irin Bashir, daya zamo jigo ga rayuwata, bango abin jingina ta kuma abin alfahari na.

Don haka har kullum bana tashi daga inda nai Sallah ban nema masa rahma da gafarar Ubangiji ba.

Sati na zagayowa sai ga Bashir cikin farin cikin da ba zai misaltu ba tare da wani abokin sa Hassan cikin motar Hassan din.

Yana gaida kowa shi da Hassan suka shigo dakin mu, Bashir ko kulawa da su Hajjo da Hassan bai yi ba ya sure ni ya shiga juyi da ni a tsakar dakin. Hajjo ta ja mayafinta ta rufe ido tana laluben bango tana cewa “bako-bako boye ni, kada Kawu na yace na yi rashin kunya� ta shige cikin babbar rigar Hassan gabadaya suka sa dariya.

Bashir yace “Khadijah tabbas ke alkhairi ce a gare ni, kamar yadda takwarar ki Nanah Khadijah ta zamo alkhairi ga Manzon mu?�

Bashir bai taba tsayawa tambaya na ina son shi ko bana son shi? Abin da ya sani shine in har sai ya san wannnan za mu yi aure, ashe kuwa zamu mutu ba mu yi ba. Tunda dai ina bashi girma ina kuma tsananin jin kunyar sa, yasan alamun so kenan a wancan zamanin.

Ya samu Hakimi ya gaya mishi sati mai zuwa zamu tashi zuwa kasar Faransa in da zai fara aiki da ofishin jakadancin mu na kasar. A ranar da aka kira su Abuja aka danka mai takardun shi na daukar aiki shi da Hassan babban aminin shi da wasu abokan karatun su da dama.

Ya tsaya ne shirin ‘pass-port� da bisar mu ne ni da shi da Hajjo. Hakimi ya sa wa abun albarka, ya kuma kara dankawa Bashir amanar mu, yace ya ke tunawa a kullum bamu da kowa, Allah shine gatan mu sai ko shi, Basheer.

How much do you like this story?
5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two

*@Takori*

Page8ï¸âƒ£

Da ranar tafiyar mu tazo ni kam sabanin ‘ya’yan gata da ake rakasu da nasiha da Addu’a ni da zagi da gori da habaici ‘ya’yan Hakimi da matan shi suka raka ni wai mu mayu ne, mun lashe kurwar Bashir da ta Hakimi to su kurwarsu ta fi karfin kankarar mu. Hajjo yarinyace ba hankali ga maida martani inda duk aka tsokalo ta sai ta yi masu gwalo da zata shiga motar Hassan ta ce,

“Alalalo! Zamu shiga jirgi dai ba ke Inna Kwaire�.

Daga Bashir har Hassan dariya su ka yi, ni ko har muka zo Abuja kuka na ke na tunanin iyayen mu da batacciyar jaririya ta.

A filin jirgin saman Abuja muka kwana tsimayen jirgi mai zuwa France ana ta cike-ciken takardu, da asuba muka bi jirgi ‘direct� (kai tsaye) zuwa babban birnin Paris. Gidan da muka zauna yana nan a jerin gidajen ma’aikatan jakadanci na kasar.

Ba anguwa daya muke da Hassan ba don shi yana cikin gidajen ma’aikatarsu ne amma kullum ya taso aiki gidan mu zai yada zango su ci abincin rana tare da Bashir har dare.

Shakuwa mai tsanani ke shigar su shi da Hajjo. Da girman Hajjo da komi Bashir ya dauketa ya dankara a aji daya.

Hajjo ta sha tsiya wurin ‘ya’yan Faransawannan don tace mun har kungiya-kungiya suke yi zuwa kallon ta (katuwa a aji daya) ga wani sunan shakiyanci da suka lika mata (Mère) watau Mamar su kenan.

A rayuwata ban taba halartar makarantar boko ba, amma na yi karatun Addini mai yawa a wurin Baffan mu sanda ya ke da rai. Sai Bashir ya kashe muhimmin lokacin sa yana koyar da ni karatu da rubutu haka Hajjo komi ta koyo haka zata zo ta yi ta koya mun Bashir na aiki ya koma karo karatu (PhD) babbar Jami’ar Faransa yana kara zurfafa ilimin sa.
Chapter 35 · 0% Book details